*ABINDA AKA GASA...!*
_Shi yaga wuta..._🔥
*_TRUE LIFE STORY_*By
_Hafsat A Garkuwa_✨🌹_In the Name of Allah the most Beneficient the most mercifull praise be to Allah lord of the worlds._
*_Wannam labari ya faru da gaske sai dai garuruwa da zan chanja ban yarda a chanja min labari ta ko wacce sigaba ba._*
https://chat.whatsapp.com/ChTy4SwTGp60yRFohRmxoD*_Page 1&2_*
_SOKOTO_
"Arkillah Lowcos Wani anguwa ne dake Neja Delta a cikin garin Sokoto da misalin karfe 2:35pm na ranar Asabar wata matashiyar yarinya cikin shiga ta Uniform din islamiya ta shiga wani dan madai-dai cin gida da gudun ta da alama wani abun take guduwa.da Sallama ta shiga gidan Assalamu Alaikum".Wa,alaikis salam" *Sultanah* ya naga harkin dawo nasan dai ko isa Makarantar bakiyi ba. Wanda aka kira da. *Sultanah* tasa wani kuka, tana durƙushewa a parlour. Matar cikin tashin hankali ta isa gareta, tana cewa "*Sultanah* lafiya kuwa kike wannan kukan? Mai ya faru? Mai aka miki?. Nam ita ma ta fara kuka dan tasan tatsoniyar gizo baya wuce na ƙoki, sai da suka ci kuka sosai sannam Matar tace, "Haba *Sultanah* mai yasa baza ki yarda da ƙaddarar da ta zo miki bane?, *Sultanah* na fiki jin zafin wannam lamari da banyi imani da ƙaddara ba, da yanzu bana duniyar nam, Amma dana danne zuciyata ta kuma yi hakuri gashi nam ina rayuwata kamar kowa, Dan Haka kema ki ɗauki Hakuri kamar yadda na dauka Insha Allah komai zai zama tarihi..
*Sultanah* tace "Wallahi Umma na yarda da ƙaddarata amma abun yayi yawa , har takai a gaban idanuna ana cin zarafina, Umma bayan fitata daga gidan nam, ina cikin tafiya naga wata mota tasha gabana dole tasa na tsaya saboda ya tare hanyan wani matashin Saurayi ne ya fito tare da min Sallama na amsa masa tare da ce masa lafiya,cikin fara,a yace "lafiya klao sai Alheri, ya gyara tsayiwa tare da bani hakurin tsai dani da yayi akan layi, na ce masa ba komai amma yayi sauri ya fadi abun da zai fada. Yace dama ba komai bane ya kawo ni gunki Illa soyayyarki sai da gabana ya faɗi da na ji yace haka. Ya kara da cewa Wallahi ba tun yau nake ganin ki ba yau ne dai Allah ya nufa da zan miki magana, ina matukar kaunarki In har kin amince a yau zan tura gidan ku domin ayi maganar Aure...
"Kafin na bashi amsa wasu samari da tun tsayiwar mu suke kallon mu suka iso wajen tare da cewa mutumin Wallahi malam wannam ba mutumiyar kirki bace hasali ma bata da Asali.... " kafin su karasa ne na yiwo gida ban san mai suka ƙara gaya masa ba, Umma wai mai yake faruwa dani ne? Shikenam ni haka zan rayu ba Aure?. wani kuka Mai ban tausayi ne ya kwace mata kuka take sosai Umma tayi matukar tau saya ma diyar'tata nam ta shiga lallashinta.
da kyar Umma ta samu kanta tayi shiru nam ta mike tayi dakinta ta fada toilet ta sakar wa kanta ruwa da tuna ni barka tai a zuciyatar, anya kuwa Abunda Umma ta gaya min gaskiya ne kuwa?. Gaskiya akwai abu akasa wannam cin mutuncin da ake mata ba banza ba dan kawai an tsinto ni shikenam ata shegan tani da rashin Asali kawai wannam lamari akwai daure war kar amma insha Allah sai na san gaskiyar abun, haka tayi ta tunani a zuciyarta, har wani bacci mai nauyi ya dauketa. Umma kuwa tun shigar Sultanah ɗaki take zubar da hawaye tare da tsinewa *Majid* ta ƙara da cewa insha Allahu *Majid* baza ka taba rayuwar jin dadi ba Allah ya isa tsaka nina da kai Allah sai ya saka mana na tsaneka, haka tayi ta sambatu tana kuka sosai.( Niko nace tofa mai ke faruwa ne a wannam gidan).
Tunda *Sultanah* ta baro wajen samarin nam suke ta gaya masa ƙarya da gaskiya akanta har sai da suka tabbatar da ya yarda da maganarsu sannam suka barshi ya tafi da tunani bar ka tai a zuciyarsa yana cewa "anya gaskiya ne kuwa?. wata zuciyarsa tace gaskiya ne mana in da ba gaskiya bane ai baza ta gudu ba a haka yana zancen zuci har ya ƙarasa katafaran gidan su, yayi horn mai gadi ya wangale masa get yana shiga cikin parlour su ya ji hayani sai tashi yake yi . A zuciyar sa yace wannam wani irin faɗa ne haka sun girma amma suna mai da kansu ƙana nun yara wannam a gaban yaransu suna fada mtsss ya daka tsaki tare da Sallam, babu wanda ya amsa masa hasali ma babu wanda yake jinsa. Wasu mata biyu ne ɗaya zata kai 35year daya kuma 45year mai 45year ce tace ke kika sani tunda ba,a gaya miki gaskiya haka kawai kina barin yarinya ƙarama tana zuwa shagon da maza suke taruwa tana zama daga ita sai vest wannam ai ba yi bane ba dama a miki magana sai ki hau mutane da ban bamin banza, "eh ina ruwanki da rayuwar ɗiyata kiji da naki mana ni bana son sa ido da gulma dan kawai Sado mai shago baya bawa Salma sweet shikenam kuma baƙin cikin ki ya motsa.
Yana jin akan abun da suke faɗan yasa shi juyawa da sauri ya fita yana fita kuwa ya hango Nusaiba kan cinyar wani dake zaune a bakin shagon Sadi da sauri ya finciko ta tare da gallawa yan shagon harara ya shige gida da ita yana zuwa ya kaita gabansu har yanzu suna kan cha-char bakin su bai ce musu kala ba ya juya ya fita ya nufi part din shi dan shi ya tsani hayaniya a rayuwar sa yana shiga ya nufi toilet yayi wanka ya fito tare da shafe jikinsa da daddan mai ya dauko t-shirt da wandon jean's marassa nauyi ya sanya ya feshe jikinsa da turare sannam ya shafe gashin kansa da mayuka nan da nam ya fara sheki da daukar idanu ya dauki makullin motar ya fice abunsa daga gidan. Yana fita wata motar ta shigo gidan wani dantijo ne ya fito a motar ya nufi cikin parlour yana sallama kowa dake parlour ya watse babu wanda ya tsaya balle ya amsa masa.
*Sultanah* haka ta wuni tana bacci Umma bata tashe ta ba dan ta mata uzuri dama yau ba salla take ba bare ta tasheta itama Umma inin ranar kawai tayi sane a gidan amma ba wani dadi yake mata ba damuwar duniya yayi mata yawa ta rasa mai ke mata dadi in har ta tuna *majid* ta ringa tsine masa kenam da sawa diyarta *Sultanah* Albarka. Wani matasin saurayi ne dan kimanin 46year ya shigo gidan da Sallamar sa sai da gaban Umma ya fadi dajin muryar sa ya shigo ya zauna kusan ta tare da cewa "ina wuni Umma nah. Cikin takai ci Umma take kallon sa tare da cewa "Uban wa yace ka shigo min gida *Majid* ban ce kar ka sake zuwa inda nake ba wallahi in baka tashi ka bani wuri ba sai na ci Uban ka Tsinan ne kawai". *Majid* ya tashi ko a jikin sa ya ajiye mata damin ƙudi tare da ficewa ta dauki kudin ta jefeshi da shi tare da fashewa da wani irin kuka mai ban tausayi. *Majid* yana fita ya nufi part din sa dan yace bazai taɓa barin gidan ba yana shiga wayansa ya fara ruri da sauri ya dauka banji mai aka fada daga dayan bangaran ba sai naji *Majid* yace 'Wallahi ranka shi dade na rasa ta wani hanya zan bi in shawo kan Ummanah ta yarda mu ƙara guda ɗayan nam. Chan yace kai *Sultanah* gaskiya bazan iya yi akan ta ba gwanda dai Umman tunda Munyin ɗaya............_TOFA WAI MAI KE FARUWA NE A WANNAM GIDAJE BIYU KU DAI KU CIGABA DA BINA DAN KUJI WACCE WAINAR AKE TOYAWA_
_SAI NAGA YADDA KUKA KARBI BOOK DIN ZAN CI GABA_
Vote
Comment
Share
One love08132761212