4.

1.8K 174 47
                                    

Salaaam Alaikum everyone. Sorry for my silence.

4.

Abban Bilal bai farka ba sai washegari da Asuba. Umma kam kwana tayi tana roqon Allah ya ceci ran mijinta. Daga qarshe haqura tayi ta kira Balaraba ta sanar da su Fareeha halin da ake ciki. Inaayaah kam har da kukanta wai zata taho. Ta dai basu haquri tace su tayasu da Addua. Dada ma tayi jajen abun. Ta yi wa Umma alqawarin cewa gari yana wayewa Balaraba zata rako yaran insha Allah.

Fitar da tayi zuwa bandaki domin ta kama ruwa kuma tayi alwala ne ya farkar da Abban Bilal din. Ta dawo kenan tana qoqarin fuskantar alqibla kawai sai taga idonshi a kanta. Gabanta yayi mummunar faduwa. Suka tsaya suna kallon kallo. Abubuwa da ta dade bataji game dashi ba taji sun taru wake daya sun dunqule a can cikin zuciyatrta. Da qyar bakinta ya motsa

"Sannu Abban Bilal. Ya jikin?"

Kai kawai ya iya daga mata saboda wani azababben zafi da ya keji tun daga qaramar yatsar qafarshi har zuwa qasan kanshi. Sake runtse idonshi yake ko hakan zai sama mishi sauqin ciwon dayakeji amma kamar an qara rura wutar ciwon.

Ta dan dafa gadon tana matsowa kusa dashi. "Akwai abinda kakeso? Ko in kira doctor?"

Kasa motsawa yayi balle ma ya bude baki ya fada mata irin azabar dayake sha. Wata ajiyar zuciya ta saki kafin nan ya bude idanuwan nashi ya sauke su a kanta.

"Sannu. Sannu kaji" abinda tace kenan domin ta karanto abunda ke kwance a cikin idanuwan nashi.

Ya dan gyada mata kai kadan.

"Me kakeso? In baka ruwa kasha? Ko in taimaka maka ka zauna?" Ita kanta bata san daga ina wadannan tambayoyin suke zuwa mata ba, kawai ta tsinci kanta da yi mishi su.

Bai bata amsa ba illa lalumo hannunta da yayi ya damqe cikin nashi ko zai samu sauqin azabar dayakeji din. Wani baqon abu taji ya ziyarci dukkan ilahirin jikinta har yana barazanar fasa mata kwanya.

Shikuwa sake lumshe idon nashi yayi. Tana durqushe a wajen hannunshi na cikin nata har wani baccin ya sake daukeshi. A hankali ta zare hannun nata sannan ta tashi ta gabatar da sallar Asuba domin har lokaci ma ya wuce.

Ta na nan zaune a kan sallayar har nurses sukayi canjin shift; 'yan dare suka saki aikinsu wa 'yan safe. Wata nurse ta shigo dakin tana dudduba marasa lafiyan har ta iso gadon nasu. Suka gaisa ta tambayeta ya mai jiki ta amsa da lafiya hadi da sanar mata cewa har ya farka dazun. Nurse ta danyi wasu rubuce rubuce a jikin wani littafi dake maqale a kan gadon sannan ta cire mishi ledar jini da ta drip din wanda tuni duk sun qare.

"Doctor zai shigo nan da one hour insha Allah " fadar nurse din kafin ta mata sallama ta fita.

Fitar nurse din keda wuya saiga kira yana shigowa wayar Umman. Maman Walid ce don haka tayi saurin dauka. Suka gaisa ta tambayi mai jiki tace da sauqi.

"Umma ko akwai wani abunda kikeso in kawo muku daga gidan? Ina tura yara makaranta nima zan taho insha Allah"

Umma ta nisa tana jinjina qoqarin maqociyar tasu. "Babu komai Maman Walid. Dama kinyi zamanki basai kinzo ba"

"A'a Umma ga abinci kari har na dafa ai ya kamata kici wani abu a cikinki indai kema ba jinyar kikeso ki fara ba"

Dan guntun murmushi ya kubce mata. "Toh mungode. Sai kinzo"

Har zata katse wayan ta dakatar da ita.

"Nikam Baban Walid yace miki ko yaga Bilal? Tun jiya fa na kasa samunshi a waya na fada wa Baban Walid din yace ze nemeshi a unguwa"

Maman Walid ta danyi jim. Bata son sanar da Umman halin da ake ciki domin hankalinta ne sai qara tashi. Ita ce ma ta hana Baban Walid din kiran Umman, don da shi niyyar shi ya sanar mata halin da ake ciki.

MaktoubWhere stories live. Discover now