Page 11

115 11 0
                                    

🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱

*RAYUWAR CIKIN AURE*
_(True Life Story)_

🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱

*Story & Writing:*
_Nafisat Isma'il Lawal_

*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT🧝*

*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

'''( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)'''

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

*P.W.A✍️*








*TSOKACI*
_Wannan littafin tsokaci ne a kan rayuwar ma'aurata, abubuwan dake faruwa yanzu a gidajen Auren mu, da kuma matsalolin dake cikin auren. Duk wanda yaga labarin nan yayi iri ɗaya da rayuwar sa to yayi haƙuri domin ban yi don cin zarafin sa ba, nayi ne domin gyara, domin rubutu da gyara shi ne buri na, Faɗakarwa ita ce tsari na, Ilimantarwa kuwa muradi na ne. Isar da saƙon amfana ga al'umma shi ne tunani na. Alƙalami na a kullum yana bin hanyar da zai riƙa gyara ne._




*PAGE:11*

_____Yau su Hauwa suka wayi gari sun samu Abokiyar zama, an kawo musu wata ƴar hayan, yarinya ce ƙarama don sun girme ta sosai, sunan ta Ruƙayya sai dai ana ce mata Maman Safina kasancewar ta tana da ɗiya guda, auren nasu da Mijin ta Sadis be fi shekara ɗaya ba, domin duka-duka watan Safina ƴar su biyu ne

Kasancewar Sadis Mutum ne me son ƙarya da son rayuwar ƴan gayu, hakan yasa ya zurma Ruƙayya wacce a tunanin su ita da dangin ta me kuɗi ne. Sai da aka yi auren ya kama musu plat ɗin gida a cewar sa, "Gidan shi ne", a lokacin da ya je neman auren ta ya kashe musu kuɗi sosai wanda lokaci ɗaya aka ba shi ita ba tare da wani ƙwaƙƙwaran bincike ba, inda aka yi auren aka gama lafiya. Sai dai kuma tashin farko suka soma samun saɓani da Ruƙayya sabida rashin wadata da ba ta gani a zaman su, abinci ma wannan sai an yi da gaske yake iya kawo musu, daga baya ne suka gane ashe dama ba me kuɗi bane shi yaudaran su yayi tunda ga shi gidan ma da suke ciki haya yake yi, bata gane hakan ba sai da Me gidan ya soma mishi jeka-ka-dawo saboda ya ba shi kuɗin shi, tunda gidan da ya kama hayan ko biya gaba ɗaya be gama yi ba. A nan ne suka soma samun matsala wanda ita Ruƙayya ta tayar da hankalin ta a kan, "sai ya sake ta." But ya ƙi. Daga nan ne ma ya soma nuna mata halin sa na mugunta don har dukan ta yake yi, ga shi ba ya son bata abinci nan da nan Ruƙayya ta soma sauyawa, wahala ta ishe ta har yaji tayi, ƙarshe dai iyayenta su suka dawo da ita tunda me afkuwa ya rigada ya afku ga shi har da rabon ciki. Basu da yanda zasu yi su saka ya sake ta tunda shi ya rantse ya maya, "bazai taɓa sakin ta ba, wahalar da ya sha bazai tafi a banza ba." Dole Ruƙayya ta dawo gidan ta zauna ta ci gaba da zaman haƙuri. Ga shi da biye-biyen Mata har giya yake sha, ta rasa yanda zata yi tun tana iya magana har dai yanzu ya fi ƙarfin ta sai yanda ya juya ta, duk ta gama koɗewa saboda wahala a ɗan ƙanƙanin lokaci.

Wata tara da kwanaki ta haifi Safina, kuma har a lokacin zaman nasu be sauya zani ba

Lokacin da suka cika shekara ɗaya cif me gidan ya zo yayi musu watsi da kaya tunda har yanzu Sadis ya kasa biyan kuɗin shekaran

Dalilin da yasa suka samu haya a gidan da su Hauwa suke haya; saboda yaron Me gidan shi ya nemi alfarma wajen Hajiyar tashi yace, "ta taimaka ta basu ɗaki, daga baya idan Sadis ɗin ya samu sai ya biyata". Saboda shi tausayi suka ba shi kasancewar a gaban shi aka yi musu watsi da kayan. Dalilin da yasa kenan Hajiya me gidan hayan ta basu ɗaki kenan.

Suna zaune su Hauwan suka ga ana ta shigowa da kaya gidan

Yaron Hajiya shi yayi musu jagora zuwa gidan, sannan ya buɗe musu ɗakin ya ƙara gaba

RAYUWAR CIKIN AUREWhere stories live. Discover now