Littafi ne a bude a kan cinyarta. Duk wanda ya kalleta zaiyi zaton karatu take don gaba daya hankalinta yana kan littafin, amma a zahirin gaskiya tunani me zurfi take.
Tunanin Muazzam take da sauyin data gani a tattare dashi tun ba yau ba. Tsakaninshi da ita babu boye-boye don sun taso rayuwarsu daga ita sai shi. Mahaifinsa ya rasu tun yana karami don haka ita ta zame masa komai a rayuwarshi. Sunyi shakuwa matuka da babu abun da yake boye mata a rayuwarsa; ko ya boyen ma shi da kansa yake zuwa ya fada mata daga baya. Ita ce babbar aminiyarsa wanda tasan duka sirrikansa a fadin duniyan nan.
Ko lokacin da ya auri Najmah idan yazo wajenta neman wata shawara game da aikinsa ko abin da ya shafi lafiyarsa, sai tace masa yaje yayi shawara da matarsa tukun. Amma hakan bazai hanashi zuw washegari da wata matsalar ba. Ya riga ya saba ita ce komin sa.
Ita dinma kuma kusan hakan ne. Duk inda ta waiwaiya in tana neman shawara shi take fara kira. Shine abokin hirarta shine me bata shawara kuma shine babban abokinta. Kuma bata fata hakan ya canza a tsakaninsu.
Amma kwanan nan sai taga kaman akwai abun da yake boye mata. Da ta tambayeshi kuma sai yace mata babu komai. Ta hango rashin gaskiya karara a idonsa amma sai ta kyale tana jiran ranar da zaizo da kanshi ya sanar da ita abunda yake faruwa. Amma sai me? Shiru shiru har yanzu ranar batazo ba, har ta gaji da jira. Hankalinta kuma kara tashi yake don ta lura ko ma meye Muazzam yake ciki to ba alkhairi bane.
Bazatace ga abunda take tunanin shi ne matsalar ba amma har cikin zuciyarta tasan yana cikin matsala kuma yana bukatar taimako.
Ajiyar zuciya ta sauke kafin nan ta lalubo wayarta dake gefen ta. Yau sati biyu kenan rabon da ta saka shi a idonta, abun da bai taba yi ba kenan a rayuwarshi. Baya sati bai leko ta duk kuwa irin matsin da ke cikin aikinsa. Amma ace har sati ba daya ba, har biyu, kwana goma sha hudu, amma babu labarinsa.
Kai tsaye kiran nata voice-mail ya shiga alamar cewa wayar tashi ma ba a kunne take ba.
Babbar magana.
Tashi tayi daga mazauninta ta nufi bandaki. Alwala tayi ta dawo parlon nata ta shimfida babbar daddumarta ta fuskanci gabas.
Sallar walaha ta gabatar sannan ta zauna ta danyi karatun alkur'ani ko zata samu nustuwa. Ta dan jima tana karatun kafin ta rufe ta daga hannunta ta fara Addu'a. Wayarta ce ta shiga ringing. Har za ta katse addu'o'in nata a tunaninta ko Muazzam dinne yake kira amma sai ta cigaba da zayyano wa Ubangijin Rahama matsalolinta kuma ta nemi taimakonSa a dukkan lamuranta. Tana idarwa ta jawo wayar sai taga Anti Bebi ce ta kirata.
Ta dan murmusa kafin ta kirata.
"Mama Amma am" muryar Anti Bebi ta jiyo daga daya bangaren. "Ina kwana ne ko ina wuni?"
Amma tayi dariya "Yanzu kam safiya ne anan. Yaya kuke?"
"Lafiya Alhamdulillah. Yaya kanina?"
Amma ta danyi Jimm kafin tace "Kwana biyu ban ganshi ba amma yana nan lafiya Alhamdulillah"
Anti Bebi ta yi ajiyar zuciya "Amma da dai ya dawo gida yanzu tun da shi kadai ne. Kema kina bukatar wani a kusa da ke ai ko kuwa?"
Ta danyi murmushi wanda yafi kuka ciwo. "To Bebi ai yanzu kam ya riga da ya saba da zama shi kadai. Kuma ni dinma na kusa dawowa gida inshaAllah "
"Kai haba? Gaba daya?"
Amma ta jinjina kai kamar Anti Bebin na gabanta. "Haka nake fata. Nayi applying for early retirement. Zuwa dai wata shekarar inshaAllah"
"Kai Alhamdulillah. Amma nayi murna. InshaAllah kina nan za ai biki"
"Ke kam dai har yanzu baki daina zancen bikin nan ba. Ni na dauka ma an fasa" Amma ta fada tana dariya.
YOU ARE READING
Maktoub
Romance"Babu wanda ya ke tsallake kaddararsa a rayuwa Adda. Duk abunda kika ga ya faru dake to Allah ya riga ya rubuta tun kafin kizo duniyan nan. Hakuri zakiyi sai kuma kiyi Addu'a Allah ya baki ikon cin wannan jarabawar. Amma wannan al'amari rubutacce ne...