Ba zan gaji da yi muku godiya ba. The massive love this book is getting on this app is beyond me. Allah ya saka muku da mafificin alheri Ameen🤍.
26.
Fareeha ta kurawa notice board din ido tana kallon sakamakon jarabawar ta na semistar farko. Abun ba'a cewa komai don Alhamdulillah tayi kokari saidai kwas guda daya ya dawo mata da katotuwar F.
Gwauron numfashi taja kafin ta matsa a wajen don bawa wasu dama suma suga nasu sakamakon.
Ko da ta fito a department din nasu, sai ta kama hanyar get. Tana da lakcha karfe hudu amma gaba daya sai taji ran ta ya dagule, so take kawai ta ganta a gida.
A adaidaita kam har da dan kwallar ta.
Tana isowa gida taga Samha sunzo ita da Anti Balaraba, nan ta hadiye duk wani bakin ciki da take ji ta sake ranta suka gaisa da fara'a.
Shirye-shiryen bikin Ya Ashraf sun kankama don haka Samha da Anti Balaraba kullum suna sintirin zuwa gidan da zuwa kasuwa. Wasu lokutan kuma Anti Bebin ce take zuwa can gidan Anti Balaraban su hadu a can.
Kaya kam har an kusa kammala hada su abinka da kudi a aljihu. Abubuwan da suka rage kalilan ne su dinma don dai kawai a cika akwati ne amma idan babu su dinma kayan sun wadatar haka.
Sun ma daina zancen kaya yanzu zancen saukar baki ake da yadda za'a tarbi amarya da sauran dai al'adun da za'a gabatar a bikin tunda har an saka rana.
Ya Ashraf yace baya son wani taro amma Wafiyya ta riga ta yanke shawara zatayi Kamu da kuma Arabian Night. Da farko yace suyi abunsu su kadai amma dai an samu an shawo kansa da kyar sannan yace zai je wajen event din amma ba ze dade ba.
Ganin yadda aka kai ruwa rana da shi ne ma yasa su Anti Bebi suka yanke shawarar baza'a yi wani taro anan dinba sai dai kawai Wuni da za'a yi in an daura aure. Budan kai dinma yace baya so kawai a kai masa amaryar sa a musu fatan alheri da Addu'a kowa ya watse.
"Mu a saukin mu ai" Anti Balaraba ke cewa "Yo ko da abincin baki aka bar mutum ai an barshi da aiki. Hakan ma yayi ayi wunin kawai kowa ya koma inda ya fito. Allah ya sanya musu alheri"
"Ameen" Anti Bebi ta amsa. Ita dai taso ace a dan yi wani abu daga bangaren angon, ko da kuwa 'yar dinner ce. Duk da ba shine bikin ta na farko ba, amma shine bikin namiji da zatayi na farko, ya kamata ta fito a maman ango dinta kowa ya ganta. Amma hakan ma yayi ba komai.
Addu'a ta bisu da shi a ranta kawai.
Sai bayan Maghreb sannan suka watse. Mijin Samha ne yazo daukar su. Bayan ya shigo gaida Anti Bebi ta rike shi akan lallai sai yaci abinci tunda daga wajen aiki ya taho. Sai da yaci tukunna suka tafi.
Amina ta sake share falon tayi mopping kafin nan Fareeha ta kunna turaren wuta a electric burner.
Zama tayi a wajen ta kira Ummanta ta sanar mata sakamakon nata.
"Ai kinyi kokari Adda. Banga abun tayar da hankali ba. InshaAllah nan gaba sai ki kara kokari. Allah yasa kifi haka"
Hawaye ne taji sun cika mata ido tap! Tayi kewar Ummanta matuka. A lokacin ta ji kamar tayi tsuntsuwa taji ta a cikin rikon ta, ta shaki kamshin ta ta kuma ji dumin jikinta.
"Ameen Umma. Yaya Abba?"
Umma taja numfashi kafin tace "Alhamdulillah kawai za'a ce. Yana nan dai yadda kika barshi, sai Addu'a"
Ta hadiyi wani kulliti a makogoronta. "Allah ya tashi kafadun shi yasa kaffara ne"
"Amin Amin. Ga Qulsoom wai zaku gaisa"
YOU ARE READING
Maktoub
Romance"Babu wanda ya ke tsallake kaddararsa a rayuwa Adda. Duk abunda kika ga ya faru dake to Allah ya riga ya rubuta tun kafin kizo duniyan nan. Hakuri zakiyi sai kuma kiyi Addu'a Allah ya baki ikon cin wannan jarabawar. Amma wannan al'amari rubutacce ne...