Spoilerrrrrrrrrrr alertttttt.
This is the chapter where we get married y'all 👰🏽♀️🤍💍💐.
30.
Dawowarsu kenan daga gidan Mama Uwani. Tun bayan da ta gama jarabawa da ta dawo gida su Inaayah suke ta damun ta akan suna so suje don suma sunyi hutu a lokacin. A lokacin ne kuma aka sallamo Abba a asibiti don haka sai ta maida hankalin ta kacokam wajen taimakawa Umma kula da shi da kuma aikin gida.
Yau din sun tashi jikin da sauki don haka Umma ta ce su tattara suje su gano yayar tata don itama ta sha sintiri akan su tunda Abban ya kwanta.
A bakin layi mai keke napep din ya sauke su don haka takowa sukayi suka karaso.
Inaayah da Qulsoom sun rigata shigewa gida don su suna gaba ita kuma tana rike da hannun Ahmadi shiyasa bata tafiya da sauri.
Kamar daga sama taji ance "Hauwa"
Ko a mafarki ko a farke idan taji wannan muryar tasan waye mammalakin ta.
Sake kankame hannun Ahmadi tayi tana juyawa don ta tabbatar da abun da kunnuwanta suka jiye mata.
A lokacin ne kuma ta fahimci me hausawa suke nufi idan sunce mutum ya tsorata kamar yaga fatalwa, don kuwa abun da taji a lokacin da tayi ido hudu da Engineer Faruk ya wuce tsoro, ya wuce fargaba. Ba ta ma san da me zata kwatan ta shi ba.
"Innalillahi wa inna ilaihi raajiun" abun da ta iya furtawa kenan kawai.
Sakin hannun Ahmadi tayi inda shi kuma ya ruga gida da gudu.
A hankali Faruk ya fara takowa inda take, yayin da ita kuma ta fara ja da baya.
"Hauwa please ki tsaya muyi magana" muryarshi can kasa kamar me shirin yin kuka "awa ta biyu a nan ina jiran naga giftawarki saboda bani da karfin gwiwar shiga cikin gidanku"
"Me ya kawo ka nan?"
Jin tambayar tata yayi kamar ta watsa masa garwashin wuta.
"Wajen ki nazo"
Cigaba da kallon sa take kamar har yanzu bata gasgata shi dinne a gaban ta ba.
Ya karanci halin da ta shiga a lokacin don shima kusan hakan ne a wajen shi.
Ya cigaba da magana.
"Magana nazo muyi Hauwa. Please kiyi hakuri ki saurareni"
Wani abu ta hadiya mikit. Yaji-yaji takeji a idon ta wanda ya nuna alamun cewa kiris ya rage ta fara hawaye. Nan da nan kuwa ta danne su.
Ba shi da wannan matsayin a rayuwar ta da zata tsaya tana zubar kwalla saboda shi. Yayi kadan.
"Ina jinka"
Maganar da ya zo da ita bata cancanci suyi ta a tsaye a kofar gida ba amma yanda yaga yanayin ta yasan bata da niyyar ce masa ya shigo. Hasalima yana ganin idan ya tsaya bata lokaci to zata iya shigewa ta bar shi a wajen.
Shi kuma yazo ne da kudiri babba a ransa, kuma yana fatan ta saurare shi ko da kuwa na minti daya ne.
Ba tare da bata lokaci ba ya shiga bata hakuri akan irin rabuwar da sukayi da yadda bai neme ta ba tsawon lokacin nan da kuma karin bayani akan yadda dangin sa suka hana shi auren ta a bisa dalilin abun da ya faru da ita.
Tun da ya fara magana kawai jin shi take, sai da taji yace "I want you to give us a second chance Hauwa" tukunna ta dawo daga duniyar tunanin data fada.
YOU ARE READING
Maktoub
Romance"Babu wanda ya ke tsallake kaddararsa a rayuwa Adda. Duk abunda kika ga ya faru dake to Allah ya riga ya rubuta tun kafin kizo duniyan nan. Hakuri zakiyi sai kuma kiyi Addu'a Allah ya baki ikon cin wannan jarabawar. Amma wannan al'amari rubutacce ne...