Azare, Nigeria
Yau kwana hudu kenan da tafiyar Bilal Kano shi da Bappah Dattijo. Umma duk sai taji gidan ya mata shiru tunda ba wanda zatayi wa fada ko ta tada hankalinta akanshi. Musamman ma yau da su Fareeha suka tafi islamiyya ga Abba tun bayan asuba daya koma bacci bai tashi ba.
Sai ta samu kanta da yin aikace-aikacen da ba kasafai takeyi ba don kawai ta samu abunyi saboda in ta zauna hakan tunani zata shiga yi. Abun da kuma bata son yi kenan.
Ta gama 'yan abubuwan da zatayi sannan ta daura abincin rana. Daya ke masu zuwa gaishe da Abban sun dan dauke kafa sai tayi abincin dan daidai. Zuwa sha biyu yaran zasu dawo a Islamiyya bataso su dawo ba abinci.
"Lami" Abba ya kirata daga falon shi.
Ba laifi kwana biyu jikin yayi sauki don haka yanzu sai aka tattare shimfidin kwanciyar tasa aka mayar daki sannan aka sake gyara falon. Yanzu ya kan zauna akan kujerarsa wasu lokutan kuma ya kishingida a kasa.
Alhamdulillah har ya kan taba hira da abokansa masu zuwa dubiya. Da daddare kuma zai saurari radio ko kuma ya ce su Inaayah su zo su taya shi hira.
Ta shigo da sallama ta samu waje ta zauna a gefensa.
"Ga ni Abba"
A hankali ya jawo hannunta na dama ya damke a hannunsa na hagu. Wani dumi ya lullube zuciyarta.
"Na gode" ya furta idon sa na cikin nata idon.
Ba sai yayi wani dogon bayani ba, tasan me ya ke nufi.Yawu ne ya kafe a bakin ta ta rasa me zata ce. Kai kawai ta gyada sannan ta sunkuyar da kanta.
Da taga bashi da niyyar sakin hannun nata sai ta zame a hankali.
"Na bar abinci akan wuta" abinda ta ce da taga ya mata kallon tuhuma.
Bai ce komai ba ta tashi ta koma kitchen din.
Duk sai taji jikinta ya mata lakwas. Ta samu ta karasa abincin.
Azahar ta gabato dan haka ta shiga bandakinsa ta hada mishi ruwan alwala.
"Zo ki kamani" ya fada mata yana mika hannunsa a lokacin da ta ce ya tashi yayi alwala.
Murmushi dauke a fuskarta tace "Haba Abba, yaushe rabon da a maka jagoranci? Ina ce jikin da sauki yanzu?"
Ya kafeta da ido "To laifi ne Dan nace kizo ki dagani?"
"A'a ni bance ba"
Ba musu ta karasa wajensa ta riko hannun nasa. Har wani jingina yayi a jikinta wai shi a dole baya jin dadin jikin nasa. Dariya ta ke son yi amma ta gintse. Har kofar bandakin ta rakashi sannan ta dawo.
Fareeha tayi sallama suka shigo.
"Umma sannu da aiki"
"Sannu Adda am. Ya makaranta?"
Fareeha ta cire hijabinta ta lankaya a wuyanta "Alhamdulillah"
A daidai lokacin Qulsoom da Inaayah suka shigo da gudu.
"Ku kuma babu sallama?" Addan tasu ta watsa musu wani kallo.
Inaayah bata tsaya jin ta ba ma ta kara shigewa ciki da gudu. Qulsoom tayi sallama sannan ta wuce ciki.
"Kuje kuyi sallah kuzo kuci abinci" inji Umma.
Fareeha ta gyada kai ta bi bayan kannenta. Wanka duka sukayi dayake basu samu sunyi da safe ba sun makara. Fareeha ta jika uniform uniform nasu sannan suka zo sukaci abinci domin sai da sukayi sallah a islamiyyar kafin suka dawo gida.
Tana wanki ne ta ji sallamar kawarta Hafsatu. Dama tace mata zasuzo da mamanta duba Abban nasu don tun da aka sallamoshi sau daya tazo kuma ita kadai ne.
YOU ARE READING
Maktoub
Romance"Babu wanda ya ke tsallake kaddararsa a rayuwa Adda. Duk abunda kika ga ya faru dake to Allah ya riga ya rubuta tun kafin kizo duniyan nan. Hakuri zakiyi sai kuma kiyi Addu'a Allah ya baki ikon cin wannan jarabawar. Amma wannan al'amari rubutacce ne...