Inyeh!!!. Ku tafa min dan Allah😂
27.
Tsayawa sukayi kallon-kallo, kowa da abun da ke gudana a cikin ransa.
Shi dai Mu'azzam in banda tasbihi ga Allah babu abinda yakeyi. Nutsuwa ne da wani farin ciki yaji sun mamaye shi lokaci guda a dalilin ganin ta tsaye a gabanshi.
Fatabarakallahu ahsanul khaliqeen.
Wata guda kenan rabon da ta saurare shi, bai ma san ya akayi yayi hakuri har haka ba don yanda wani abu ke fizgar shi ji yayi kamar yayi tsuntsuwa yazo inda take ya fuskance ta.
Horon da ta mishi yayi tsanani matuka. Babu hanyar da bai bi wajen lallaminta amma ta kafe ta tsare, karshe dai abun da yake gudu shi ya faru. Blocking dinsa tayi.
Bata san hakan data yin ba kuwa kara tunzura shi tayi. Wannan ne dalilin daya sa ya kara jin dole-dole yazo ya same ta ya kalle ta cikin ido ya sanar mata da kudurinsa a kanta.
Ya san ya tafka kuskure wajen shigan saurin dayayi mata, yaso ace ya bita a hankali tukunna. Amma yayi gajen hakuri.
To yanzu dai koma menene, gashi nan yazo, kuma ba zai koma inda ya fito ba, sai ya aiwatar da abun da yayi niyya. Ko da kuwa ba yau bane.
Duk abun da zai faru, sai dai ya faru.
"Me kakeyi anan?" Ta furta a hankali.
Har yanzu zuciyarta bata daina sassarfa ba don sam ta kasa yarda da abunda take gani.
Murmushi yayi wanda ya kara masa kyau sannan yace "Wajen ki nazo". Ganin kallon rashin fahimtar da take mishi yasa shi karawa da "Nazo ne na bada hakuri akan laifin danayi miki wanda mind you, bansan menene ba. Amma dai punishment din ya isa haka dan Allah. Ayi min afuwa"
Kankance idon ta tayi akanshi wanda hakan yaso ya bashi dariya.
Bai san me yayi ba? Karar da ya kaita wajen Anti Mami kuma fa?
Gyara tsayuwar ta tayi sannan tace "Ni ba abun da kayi min kawai dai...."
Ya karya wuyansa "Kawai dai me?"
Yanda ya tsare ta da idanunsan nan sai ta kasa fadin abun dayake ranta. Gaba daya sai taga ya mata wani kwarjini. Dukda dan durkusowar da yayi hakan bai sa sai ta daga kai take iya kallon shi cikin ido ba, don haka ta sunkuyar da kanta.
"Kayi hakuri idan abun da nayi ya bata maka rai. Kawai dai naga hakan danayi shi ya fi"
"Meyasa?"
Ta dan dago ta kalleshi kafin ta sake sunkuyar da kanta. "Saboda banga amfanin alakar mu ba"
Kallonta yakeyi a yayinda wani abu ke yawo a cikin zuciyarsa. Alakarsu bata da amfani fa tace? Lallai akwai aiki a gabansa.
Murmushin gefen lebe yayi yace "To za'a bani dama dan in nuna amfanin wannan alakar?"
Ji tayi kamar ta shake shi.
Ita ba karamar yarinya bace, don haka ta fara gano inda ya dosa.
Bazata iya bane kawai. Da wani ido zata kalli Anti Mami?
"Kayi hakuri dan Allah" muryarta har rawa takeyi kamar me shirin yin kuka.
Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya daga kai ya kalli sama, sannan ya sauke.
"Mamish tace min zaki tafi gida gobe. Yaushe zaki dawo?"
To yanzu kuma rahoto ake bayar wa a kanta wato? Yau tana ga ikon Allah.
"Ban sa ranar dawowa ba. Mid semester break dinmu sati biyu ne, to kafin dai ya kare zan dawo inshaAllah"
Kwana uku take da niyyar yi idan ta je don suna dawowa da sati biyu zasu fara exams, tana so ta dawo ta yi karatu don wannan karon bata son carry over ko kwalli daya. Bata fada mishi hakan bane kawai don tana fata kafin ta dawo ya koma inda ya fito don da dukkan alamu ba wai yazo kasar bane da niyyar dadewa.
YOU ARE READING
Maktoub
Romance"Babu wanda ya ke tsallake kaddararsa a rayuwa Adda. Duk abunda kika ga ya faru dake to Allah ya riga ya rubuta tun kafin kizo duniyan nan. Hakuri zakiyi sai kuma kiyi Addu'a Allah ya baki ikon cin wannan jarabawar. Amma wannan al'amari rubutacce ne...