*ABIN DA AKA GASA...!*
_Shi yaga wuta..._🔥
*_TRUE LIFE STORY_*By
_Hafsat A Garkuwa_✨🌹WWA
*Sadaukarwa*
'''My Rafi'a wannan page gaba ɗaya na ki ne sai yadda kika so za kiyi ina miki son so'''✨🌹💋*_page 3&4_*
*…Dattijon ya haura sama yana ƙwafa yana jin takaicin rashin haɗin kan matan nasa amma zanyi maganinsu ya haura ɗakin sa abunsa kowa tayi lamu a ɗaki baka jin ko motsi chan dai Hajiya babba ta fito domin ita ce da girki ta nufi ɗakin san zuciyarta na matukar bugawa da sallama ta shiga ta same sa yana saka kaya Alamar daga wanka ya fito, "Daddyn su sannu da….da.wo…wa tana maganar bakinta na rawa alamar tsoro, Daddyn su wani wawan Mari ya sakar mata tare da bal da ita wani ƙara ta sake wata tsohuwa dake ɗakinta da taji kukan Hajiya Babba wani dariyar mugunta ta sheƙe da shi Yasmin tace "sannu muguwa ana dukan mahaifiyar mu amma ke dariya abun ya baki.
"Eh ba dole nayi dariya ba tunda iyayenku basu jin magana basu san kuma na hanasu su hanu ba ai gwara ya koya musu hankali saura ɗayar mai kama da kazar bitinare wallahi ni nafi so ya kamata ya mata shegen duka.Yasir yace "Wallahi kin cika mugunta tsohuwar nam, Haka Daddynsu sai da yayi wa Hajiya babba dukan tsiya sannam ya ce "ina ku baku da hankali kuna zaune kamar karnuka to wallahi gobe ma kuka sake haka zanyi itama zan kamata tashi ki fecemin daga ɗaki wawaye kawai da basu san sun girma ba" Hajiya Babba ta mike duk jikinta yayi tsami ta sauƙo ta nufi ɗakinta tazo wucewa wannma tsohuwar tace "Allah shi ƙara ƴan maƙwallaton wani waje ta kuma kwashewa da dariya.
Daddynsu ya fito ya nufi dining ba kowa a parlour sai da ya zauna sanna ya kira Hajiya Babba tana zuwa yace "ni zan saka ma kai na yana maganar yana mata wani mugun kallo cikin sauri ta haɗa masa komai sannam ta juya zata tafi yace "ki kira min kowa na gidan nam. Ba dan ta so ba ta fara zuwa ɗakin Hajiya Karama tace "wai kizo inji Daddynsu sannam ta nufi dakin Kaka da Sallamarta tace Hajiya wai Daddynsu na miki magana kizo aci abinci kuma ku taso kuzo Hajiya Kaka ta kwashe da dariya tace sannu "Zainab kinsha duka Allah ya shiƙara Allah ya ƙara na gobe ta kuma kwashewa da dariya Hajiya Babba dai ta juya dan abun ya fara ƙularta Hajiya kaka ta mike tana dariya sosai suka nifo dining din Daddynsu ya gaida Hajiya Kaka da gidan sannam yaran suka masa sannu da dawowa *Nusaiba* ne tazo tace "Dady kaciyo min ceweet ta fada cikin gwaran cinta ya daga ta tare da cewa "na suyo miki mai sunan Manya *Salma* ke baki son sweet din ne?. Ena so adi. Ina so Daddy take son faɗa a gwaran cinta kasan cewar *Nusaiba* ta fita ta kuma fita wayo nam dai suka fara cin abincin su babu wanda yace ƙala sai Hajiya Kaka data ke ta shan dariya sannam tace" *Hamza* ya kamata kayi wa matan ka faɗa saboda basu ɗauke ni a komai ba ga shegen faɗa kamar karnuka to wallahi wannam ba tsari ba ne" Daddyn su yace "kiyi hakuri Hajiya insha Allah hakan bazai sake faruwa ba sannam ya kalle su cikin tsawa yace baza ku bata hakuri bane?. Bakin su a haɗe cikin rawar murya suka ce kiyi hakuri cikin yanga Hajiya Kaka tace to.Daddy ne ya mike ya haura sama tare da kiran Hajiya Karama. Cikin rawar jiki da tsoro dan yau tasan kashinta ya bushe ta bi bayan sa Hajiya kaka tace "shegiya yau zata daku wallahi Allah yasa ya balla miki ƙafa daya ta kwashe da dariya. *Nusaiba* tace ba amunba Kaka ke mulguwaje. Hajiya Kaka tace "kinci gidan ku nine Muguwar?. *Nusaiba* tace "Em ba kina so A daki mamana ba kuma sai na gayawa Yaya Mu,anjal. Duka parlour suka kwashe da dariya saboda yadda ta fadi sunan da kuma yadda bakinta yayi *Mubajjal* take nufi.
★★★★
"Gwanda dai Umman tunda munyi Sau ɗaya Amma *Sultanah* kam Wallahi bazan iya ba daga haka suka yi sallama ya shige ɗakin sa ya kwanta yana tunanin mafita, *Sultanah* sai mangari ba ta tashi tana tashi ta shige toilet ta yi wanka tasa wani materials mai kyau bata yi wani kwalliya ba amma tayi kyau sosai ta fito parlour ta samu Umma tana kallon Sunna Tv tace "Umma sannu da gida yau kin barni sai bacci nake ban taya ki aiki ba. Umma tace "ai na barki ne ki huta *Sultanah* kinga ai kin samu bacci sosai.
"Haka ne kam"
"To kije kitchen ki ɗauko abincin ki. "Ai kuwa Umma dama yunwar ce ta tasheni da ban san ranar da zan tashi ba" ta faɗa tana shigewa kitchen ɗin Umma tayi Murmushi taci gaba da kallonta. *Sultanah* ta fito da Tuwo miyar egusi ta zauna tana ci tana yaba Umman nata. Wata budurwane tayi Sallama Umma ta amsa mata tare da cewa. "*Walida* yau kece da magriban nam kinzo duba mutumiyar taki da bata je makaranta ba ko? Walida tace "ai kuwa Umma kamar kin sani Ina wuni. Lafiya klao ya mutan gidan naku. Suna Lafiya lau . Ta karasa kusa da *Sultanah* tace "Yau kuma yan shariyar sun zo kenam *Sultanah* tace "Wallahi kin fiye surutu Walida kamar wata aku duka suka sa dariya sannam walida tace mai ya hana ki zuwa Makaranta yau nasan dai babban Abu ne da Sauri *Sultanah* ta kalli Umma sannam ta dawo da Kallonta ga Walida tace "har na shirya kuma zazzabi ya rufe ni shine kawai na kwanta kinga aai yanzu na tashi. "Ayya Allah yaƙara sauki dama na san dai ba banza ba *Sultanah* tace muci abincin mana Walida tace Wallahi yanzu na tashi daga kanshi bari kika nazo na wuce dama nazo jin mai ya hanaki zuwa ne. Suka mike tayiwa Umma Sallama sannam suka fita ta raka ta har bakin get sannam suka yi Sallama ta dawo cikin gida taci gaba da cin Abincin ta.
Tun fitar *Mubajjal* bai tsaya ko ina ba sai gidan su Amininsa Mudansir ya shiga gidan da sallamar sa wata mata dake zaune ta amsa masa tare da cewa "*Mubajjal* yaushe a gari haka dirar yaushe yace "wallahi Mummy yau din nam ko awa biyar banyi da sauka ba ina wuni. Lafiya klao ya karatu? Alhamdulillah yanzu kam mun kammala sai dai aiki kuma. To Allah ya taimaka Allah yasa an kammala a sa,a muje dining na zuba maka abinci. A,a Mummy sai naje na ga Mudan'sir. "Oh ai kuwa yana part din sa dan bai jima da dawo wa ba. To bari naje na same shi ya mike ya nufi part din Abokin nasa ya shiga da Sallamarsa Amma bai ji an amsa ba ya shiga yaji Alamar motsin ruwa a fili yace yana wanka kenam sannam ya kwanta a kan gado ya ciro wayarsa yana fara dannam wa yaji cikinsa ya wani kulle nam ya kama lebensa na kasa yana cija yana rike da cikin a haka Abokin nasa ya fito ya same shi yace "kai Baba shine kamin bazata yanzu ma shirin zuwa……. bai kara sa ba yaga halin da Abokin nasa yake ciki yasan mike damun sa yace "kai wallahi Allah ka cika jarabara Wannan su Daddy suyi su Aurarka kar ka zama bunsuru. *Mubajjal* yana cije baki yace "ni ka m kaje kace Mummy ta hada min tea da lemon tsami pls ka kawo min. Mudan'sir ya fita ya sanar wa Mummy tana Mamakin wannam ciwon nasa ta hada masa ta bashi ya kawo masa yana sha kuma sai zufa da yake zubawa sai kuma chan yaji marar ta sake sannam ya gyara zaman sa. "Kai Abokina Wallahi jarabarka tayi yawa. *Mubajjal* yace "*Mudan'sir* ya kake so nayi wallahi nima inso nayi aure amma ko na tunkari Daddy da maganar fada zai min sosai yace yaushe nakai aure. *Mudan'sir* yaji Abokin nasa ya bashi tausayi sosai sannam yace kayi hakuri *Mubajjal* insha Allah wataran zai Amince ka cigaba da hakuri to wai baza ka fadawa Hajiya Kaka ba. "Tab kamarasa wanda zan gayawa sai Hajiya Kaka wannam fa muguwace in na fada mata ma kara zuga dady zata yi ta dinga tallena kuma kenam kamar makilin suka sa dariya baki daya sunan suka ci gaba da hirirsu ta yaushe gamo.
Hajiya ƙarama tana shiga Daddy ya fara jibgarya kamar Allah ya aiko sa sai da yayi mata lilis sannam ya korota waje. Ta sauko a hankali Hajiya Kaka data ganta tana tafiya da kyar sai da ta dunguro daga kujera tsabar dariyar mugunta yaran parlour ma suka taya ta saboda tafiyar Hajiya Karamar har gwara na jinjiri mai koyan tafiya tazo ta gefensu ta shige Hajiya Kaka tace "kaga shegiya kamar ba ita ta gama cacar baki da yayarta ba ta taho zukai- zukai kamar wata doki. Ta kuma kwashewa da dariya suna taya ta a lokacin kuwa *Nusaiba* ta sulale tayi waje abunta tana shagon Sado tana ta wasa shiko yana kallonta yana lashe baki kamar tsohon maye.
Tana zaune a shagon Sado har magriba babu wanda ya damu da inda take a gidan su kowa na harkan gaban sa tana kan cinyar Sado sai shafa mata baya yake yana wani nishi kamar ya samu cikakkiyar budurwa itako sai shan Sweet dinta take abun ta. Suna haka sai ga *Mubajjal* kamar ya sani yayi parking ya taho wajen shagon Sado a lokacin Sado da ya hango motar sa ya ce jeki gida *Nusaiba* sai gobe ki dawo. Tace to chado ta juya ta tafi da gudu a hanya suka ci karo ya rike kunnenta tare da cewa "ke dan Ubanki mai kike anam da magriba. "Yaya Mu'ajjal ayi akuyi najo arban ceweet ne agon chado. "Dan Ubanki in na kara ganin ki kin fito wani karbar minti sai na karya mika kafa shige mu tafi ya hankada ta gida sannam ya shiga mota yayi horn mai gadi ya bude masa ya shigo ta shiga gida tana kuka Kaka ce a parlour da Yasmin da Yasir tana basu labari sai dariya suke dan Hajiya Kaka ta iya bada labari. *Nusaiba* ta shigo tana kuka Hajiya Kaka tace "mugun ya dawo kenam yanzu kuma za,a fara jin kukan ki kai wannan da baka da mutunci daga dawo warka daga tafiya zaka fara dukan yar mutane lokacin *Mubajjal* ya shigo parlour ko kallon in da take bai yiba yace "*Yasmin* kawo min Abinci na ta mike da sauri ta nufi kitchen ta kawo masa ya zauna kusa da Hajiya Kaka yace "wai mai kike fada ne tsohuwar nam. Hajiya Kaka ta sake baki tare da cewa "Oh oh ni naga ɗan banza ai zakaci kwal Ubanka Kai ma sai nasa Ubanka ya naɗa maka duka Kamar yanda ya nadawa iyayenka yanzu. Ji yayi zuciyarsa ya wani har bawa yace "Kaka wa aka daka kamar karamin yaro ta kwashe da dari tare da gaya masa duk abun da ya faru ta kara she da cewa "kaga yadda suke tafiya kuwa musamman ma wacchar shegiyar ita aka daka ta karshe data fito kamar kwai ya fashe mata ta kuma kwashewa da dariya. Da Sauri *Mubajjal* ya ajiye Abinci ya nufi……*_TO FAN'S YANZU ZA,A FARA WASAN_*😂
#Vote
#Comment
#ShareONE LOVE💕🤞🏻
08132761212