Page 7

132 13 0
                                    

🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱

*RAYUWAR CIKIN AURE*
_(True Life Story)_

🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱

*Story & Writing:*
_Nafisat Isma'il Lawal_

*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT🧝*

*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

'''( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)'''

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

*P.W.A✍️*





*TSOKACI*
_Wannan littafin tsokaci ne a kan rayuwar ma'aurata, abubuwan dake faruwa yanzu a gidajen Auren mu, da kuma matsalolin dake cikin auren. Duk wanda yaga labarin nan yayi iri ɗaya da rayuwar sa to yayi haƙuri domin ban yi don cin zarafin sa ba, nayi ne domin gyara, domin rubutu da gyara shi ne buri na, Faɗakarwa ita ce tsari na, Ilimantarwa kuwa muradi na ne. Isar da saƙon amfana ga al'umma shi ne tunani na. Alƙalami na a kullum yana bin hanyar da zai riƙa gyara ne._












*PAGE:7*

_____Ba komai ne ya ja taron jama'ar a gidan ba illa faɗan da ake yi da Sauda da wata Mata. Sanadin Sauda tana bin ta Naira ɗari biyu ta je har gida bin bashin ta, ita kuma Matar tace mata, "bata da shi yanzu". Shi ne ita kuma ta ɗauko mata ƙaton gas-kuka ta nufo da shi gida, Matar ta biyo ta har gida tace, "baza ta yarda ba sai ta bata". Shi ne faɗa ya kaure a tsakanin su, duk yanda aka so a raba su an kasa sai cacan baki suke yi suna dambe. Sauda ta shigar da gas-kukan cikin ɗaki ta hana matar shiga sai kokawa suke yi, hakan yasa mutane suka cika gidan ana ta son raba su amma an kasa

Hauwa dake cikin taron jama'ar har da ita ake rabon faɗan, tana hango Anwar ya shigo gidan ta lallaɓa ta wuce ɗaki, sallama tayi ta shiga

Anwar da har ya samu wuri ya zauna a gefen gadon su ya amsa mata yana cewa, "wai me ake yi a gidan nan ne aka tara mana mutane?"

Murmushi tayi tana taho wa ta zauna a gefen sa da cewa, "kai ma ka san bazai wuce fitinan da Sauda ta saba tara mana mutane ba, faɗa suke yi da wata Mata ta ɗauko mata Gas-kuka a kan Naira ɗari biyu, Bilal ma yayi rabon ya kasa ya ficewar sa tunda ba ta jin rarrashi, wlh ta hana Gas-kukan nan sai an bata kuɗin ta".

Ajiyan zuciya ya sauke yace, "to Allah ya kyauta, Ni fa gaskiya lamarin gidan nan sai a hankali, ni da zan samu wani gidan me sauƙin kuɗi tashi zamu yi a nan tunda ban ga amfanin zaman mu ba, kullum gida ana tara mana jama'a ana fitina har kaina ya soma ciwo wlh." Sai ya ja tsaki yana cewa, "kin ga kawo min ruwa da abinci na in ci kafin a Kira Sallah".

Tashi tayi ta fita, bata jima ba ta dawo da kwano me murfi a hannun ta ta ajiye masa, sannan ta ɗibo masa ruwan daga cikin randan ta dake bayan ƙofar ɗakin. Ta ajiye masa tana zama a inda ta tashi

Kallon ta yayi yace, "baza ki koma rabon faɗan bane?"

Dariya tayi tace, "a'a kai ma ka san bazan koma ba tunda kana gida ka dawo. Ni akwai maganar ma da nake so mu yi da kai idan ka gama."

"Ok kiyi magana ai ina jin ki". Yafaɗa yana saka tuwon a bikin sa

Ita kuma gyara zaman ta tayi ta soma magana da faɗin, "dama gobe nake son in leƙa gidan mu; daga nan sai in wuce gidan Muhseen mu gaisa da Amarya".

Kallon ta yayi yace, "a'a ki bari zuwa jibi ki je hakan zai fi, zuwa lokacin na san na samu kuɗin da zan ba ki ko tsaraba ne ki yiwa su Hajiya. Ɗazu yaro ya kawo miki kayan miya ko?"

RAYUWAR CIKIN AUREWhere stories live. Discover now