*ABIN DA AKA GASA...!*
_Shi yaga wuta..._🔥
*_TRUE LIFE STORY_*By
_Hafsat A Garkuwa_✨🌹*Women Writer's Asso...*
*_Page 31&32_*
*★★★★★★*
*Jawaheer* wani wawan birki ta taka jikake kir! kir! cikin firgici suka juyo suka kalli motar *Malika* ta isa wajen tana cewa "Jawaheer lafiyan ki kalai kuwa? Cikin ƙarfin hali *Jawaheer* tace "lafiya klao kai na ne kawai yake saramin, *Malika* yau ke na gani da saurayi ke da bakya kula samari yau kuma na ganki da wani"
*Malika* tace "wallahi da ɗin ma ban samu wanda nake so bane sai yanzu shi yasa dan har an saka mana rana, wani zare ido *Jawaheer* tayi tare da cewa "an sa muku rana fa kika ce?"
"Eh nam da wata Biyar za ayi Auren mu"
Da sauri *Jawaheer* ta figi motarta ta bar wajen gudu take sosai har ta isa gidan ta, Horn ta buga wanda mai gadin yasan yau fa ba lafiya yayi hanzarin bude mata ta shiga saura kadan ta bige sa yayi saurin kaucewa. Tana parking ta fito da gudu tayi cikin gida tana wani irin kuka ta zube a tsakar falo, kuka take sosai tana cewa "Haba *Sultanah* mai yasa zaki cuci kanki? mai yasa zaki tsaya wata ta kwace miki Farin cikin ki? Gaskiya gwara ki tashi tsaye domin ki kwato abun alfaharinki a hannun wata kar kiyi sake. Ta sake wani kuka tana ta sambatu. Da sauri ta ɗauki wayanta ta danna number Uncle Doctor. Yana ɗagawa ta sake fashe masa da kuka cikin rikitar zuciya yace "mai ya faru kike wannam kuka?. Cikin kuka tace "*Mujahit* ! shikenam zan ƙara rabuwa da shi har an saka masa rana da wata. Cikin kidimewa yace "baza ki rasa saba *Sultanah* in sha Allah *Mujahit* naki ne ke kaɗai Ina nam zuwa kiyi hakuri ki bar kuka. Daga haka sukayi Sallama taci gaba da kukanta.*★★★★★★*
A yau Jumma'a ne duban jama'a suka halacci ɗaurin Auren *Mubajjal Hamza* da Amaryarsa *Nusaiba Kabir* an daura aure akan Sadaki Dubu Dari da Hamsi. An daura Lafiya *Mubajjal* kuwa murmushin yaƙe kawai yake yi *Mudan'sir* sai masa dariya yake shi kuwa ya cika ya batse kamar bai taɓa dariya ba kafin wasu mutanen su gaisa dashi ya sa ki jiki ya bar wajen yayi bakin gidansu ya faka Motar yayi kwanciyarsa a ciki yana jin wani bakin ciki wai yau shi aka daurawa Aure da wannam yarinyar. "Wai yau ni zan aure sauran mai shago gaskiya anyi matukar cutata sosai. Yana cikin wannam tunanin yaji ana masa knorking kamar bazai bude ba ganin *Mudan'sir* ne yasa shi budewa. Yana shiga yace "Haba Abokina ya ana gaisawa da kai kawai aka ne meka aka rasa?
"Malam dan Allah karka dame ni ka barni naji da abun da yake damuna"
"To Allah ya baka hakuri Ango cewar Mudan'sir yana yar dariyar farinciki yace "yanzu zuwa anjima zamu shirya wajen Dinner ko? Wani kallon Raini Mubajjal ya masa tare da cewa "wai so nawa zan fada maka ni babu wani abu da zanyi a bikin nam to bari kaji na sake fada maka Wallahi babu abun da zanyi na biki. Ya daka tsaki tare da mikewa ya tada Motar suka shiga cikin gidan. Yana fitowa aka fara rantaba guda ana masa tsiya shiko fuskar nam kamar bai taba dariya ba haka ya shige fuuu....! Kamar iska *Mudan'sir* ne yake amsa musu tare da ta yasu yi mar tsiyar.Suna shiga ya zube akan gadon sa Mudan ganin ba wanka zai shiga ba ne yasa cikin sanyin murya yace "pls ka tashi ka shiga wanka ka shirya domin muje wajen Waliman nam kasan duk sun wuce mu ake jira. Babu yadda ya iya haka ya mike ya shirya cikin wani dakakkiyar shadda Sky Blue shima Mudan shiryawa yayi sai daukan Kamshi suke suka fito suka tafi. A bangaren Amarya kuwa tunda aka ɗaura Auren jikinta ya mutu sosai duk taji wani kasala ya shigeta duk sonta da Auren sai taji sam bata so. Amma fa Amarya tasha kyau sosai sai ƙyalli da ƙamshi take zubawa. Su Yasmeen ne a gefenta sunata mata tsiya wai yau dai sai gidan Ya Mubajjal zata kwana bata so haka ba amma Daddy yace zuwa yamma za'a kaita gidan ta dake Arkillah Lowcos, haka dai tayi zugum tana jin tsiyar da suke mata da wasu kawayenta biyu Rahina da kuma Sakinah. Ko abinci ta kasa ci a ranar tana tunanin zaman da zasu fara da jan gwarzonta. Da misalin ƙarfe 6:00pm na yamma na wannam ranar wasu Motoci ne na fada a ji suka shigo gidan su Mubajjal domin ɗaukar Amarya aiko nam aka fara shiga aka fito da Amarya tana kuka sosai da kyar aka cireta daga jikin Hajiya babba da kuma Hajiya Karama suma sai da sukayi kuka. Hajiya Kaka ko dariyar ta take sha tare da cewa" dole kije gidan mijinki! nasan zaki sha walaha a wajen sa, duk da saura zai dauka. Mutanen wajen sun jita ras amma babu wanda ya tamka mata dan sun san halinta ras. Ana ta shiga mota naga wata ƙatuwar mota aiko na kutsa dan naga suwaye a cikin ta cikin Mamaki naga yan' grp din *Taskar Hafsat A Garkuwa Group* ne nace wadannam kuma ina suka san da wannam auren Basu samu damar gaisawa da kowa ba suka bi yan kai amarya dan kar a musu nisa basu san kuma gidan ba Gidan mutane kadan ne basu jeba dan suma iyaye ne shiyasa basu je ba amma Hajiya Karama taje kai diyarta haka suka dauki hanya basu wani jima ba saboda ba su da wani nisa sosai tsakanin su. Nam naga sun faka a wani katafaren gida. Aka shiga da Amarya ta wagar *Abinda Aka gasa..! grp* ma suka shiga su *Umm-Muhammad* sai ware ido ake yi anga gida kamar gidan Aljannah nam suka shiga falon gidan Babban falo ne da ya dau kayan more rayuwa suka haura samma inda dakin Nusaiba yake kusa dana Gogan ta suna ajiye ta manyan ciki suka kara mata nasiha a tsatstsaye domin yanzu za'a mai dasu suka watse Su *Yasmeen* aka bari da kuma *Sakinah* da *Rahinah*. Domin su jira zuwan angwaye sai akai su dan kar a barta ita daya. Suna cikin hira suka ji Sallamar su Sis Nafisa yan' grp din Abinda Aka gasa...! Da Sauri Nusaiba ta mike domin ta gane su tace *Mom Haidar&Khairat* ! *Sis Nafisa* , *Ummu-Muhammad,* *Suleja,* *Maryam a tafida,* *Nana Khadii,* *mmn ibtisan,* *Ummu Eeman,* *Brr Husnah,* *Ummu suhaima,* *Mummy Jiddah,* *Halima,* *Zainab,* *Aisha Abubakar* *Mrs Nurah*, *Rafi'a*, *Queen Fatee*, *Sophie's*. Lalle kun min karamci sosai wallahi nagode Allah ya bar zumunci *Mummy Jiddah* tace "ba komai Kawa ai mun zama daya(Niko nace O ko yaushe ta santa har ta zama kawarta Ohoo Lol.). *Yasmeen* tace "*Nusaiba* ina kika samu wadannam kuma? Ta bada cikin sigar tambaya.
*Ummu-Muhammad* ne ta galla mata wani harara har da murguda baki(Kai Ummu tambaya fa kawai tayi nima ai dole in tambaye ku yaushe kuka santa har kuka je bikinta). Nusaiba tace "ke dai ki bari kawai wadan nam yan Amana ne a Grp ɗin *Abinda aka gasa...! Na Sister Hafsat A Garkuwa* muka hadu wallahi suna da mutunci sosai. Yasmeen tace "aiko dai kam gaskiya muna godiya da wannam zumunci Nam kowa ya dauko abun da ya kawo mata ya mika mata daga mai kudi sai mai kayan mata da dai sauran su. Su *Nana Khadii* iyayen mako ne bata bada komai ba ita da mrs Nurah, haka suka mike saboda driver yana jiran su a yau zasu koma. *Nusaiba* har da dan kwallanta ta raka su har bakin kofa suna musu godiya suka rabu. Nam suka dauki hanya su sis Nafisa basu so subar gidan ba saboda gidan ya hadu sosai. Nam suka dauki hanyar komawa. Su Nusaiba ko suka kuma suka zauna suna dan taba hira ganin fa Angwaye basu da niyar zuwa ne yasa Yasmeen tace "bari dai na kira Ya Mubajjal dare sai yi take yi. Sakina tace "gaskiya kam ta dauki wayarta ta kira sa sai da ta kusa katsewa ya daga tayi sallama ya amsa mata tare da cewa "Yaya muna ta jiran zuwan ku amma har yanzu shiro... kafin ta kara yace "dama ai ban ce kowa ta jirani ba dan haka ku kama hanya ku tafi ba yanzu zan shigo ba daga haka ya kashe wayar. Yasmeen ce tace "to kunji dai abun da yace dama Hand-free ta saka nam suka mike suka mata Sallam tana kuka suna kuka suka rabu Yasmeen ta jasu a motar ta suka yi gida.*★★★★★★*
*Malika* ta sake baki tare da karasawa wajen *Mujahit* yace "wanchar kuma waye take so ta bige minke dariyar yake tayi tare da sanar masa yadda sukayi. Sai da gaban sa ya fadi a yanzu ya sake tabbatarwa wannam *Sultanah* nan sa ce. To mai yasa *Sultanah* zata masa haka kenam? mai yasa bata mutu ba za'ace ta Mutu? Mai kuma tazo yi nam garin? *Malika* ne ta katse mata tunaninsa ta hanyar cewa "muje mana dan anaci yana ta masifa nam suka shiga motar *Nura* yaja su yana mita suka nufi Halwa I Cream. Wajene babba nam suka ta jidar Icream sannam suka zauna *Malika* da *Ikram* da kuma *Nura* ne kawai suke sha amma *Mujahit* ko kallon abun bai yi ba tunani kawai yake yi. *Nura* ne ya lura da haka yace "Abokina wai meke faruwa ne haka? *Mujahit* yace "ba komai kuyi kusha mu tafi akwai abunda zanyi yanzu jin haka *Nura* yace kawai mu dauka mu tafi dashi *Malika* bata so haka ba amma suka tattara suka shiga motar suka tafi suka ajiye su a kofar gidan suka yi sallama suka juya su kuma suka shiga gida. Suna juyawa *Mujahit* ya sanar masa duk abun da *Malika* ta sanar masa ya kara da cewa"*Nura* babu makawa *Jawaheer* itace *Sultanah* ta. *Nura* yace "Lalle nima yanzu na yarda da haka amma kana ga wacce hanya zamu samu dan mu gane itan ce. "Da akwai hanya *Nura* kaga yau da ta gammu ta shiga damuwa sosai in har ta ci gaba da ganinmu da kanta zata zo ta fallasa kanta, dole naci gaba da zuwa hira wajen *Malika* kuma dai-dai lokacin da *Sultanah* zata dawo daga aiki mu fito waje dan ta gan mu dan *Sultanah* tana da matukar kishi. "Gaskiya haka za'ayi to in kuma ka gane itan ce ya zaka yi da *Malika*"
"*Nura* ya zanyi da ita kowa dole sai na aureta dan bazan yaudareta ba amma inhar *Sultanah* ce wallahi Zata kwacewa *Malika* fadar ta a waje na dan dama ba wani sonta nake ba wallahi kawai dai na rasa wacce nake so ne..._Kuyi Manage da wannam Ina matukar Alfahari daku fan's dina wanda na sani da wanda ban sani ba Ina kaunar ku a ko da yaushe.💕
#Vote
#Comment
#ShareONE LOVE💕🤞🏻
08132761212