🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱
*RAYUWAR CIKIN AURE*
_(True Life Story)_🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱
*Story & Writing:*
_Nafisat Isma'il Lawal_*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT🧝*
*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞
'''( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)'''
/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
*P.W.A✍️*
*TSOKACI*
_Wannan littafin tsokaci ne a kan rayuwar ma'aurata, abubuwan dake faruwa yanzu a gidajen Auren mu, da kuma matsalolin dake cikin auren. Duk wanda yaga labarin nan yayi iri ɗaya da rayuwar sa to yayi haƙuri domin ban yi don cin zarafin sa ba, nayi ne domin gyara, domin rubutu da gyara shi ne buri na, Faɗakarwa ita ce tsari na, Ilimantarwa kuwa muradi na ne. Isar da saƙon amfana ga al'umma shi ne tunani na. Alƙalami na a kullum yana bin hanyar da zai riƙa gyara ne._*DATA SHARE*
Call, message or whatsap 07065334256
*MTN*
500MB 150
1gb 280
2gb. 560
3gb. 840
4gb. 1120
5gb 1400
6gb. 1700
Verlid for 30 daysAirtel
500MB 160
1gb. 310
2gb. 620
3gb. 950
4gb. 1250
5gb. 1550
Verlid for 30 days9mobile
500mb. 500
1gb. 530
2gb. 1000
3gb. 1450
4gb. 1900
5gb. 2200
Verlid for 30 daysGlo
1.35gb. 550
2.9gb. 1000
4.1gb. 1400
7.7gb. 2300
10.0gb. 2650
Verlid for 30 daysCheap in safety.👌🏼
*PAGE:14*
_____"wlh kin ji na rantse idan har ba ki bar yarinyar nan ta koma gidanta ba; wlh daga ita har ke sai dai ku bar gidan, muddin ba ki barta ta tafi ba auren mu ya ƙare dani da ke, sai ku tarkata ku bar min gida." Yayi maganar cikin tsananin ɓacin rai yana juyawa ya fice
Sosai kuwa jikin Fauziyya yayi sanyi da jin zancen Jamal ɗin, ta tsorata ta san zai aikata tunda ya rantse, kuma bata shirya rabuwa da shi ba, bata shirya rasa igiyoyin aurenta ba, shiyasa cike da borin kunya take ta faɗa tace wa Intisar ɗin, "ta tafi, amma zata san yanda tayi ta ɗauki mataki a kan Shureim ɗin."
Haka Intisar tana kuka Sumayya na taya ta a yanzu ɗin ta bar gidan. Direba ya ɗauke ta suka wuce gidan nata.
Duk abinda ake yi Mama da Hafsah basu sani ba, suna can sashin su suna ta hira abun su.
Drever yana kai Intisar ya juyo ya dawo
Ita kuma ta shiga gidan cikin kuka
A lokacin Shureim na zaune a kan sofa yana kallo, dama yana bari ne ayi sallan isha'i sannan ya tafi ɗauko ta. But sai ga ta ta shigo tana mishi kuka, kallonta kawai yake yi kamar zai yi magana amma ya ƙi furta komai, har yanzu haushinta yake ji don yana son ya koya mata hankali ta dawo tunaninta, yana matuƙar sonta shiyasa yake matuƙar kishin ta, ya san shi kaɗai ya santa a ƴa mace domin da budurcinta ta zo mishi gida, amma kuma ai be da tabbacin shi kaɗai ya taɓa latsa ta, sannan kuma idan ya barta ta ci gaba da zuwa makaranta yana ga kamar zata iya samun waɗanda zasu hure mata kunne irin ƴan iskan Mazan nan har ta biye musu, shi kawai hankalin sa be kwanta ta ci gaba da karatu ba, idan har karatu ne a gidan sa ta gama shi har abada
YOU ARE READING
RAYUWAR CIKIN AURE
AventuraTSOKACI Wannan littafin tsokaci ne a kan rayuwar ma'aurata, abubuwan dake faruwa yanzu a gidajen Auren mu, da kuma matsalolin dake cikin auren. Duk wanda yaga labarin nan yayi iri ɗaya da rayuwar sa to yayi haƙuri domin ban yi don cin zarafin sa ba...