23.
Gidan tsit kamar ba kowa dukda cewa kuwa duk yaran suna gida; Fadila da Baba Habu sun samu hutu suma duk da yake Yusrah ta riga su fara nata hutun, sannan Samha ma ta zo musu wuni. Maimakon duk a hadu a danyi hirar yaushe gamo, sai kowa ya shiga sha'anin sa kawai. Samha kam ma tana zuwa da Amina ta karbi babynta sai ta samu waje a falon Anti Bebi ta bige da bacci. Kwana biyun nan bata samun isashen bacci gashi tunda akayi wa mijinta transfer ya dawo aiki Kano shikenan bata da hutu, kullum tana cikin hidimar sa da hidimar gidan.
Anti Bebi na dakinta tana nade wasu kayyayakinta da aka karbo daga wurin tela tunani ne fal ranta ga abubuwa da dama da suka hadu waje guda suka mata cunkus a cikin kanta. Ta rasa ta ina zata fara warware su.
Ajiyar zuciya ta saki kafin ta dauki wayarta da ke gefenta ta shiga neman lambar Ashraf. Tun safe ta mishi text akan tana da magana da shi idan ya dawo gida ya nemeta, ya amsa mata da to.
Gashi yanzu har kusan la'asar bata ji duriyar sa ba don haka ta kira taji me yake ciki tunda de yau weekend kuma dama yace kasuwa kawai zasu je shi da Umar don siyo wasu kayyayakin aiki na shagon su.
Bugu biyu ya dauka.
"Assalamu Alaikum Mama"
"Wa alaikum salam, naji shiru. Har yanzu baka dawo bane?"
Ashraf dake zaune a cikin motar shi wanda yayi parking a kofar wani shagon saida kayan kwalliya ya sosa keyarsa yana fadin "Wallahi Mama wani dan uzuri ne ya rike ni amma gani nan dawowa inshaAllah"
"Toh Allah ya kiyaye" kawai tace ta katse wayar.
Ajiyar zuciya ya saki bayan ya katse wayar. Ya lumshe idanunsa tare da tallafe kansa.
Ya gaji tulus saboda zirga zirgar da sukayi shi da Umar a kasuwa, gashi ko karyawa baiyi ba ya fito. Sai da ya kama hanyar gida ne bayan ya ajiye Umar din ya samu kiran Wafiyya akan tana so ya dauko ta daga wajen dentist inda aka mata wankin hakori. Ya zaci gida zai mika ta sai kuma tace su tsaya tana da sakon da zata karba. Kaya ta siya daga Lagos sai aka hado a kayan wata kawarta shine ta tsaya a shagon don ta karba. Gashi yanzu kusan minti talatin yana jira bata fito ba.
Wata ajiyar zuciyar ya sake saukewa yana kokarin rarrashin zuciyar sa don yanzu kam ran shi ya fara baci.
Da wanne zaiji daya? Gajiyar da yayi ko kuma yunwar daya ke ji? Gashi ta zo ta wani shanya shi kaman wani direban ta? Ta ci sa'ar sa ne kawai, amma kaf cikin kannensa ba wanda ya isa ya masa haka.
Ya dauki wayar sa domin ya kirata kenan sai gashi ta taho da kaya niki-niki a hannunta tana doso motar.
A hankali ya fito a motar ya bude mata gidan baya ba tare da ya ce komai ba. Tana ganin yanayin fuskar sa ta san ta tafka lefi.
Kayan ta zuba a ciki sannan ya rufe kofar ya zagaya domin ya koma mazauninsa na direba.
"Hayati kayi hakuri wallahi kayan ne ba a gansu ba sai da aka shiga store aka binciko min su" ta fada tana dan karya wuyanta, muryar ta cike da ban hakuri.
Girgiza mata kai kawai yayi ya shige motar.
"Hayati manaaa!" ta kira da sigar shagwaba tana makala seat belt dinta. Ka'idar sa ce in dai zaka shiga motar sa kuma zaka zauna a gaba to sai ka saka seat belt. Ita kam yanzu har ta saba.
"Ya wuce" kawai ya fada a takaice ya taka motar. Bai ma tambayeta ina zai sake kaita ba, hanyar gidan su kawai ya nufa.
Haka suka karasa ba wanda yace wa kowa komai.
Yana tsaida motar Wafiyya ta juyo ta zuba mishi kyawawan idanunta. "Haba mana Hayati. Nace fa kayi hakuri. Nima ba a son raina na bar ka kana ta jira na ba fa. Ka daina fushi dani dan Allah. Raina baya so" ta san halinsa sarai, yanzu a kan abinnan sai ya share ta na tsawon kwanaki, ita kuwa Allah ya jarabceta da sonshi don ko kwana daya akayi basuyi waya ba ko bata ganshi ba gaba daya sai ta kasa sukuni.
YOU ARE READING
Maktoub
Romance"Babu wanda ya ke tsallake kaddararsa a rayuwa Adda. Duk abunda kika ga ya faru dake to Allah ya riga ya rubuta tun kafin kizo duniyan nan. Hakuri zakiyi sai kuma kiyi Addu'a Allah ya baki ikon cin wannan jarabawar. Amma wannan al'amari rubutacce ne...