This chapter is so far my favorite. Jama'a I love loooovvvveeee. Allah ya bar mana love🥰🥰🥰.
32.
"Wannan fa a ina za'a saka?" Yusrah ta tambaya hannunta rike da wani agogo me kyau. Dukkansu suka daga ido suka kalli agogon da ke manne a bangon falon sannan suka sake kallon na hannun nata. Dukka biyun sunyi kyau kuma sun cancanci a saka su a parlor din.
Anty Zu ta kalli Fareeha sannan tace "Ko a sa miki shi a daki?"
Fareeha ta danyi guntun murmushi wanda ke cike da gajiya ta ce "Ko a ina ma aka saka Anti ba matsala"
Yusrah ta tabe baki "Se da mukace ki zauna ai kar ki taho, gashi yanzu kinzo kina ta wani mashangwale"
Aunty Zu ta kalleta ta gefen ido. "Oh ni Zuwaira. Ke kam bakin ki baya taba shiru ko?"
Yusrah bata bada amsa ba ta wuce da agogon daya daga cikin dakunan da suka gama shiryawa don ta kafa shi. Idan ba don kayan sunyi yawa ba ma yaushe ake wani kafa agogo a daki?
Kaya ne gasu nan an rasa yanda za'a yi da su; Bappah Dattijo ya siya Baba Zubairu ya siya ga oga kwata-kwata Mu'azzam shima ya siyo su.
A jiya aka bashi mukullan gidan wanda daya daga cikin gidajen Prof ne ya bashi aro don ya kasa samun irin gidan daya ke so. A jiyan kuma ya tattaro masu gyaran wuta da na famfo aka canja mishi wutace da socket din gidan da kuma kan famfuna da su sink da shadda ma duk sake su akayi. Har karfe sha daya yana tsaye akan kafafun shi yana jiran masu fenti su gama nasu aikin.
Abincin daren da yake yawan zuwa ci a gidan Ammah ma jiya be samu yaje ba se hotel dinshi ya koma ya sha tea da cookies ya kwanta.
Yau kuwa suna iso wa gidan da safe suka same shi shima ya riga da yazo da akori kura an dora mata kayan wuta dangin su firij da talabijin da freezer da injin wanki.
Haka Fareeha ta tsaya tana kallon su suna ta sauke kaya. Ba'a gama wannan ba kuma sai ga Anti Bebi ita ma ta iso da mota shake da kayan katako wanda kana gani kasan showroom kawai ta shiga ta zabo su.
Aiki suka shiga yi babu kakkautawa don a ranar Mu'azzam yace yake so ta tare.
Tun safe suke ta aiki gashi yanzu har an fara kiraye-kirayen sallar Maghreb. Gajiya iya gajiya sun gama yi amma Alhamdulillah sun ci karfin aikin kuma komai yayi daidai. Abubuwan da ba'a karasa ba kadan ne kuma ko gobe ma zasu iya karasawa.
Alwala Fareeha ta shiga tayi kafin ta fito ta kabbara sallah. Tun kafin ta idar ta ji shigowar shi yana yi wa su Anti Zu sannu da aiki.
Tana idar wa kuwa sai gashi ya shigo.
"Sannu da dawowa" ta furta a hankali bayan ta kammala azkar dinta na bayan sallah.
Dagowa yayi daga kallon da yake wa wayar sa ya kalleta. Kankance idon sa da yayi a kanta yasa hantar cikin ta kadawa. Rabon da yayi mata wannan kallon tun ranar da suka fara haduwa taki karban kyautar daya bata.
Kafin ta bude baki ya mike yana fadin "In kin gama kizo"
Ta saba idan tayi farilla tana tashi ta kara da Nafila, yau kam tashi tayi ta nade sallayar sannan ta bi bayan shi.
Ta zaci a falo ze tsaya kawai sai taga ya kama hanyar waje.
Nan da nan zuciyar ta ta sauya bugu.
Anti Balaraba data idar da sallah a falon dauke ido tayi kaman bata gansu ba har suka fice.
Sai da ya isa wajen mota tukunna ya bude kofar fasinja. Ba tare da ya juyo ya kalleta ba yace "Shiga"
Wani abu ta hadiye a wuyan ta kafin ta shiga motar ya turo kofar ya rufe.
YOU ARE READING
Maktoub
Romance"Babu wanda ya ke tsallake kaddararsa a rayuwa Adda. Duk abunda kika ga ya faru dake to Allah ya riga ya rubuta tun kafin kizo duniyan nan. Hakuri zakiyi sai kuma kiyi Addu'a Allah ya baki ikon cin wannan jarabawar. Amma wannan al'amari rubutacce ne...