🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱
*RAYUWAR CIKIN AURE*
_(True Life Story)_🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱
*Story & Writing:*
_Nafisat Isma'il Lawal_*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT🧝*
*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞
'''( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)'''
/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
*P.W.A✍️*
*TSOKACI*
_Wannan littafin tsokaci ne a kan rayuwar ma'aurata, abubuwan dake faruwa yanzu a gidajen Auren mu, da kuma matsalolin dake cikin auren. Duk wanda yaga labarin nan yayi iri ɗaya da rayuwar sa to yayi haƙuri domin ban yi don cin zarafin sa ba, nayi ne domin gyara, domin rubutu da gyara shi ne buri na, Faɗakarwa ita ce tsari na, Ilimantarwa kuwa muradi na ne. Isar da saƙon amfana ga al'umma shi ne tunani na. Alƙalami na a kullum yana bin hanyar da zai riƙa gyara ne._*DATA SHARE*
Call, message or whatsap 07065334256
*MTN*
500MB 150
1gb 280
2gb. 560
3gb. 840
4gb. 1120
5gb 1400
6gb. 1700
Verlid for 30 daysAirtel
500MB 160
1gb. 310
2gb. 620
3gb. 1000
4gb. 1250
5gb. 1550
Verlid for 30 days9mobile
500mb. 500
1gb. 550
2gb. 1000
3gb. 1450
4gb. 1900
5gb. 2200
Verlid for 30 daysGlo
1.35gb. 550
2.9gb. 1000
4.1gb. 1400
7.7gb. 2300
10.0gb. 2650
Verlid for 30 daysCheap in safety.👌🏼
*PAGE:27*
_____Kamar yanda Muhseen yayi ƙudirin canza wurin aiki, ai kuwa bai samu matsala ba tunda Ogan shi yana sonsa sosai, shiyasa da ya nuna yana son a canza mishi wurin aiki, babu ɓata lokaci ya ce, "ya zaɓa kowanne gari yake so, cikin garuruwan da suke da reshe, shi kuma zai san yanda zai yi ya sama mishi."
Muhseen ya zaɓi Katsina tunda ya fi son can, musamman ma kasancewar garin ya fi nisa a kan Kano. A cikin satin aka ba shi damar fara aiki,
Shiyasa ya soma sanar da Umma domin ya ji mai zata ceHar ranta bata ji daɗin nisanta kansa da su da zai yi ba, duk da yace mata, "a wurin aikin ne aka canza mishi, ba shi da yanda zai yi." Shi yasa bata ce komai ba duk da a ranta hankalinta bai kwanta ba, domin ji take yi dama ya ajiye aikin ya nemi wani kawai, amma ta san hakan zai yi wuya, da aikin nan nasa suka dogara, sannan in ya ajiye ba lallai bane ya samu wani mai gwaɓi-gwaɓi kamar wanda yake yi ba, shi yake ɗaukar ɗawainiyar su, har ƙanninsa da yanzu ya saka su makaranta suna ci gaba, A'isha yanzu haka tana polytechnic ne na nan Kaduna, ajin farko, sai kuma Amina da ke SS 3 bata ƙarisa ba, shi yake musu komai na buƙatu tunda Allah ya hore babban albashi yake amsa, ga nauyin iyalansa Munira da ƴarsa Hanan, to basu da yanda zasu yi in bai tafi inda aka tura sa ba, addu'a kawai tayi masa da fatan samun nasara, sannan ta tambaye shi, "yanzu in ya tafi sai yaushe zai riƙa dawowa?"
Yace, "Umma Ni dai na yanke shawara in na tafi zan riƙa yin wata ɗaya before na riƙa leƙo ku, tunda gari ba kusa ba, nan da Katsina akwai tafiya, kuma kinga ba wai na saba da tafiye-tafiye bane ba na son ina yawan zirga-zirga a kan hanya."
"Eh hakan babu dad'i ai, amma duk da haka Ni dai idan zaka bi ta shawarata, sannan idan hakan bazai janyo maka wata matsalar ba, wata ɗaya dai yayi yawa, ina laifin ma sati biyu ka riƙa leƙo mu? Ko baka zo don mu ba zaka zo don Munira; tunda wannan tafiyar ba saba wa tayi da shi ba, nan gaba idan kana son ka kai wata ɗayan sai ka riƙa kaiwa tunda an saba, amma yanzu kwatsam ka tafi har tsawon wata ɗaya abun zai yi mana yawa, zaka bar mu da kewar ka."
YOU ARE READING
RAYUWAR CIKIN AURE
AdventureTSOKACI Wannan littafin tsokaci ne a kan rayuwar ma'aurata, abubuwan dake faruwa yanzu a gidajen Auren mu, da kuma matsalolin dake cikin auren. Duk wanda yaga labarin nan yayi iri ɗaya da rayuwar sa to yayi haƙuri domin ban yi don cin zarafin sa ba...