*ABIN DA AKA GASA...!*
_Shi yaga wuta..._🔥
*_TRUE LIFE STORY_*By
_Hafsat A Garkuwa_✨🌹*Women Writer's Asso...*
Page 13&14
...Bayan sun gama yiwa *Umma* nasiha mai ratsa jiki suka ƙara da cewa "Allah ya yiwa *Sultanah* rasuwa sakamakon jinin da ta bayar wa Mahaifiyar Mujahit nam suka Sanar mata da koma, tunda suka fara magana, *Umma* take ambaton Allah "innalillahi wa'inna ilaihi'raji'un....take faɗa idanunta suna zubar da ƙwalla ta zuba musu ido ta zama kamar mutum mutumi Hawaye masu zafi take fitarwa. Basu iya ce mata komai ba suka miƙe suna cewa "zamu ɗauko gawarce ki ganta kafin mu shige da ita? da sauri tace "A'a kawai ku kaita gidan ta na gaskiya. Ba musu suka ce "to babu wanda zaki ƙira a danginku domin a kaita dasu?. Cikin Kuka tace "ku kaita kawai bamu da kowa. Cikin tausayin *Umma* suka fita sukayi asibity aka sallaceta aka kaita gidan ta na gaskiya, sai dai muce Allah ya jiƙanki *Sultanah* . Ko da *Majid* yaji mutuwar ƙanwarsa kuma Ƴarsa yayi kuka sosai kamar ransa zai fita daga jikinsa, Amma kukansa bana komai bane sai na rashin nasara da yayi na aikin da aka sa shi akan *Sultanah* (Niko nace anya wanna kansa ɗaya kuwa Allah ya kyauta), Haka dai ya kafa runfuna a gidansu suna karɓar gaisuwa, *Umma* Sumanta biyar Kuka kam ta shashi kamar ba gobe tana kuma sakawa *Sultanah* Albarka makotanta suna amsa mata da ameen, *Walida* ma tazo tayi kuka sosai na rashin Aminiyarta jama'a da dama sun tausaya mata sosai.(Nasan zaku tambayeni *Umma* basu da dangi ne to ku ci gaba da bini zaku samu amsarku dan yanzu za a fara wasan).
Haka aka ci gaba da zama har na tsawon kwana bakwai zuciyoyi sun danga haka rayuwa tayi ta tafiya har na tsawon kwana arba'in tsawon kwana bakwai ɗinnam da *Mujahit* ake zaman makoki bakinsa ya buɗu sai dai maganar sa tayi sanyi bakasa fai yake magana ba haka *Mubajjal* tare dashi ake zaman makokin shima yajin mutuwar *Sultanah* sosai ya kuma bita da Addu'a.Bayan arba'in ɗin *Sultanah* ne *Umma* ta haɗa kayanta ta tafi Gombe ko *Majid* bata sanarwa ba dan a duniya babu wanda ta tsana kamar sa dama saboda *Sultanah* ta zauna a gidan to yanzu kuma bata dole ta bar masa gidan sa tun 9:00am na safe ta bar Sokoto sai karfe 2:00pm na yamma ta isa Gombe daga nam tahau napep zuwa anguwar Pantami layin sarkin fata ta sauƙa wani gida madai-dai ci ta shiga da Sallamarta wata mata yar dattijuwa ce ta dawo tana kallonta da mamaki take cewa "yau kuma mai ya kawo ki gidan nam ko kin manta abunda ke kanki? Kin manta bakya ɗaya daga cikin ahalin gidan nam? To maza tunkafin mahaifinki ya fito ki juya kinsan inda kika nufa. Ta karasa maganar tana mata banzan kallo. *Umma* ta durkusa a wajen tana wani kuka mai ban tausayi take cewa "Mama dan girman Allah kumin rai ku yafemin nima ba laifina bane ƙaddarata ce tazo a haka. Dan Allah ku gafarta min bani da waɗanna suka fiku a gidan duniyar..... kafin ta samu zarafin ƙarasawa wani dattijo ya fito yana cewa "ke dan Ubanki zaki tashi ki bar gidan nam ne ko sai na tara miki jama'a yar'iskar yarinya kawai. *Umma* Kanta ne yayi wani irin sarawa nam idanunta ya fara kakkafewa ta fara rawar dari jikinta na ɓari sosai idanunta sai kafewa suke nam ta zube wajen ba numfashi da sauri matar tayi kanta tana Salati tana "Fadima karki mutu! Fadima muna sonki take ta fadi shima da hanzari ya fita ya tari napep yazo suka saka ta a ciki suka nufi asibity da ita ko sanarwa matan gidan basu yi ba.
★★★★
*Hajiya Kaka* wani kuka ta zuba harda sakin fitsari da sauri su *Hajiya Babba* da *Hajiya Karama* suka kamata domin su ɗaga ta ta sake musu kuka tana "wayyo ƙafata ƙafata ku ajiye ni, *Hamza* kazo ka taimaka min *Yasmeen* ta karya ni W'wannam hegiyar yarinya Allah ya saka min abun da kika min tana kuka tana zabgawa *Yasmeen* zagi da hanzari *Daddy* ya shigo yana tambayar lafiya?. Ganin Kaka a zaune dirshan tana kuka ne yasa ya ƙarasa wajen ta yana tambayarta "Hajiya Lafiya mai ya sameki haka?. Cikin Kuka tace "waccer shedaniyar ce take zagina na biyota zan daketa kuma na faɗi daga jima kamar na karye ta ƙarasa maganar tana kuka da majina. *Daddy* yace "Ashsha ya fada yana ciro wayar sa ya dannam wa Doctor su waya aiko dama yana kusa dasu zai yiwa *Mubajjal* Allurarsa na rana da Sallama ya shigo Daddy ke masa bayanin abunda ke faruwa nam ya kama ƙafar Kaka mai ciwon nam ta saki Kuka tana rike masa Hannu amma ahaka sai da ya duba kafar yaga kuwa karyewan tayi. Nam yace bari yaje ya dauko kayan aiki ya dawo suka amsa masa da to. Su Hajiya Babba da Hajiya Karama ne suka kai Hajiya Kaka dakinta tana musu manyan zagi kamar yar'maguzawa haka suka direta a dakinta suna zaune Hajiya na Kuka Doctor ya dawo nam ya fara daura Kaka data karye a singalalin ƙafarta sai da su Hajiya da Daddy suka rike ta dan dukan Doctor take da iya ƙarfinta. Nam ta kuma cizon su Hajiya kamar wata mayya yakushi da zagi kam sun shashi amma dai sai da aka daurata tas kafin su saketa Nusaiba tasha dariya dama itace muguwar gidan.★★★★
*_WAIWAYE ADON TAFIYA_*
*_GOMBE STATE_*
_Anguwar Pantami dake garin Gombe nanne garin su *Umma* *Malam Ayuba* shine sunan mahaifinta sai kuma Mahaifiyarta *Amina* Umma ita kaɗai Maifiyarta ta haifa sai kuma Amaryar _Malam Ayuba_ *Mairamu* tana da yara biyu maza *Kabiru* sai Kuma *Musa* yaran sun taso cikin tarbiya *Malam Ayuba* Mahaucine gaba da baya Haka ma yaransa sun gado sa duka Fawa suke yi *Malam Ayuba* mutumin kirki ne sosai akwai shi da kyauta *Amina* da *Mairamu* suna zaune cikin aminci da kaunar juna. *Umma* Asalin Sunanta *Hafsat* yarinyace mai biyayya da tsoron Allah *Hafsat* nada shekara 25year a duniya Allah ya haɗa ta da *Yusuf* . *Yusuf* dan Sokoto ne yazo garin Gombe ne duba wani Abokinsa da baida Lafiya Allah ya haɗasu da *Hafsat* aiko ba a jima ba iyaye suka shiga maganar dan *Yusuf* bashi da laifi ko kaɗan dan daga gidan tarbiya yake ba jima wa aka yi auren *Hafsat* ta tare a gidan ta dake Sokoto. *Yusuf* yana da rufin asiri daidai gwargwado yana harkar saida motoci ne kuma yana samu Alhamdulillah *Hafsat* Shekaranta guda da Aure Allah ya Azurta su da 'da namiji ranar suna yaro yaci suna *Abdul'Majid* Suna kiransa da *Majid* yaron ya taso cikin tarbiya sosai daga ɓangaren Iyayensa biyu tunda ga kan *Majid* Allah bai ƙara basu haihuwa ba Nam suka ɗauki son duniya suka daura a kansa. *Majid* nada shekara 25year Allah yayiwa Yusuf rasuwa saka makon haɗarin mota da sukayi a hanyarsa ta dawo daga Gombe yaje gaida sirikansa dama duk wata yake zuwa gaidasu Mutuwar ta girgiza Ahalin biyu sunji mutuwarsa sosai sunyi kuka har sun godewa Allah. Bayan Shekara biyu da rasuwar *Yusuf* *Majid* ya zama wani taƙadiri sam baijin maganar *Umman* sa sam ya chanja kamar ba *Majid* mai biyayya bane ya zama dan Duniya ansha kawowa *Umma* karansa Nam ko *Majid* ya haɗu da abokai ƴan duniya masu son abun Duniya nam suka daurashi a hanya shima na zuwa wajen boka. Babu abunda Bokan nam baya saka su akan zasu samu kudi sosai a duniya kowa sai ya san dasu har sasu boka yayi su nemi junansu haka kuwa aka yi a gaban boka suka tube har ma da boka suka naimi junansu suka biyawa kansu bukata(wa'iyazubillah)ko kuma yasasu su nemi mahaukaci haka kuwa zasu nema kudi kuwa suna samunsa kamar na banza. Saboda sunyi amanna da maganar boka sun yarda da maganarsa yau ne Boka yazo musu da abunda sai da ya girgizasu...
#Vote
#Comment
#ShareONE LOVE💕🤞🏻
08132761212