25.

831 121 70
                                    

Assalamu Alaikum.
Kai na bisa wuyana, a min hakuri. I hope this chapter pays for all my misgivings.

25.

PHOENIX, ARIZONA

Zaune yake a dakin da aka kama musu na hutun wucin gadi wanda tsawon sa bai wuce na awa hudu ba. Iska ce mai sanyi ke busowa daga na'urar sanyaya dakin don ba laifi garin akwai zafi Masha Allah.

A watan daya wuce aka mishi canjin yanayin tafiyar tasa ta koma daga New York zuwa Arizona. Wannan yasa yanzu kwanakin aikin nasa suka ragu saboda tafiyar ta kara tsawo; yana tuki zuwa garuruwan sau uku a sati inda yake da hutun kwana uku a satin.

Tun shigowarsa daya gabatar da sallar la'asar bai motsa daga inda yake ba. In banda takalmansa daya cire da jacket dinsa har yanzu uniform dinsa na jikinsa. Yana so ya tashi ya dan watsa ruwa ya runtsa ko da na awa biyu ne kafin lokacin tashi, amma tunani ne fal ranshi.

Hirar da sukayi da Mami ne a kwanakin da suka shude ne ke ta yawo a kanshi.

Sam bai ji dadin labarin daya samu game da Fareeha ba, abun ya dame shi matuka don daga bayanin da Mami ta mishi babu tantama depression ne yake damun yarinyar. Kuma shi yasan me depression ke haifar wa a rayuwar dan adam tunda shima a wasu lokuta da suka shude ya tsinci kanshi a irin wannan yanayin. Yayi imani da cewa ba wayon sa bane ko dabarar sa ta fito dashi daga duhun da ya shiga a rayuwar sa; addu'ar mahaifiya ne da kuma rahamar Ubangiji suka kubtar da shi

Don haka jin cewa Fareeha ma tana cikin wannan yanayi ya sa abun ya dame shi sosai.

A da ya dauka aurenta da zaiyi zai kawo wa iyayenta da ita kanta mafita daga halin da suka shiga ciki, amma yanzu ya lura aure shine abu na karshe da take bukata a rayuwarta.

Tana bukatar kulawa. Tana bukatar wani a kusa da ita wanda zai saurareta ya ji damuwarta. Tana bukatar a bi da ita a hankali. Babban abun kuma shi ne tana bukatar lokaci.

A ranshi yake lissafa hanyoyin da suka dace wajen taimakonta da kuma guddumawar da yakamata ya bayar wajen taimakon, amma sai yaji wuta ta dauke a cikin kanshi.

A lokacin ne kuma ya tsinci kanshi a wani yanayi na son yaye mata duk wata damuwar da ta ke ciki, na son zame mata abun dogaro da kuma tudun dafawa. Ya ji dama ace zai iya zame mata bango wanda zai kareta daga dukkan wani abun da zai cutar da ita.

Sai dai kash!, ta mishi nisa. Teku ne babba a tsakaninsu.

Wayar sa ya daga ya duba lokaci. Karfe sha dayan dare a Najeriya yanzu, ba zai iya kiranta ba. Tsawon lokacin nan yana ajiye da lambarta a wayar shi daidai da rana daya bai taba tunanin kiranta ba sai yau. Gashi hakan ba zai yiwu ba.

Runtse idanuwansa yayi ya sauke nannauyar ajiyar zuciya. Duk sai yaji kamar ba shi ma da amfani a duniya. Duk abubuwan da yakeson aiwatarwa a wannan lokacin sun gagara.

Sake sauke wata ajiyar zuciyar yayi ya mikar da kafafunsa akan sallayar.

Yarinyar da bai taba gani ba amma lokaci daya ta shige kansa da rayuwarsa ta kudindine, ga wani abu dake zaburar da shi na son kareta da boyeta daga duk abun da zai cutar da ita. Wannan wace irin jarabawa ce?

Jiki babu kwari ya tashi ya shiga bandaki ya dan watsa ruwa sannan yazo ya kwanta.

Ba wani bacci ya samu sosai ba amma lokacin da ya tashi sai ya ji dan dama-dama. Sallah kawai yayi ya sanya uniform dinsa sannan ya ja dan karamin akwatinsa ya fice a dakin. A lobby suka hadu da co-pilot din sa da sauran ma'aikatan jirgin nasu (flight crew). Bayan sun bada makullan dakunan nasu suka shige cikin bus din da tazo daukar su domin maida su filin jirgin dayake babu nisa da masaukin nasu.

MaktoubWhere stories live. Discover now