Godiya dubu dubu ga mabiya Wagga littafi. Idan baku ban san ya zanyi ba 💞.22.
Bacci take so tayi amma abun ya gagara. Bugu da kari ga kanta dayake sarawa tun dawowarsu a asibiti a dalilin dinkin da aka mata a kan nata. Buguwar da kanta yayi ne ya haddasa mata fashewar kai saidai Allah ya takaita abun iya fatar wajen ya tsaya be zurfafa ba don har su x-ray sai da akayi mata don a tabbatar. Hakan yasa likita ya bata shawarar samun ingattaccen hutu amma da alama abun ba zai yiwu ba.
Mutane ne ke ta kai komo a cikin gidan nasu don suzo su jajanta musu, abunka da zance marar dadi, labari duk ya game gari. Yanzu da wani abun alkhairin ne ya same ta ba lallai aji shi ba kamar yanda kowa ke saurin bada labarin wannan abun alhinin.
Wasu kam har sun kara Maggi a kai. Dukda cewa duk zuwan da masu jaje zasuyi Anti Mami sai ta kara jaddada musu cewa ba abunda ya samu Fareehan don su Hafsatu sun cetota kafin samarin su samu damar yin wani abun, amma hakan bai sa sun dena yada labarin cewa anyi mata fyaden ba.
Hakan ba karamin tayar wa Fareehan hankali yayi ba, amma babu yadda ta iya. Bata isa ta hanasu fadan abun da sukayi niyya ba, sai dai tasan ko ba dade ko ba jima, watarana gaskiya zata fito. Tana fatan Allah ya wanke mata wannan dattin da aka yaba mata. Amma kam ranta ya sosu.
Babban abun daya fi damunta shine taradaddin da take kwana da shi take tashi da shi. Hankalinta sam yaki kwanciya. Gani take yi kamar in ta kwanta mutanen nan zasu lallabo cikin dare su zo har dakinta su yi mata abun da sukayi niyya.
Ko da Baba Zubairu ya iso garin a washegarin faruwar abun, baiyi wata-wata ba ya hado kan 'yan sanda aka shiga unguwar aka tattaro Nazee aka tafi station da shi. Sai da ya sha bugu sosai sannan ya fadi sunan abokan nasa da kuma inda za'a samesu. Sai da aka kamosu tukunna hankalin Baba Zubairu ya kwanta.
A halin yanzu ma jira yake Fareeha ta nutsu su je police station din ta bayar da nata statement din.
Ita kam bata san me zata ce musu ba. Ko labarin ta gagara bawa Engineer dukda dai Anti Mami ta yi masa sharhi. Jiya da ya kira fashe masa tayi da kuka, abun da bata taba yi masa ba. Sosai hankalinsa ya tashi. Karfin hali yayi kawai ya fara kwantar mata da hankali da fada mata kalamai masu tausasa zuciya har ta samu ta dena kukan. Ya jadadda mata cewa yana tare da ita a kk wani irin hali kuma yana nan zuwa Azaren don ya duba lafiyar jikinta. A haka suka rabu zukatansu cike da alhini.
Turo kofar dakin da akayi ne ya saka ta saurin rufe idonta. Koma waye idan yaga tana bacci zai juya.
Maimakon taji an koma sai taji gefen gadon ya dan lotsa alamar mutum ya zauna a kusa da ita.
"Fareeha?" Muryar Hafsatu ta jiyo ta kirata a hankali.
Bude idanuwanta tayi ta sanya su cikin na aminiyar tata. Ta dan saukar mata da murmushi wanda bai kai har zuciya ba. "Yaya kika kara ji?"
Kallon ta Fareeha ta cigaba da yi dan bata san wani irin bayani zata mata ba don ta gane yanayin da take ciki a yanzu.
Hannu ta sa ta dan shafa bandejin da ke kan Fareehan wanda aka rufe dinkin da shi zuciyar ta tana kara karyewa ta kara da cewa "Sannu kinji? Sannu"
Fareeha ta lumshe ido wanda hakan ya bawa hawayenta daman gangarawa gefen fuskarta. Ta ina ma zata fara mancewa da wanann al'amari bayan ga tabo sun bar mata? Sannan ga askin da aka mata a gefen kai duk dan a samu a mata dinki me kyau.
Sun cuce ta. Sun ruguza mata rayuwa.
Rungumeta da Hafsatun tayi ne ta gane cewa ashe ta fashe da kuka ne.
A haka Anti Mami ta shigo ta samesu duk su biyun sai kuka suke.
"Haba Hafsatu. Ke da zaki rarrasheta ki kwantar mata da hankali, shine kika biye mata kuke koke-koke? Kukan da ba zai kare mu da komai ba?"
YOU ARE READING
Maktoub
Romance"Babu wanda ya ke tsallake kaddararsa a rayuwa Adda. Duk abunda kika ga ya faru dake to Allah ya riga ya rubuta tun kafin kizo duniyan nan. Hakuri zakiyi sai kuma kiyi Addu'a Allah ya baki ikon cin wannan jarabawar. Amma wannan al'amari rubutacce ne...