*ABIN DA AKA GASA...!*
_Shi yaga wuta..._🔥
*_TRUE LIFE STORY_*By
_Hafsat A Garkuwa_✨🌹Women Writer's Asso...
*_Page 21&22_*
...Hajiya Karama ta fadi Luuu! ta suma da sauri su Hajiya Babba suka yi kanta nam likita ya dubata yaga suma tayi. Ya yayyafa mata ruwa sanna taja wani dogon numfashi ta saki wani kuka, haka su Hajiya suke ba ta haƙuri *Mubajjal* kuwa ji yayi ya tsani Hajiya ƙarama dan duk abunda ya faru da *Nusaiba* itace sila. Dan da badan kyaliyanta da nuna rashin ko in kula da take yiwa Nusaiba ba da ba'a mata wannam lalatan ba. *Daddy* da *Hajiya Babba* ne suka koma gida tare da *Mubajjal* domin kar abar Hajiya Kaka ita kaɗai. Suna komawa *Daddy* ya sanarwa *Hajiya Kaka* duk abunda ke faruwa. Nam tayi wani irin guda wanda sai da ya bawa kowa na ɗakin mamaki duk da sun san zata yi abunda ya fi haka ma amma bai dace tayi akan wannam bala'in da ya kunno musu kai ba itako ko a jikin, ta ƙara da cewa "wallahi na ji daɗin wannam al'amari sosai kai wanda yayi wannam aiki Allah yashi maka Albarka" *Daddy* bai ji daɗin maganar ba, amma ya daure yace "haba Hajiya bai kamata kiyi haka ba karki manta fa kema abun nam ya shafeki tunda jikarki ce"
Da sauri Hajiya Kaka tace "kul.. karka ƙara ni sam ba jikata bace ga iya jikokina. *Mubajjah*, *Yasmin* , *Yasir* , sai kuma *Salma* sune iya ka jikokina dana sani amma wacchar ja'irar kam bana da alaƙa da ita.
*Daddy* nam da nam yayi waje dan yaji *Hajiya Kaka* zata tona musu sirrin da basu so ƴaƴansu su sani in banda *Mubajjal* da yasan zance. Babu wanda ya sani kuma sunyi alkawari babu wanda zai sani har abada amma kuma yau gashi Hajiya zata fasa tayan agaban yaransu. Yana fita Hajiya Kaka tace "aiko kayi a banza *Hamza* dan sai na fasa wannam ƙwan kowa ya ji warin sa. *Mubajjal* ne yayi saurin isa wajen ta tare da cewa "haba Hajiya dan Allah kar ki furta komai akan maganan nam kiyi hakuri ki rufesa kamar yadda kika rufe da, Inko baki rufe ba yau bazan sayo miki wannam kazar da na siyo miki jiya ba.
Aiko nam Hajiya Kaka ta washe baki tace "aiko nayi shiru *Mubajjali* na babu wanda zan faɗawa maganar nam.
Hajiya Babba ne ta fita ganin ɗan nata ya shawo kan Hajiya Rigima sunan da suka saka mata kenam. *Mubajjal* ganin hkaa yace "yanzu zanje na siyo miki Kakata ta kaina Allah ya bar mana ke"
"Amin Jikalle yauwa yi maza ka siyo min yau ko abincin gidan nam bazan ci ba kazata zan ci nayi nak. *Mubajjal* ya sa dariya ya miƙe ya fito.
Tunda suka bar Hajiya Ƙarama ta saka *Nusaiba* gaba tana kuka sosai ta yadda taga lokaci ɗaya *Nusaiba* tayi wani irin rama abun na tsoratata sosai kuka take sosai har sai da *Mubajjal* yazo ya sanar da ita kuka ba shine maganin matsalar ba tayi hakuri suci gaba da Addu'a insha Allah zata tashi sai da yayi ta mata nasiha sosai sannam tayo shiru.
Kwanan Nusaiba 13 sannam suka samu sallama saboda a lokacin ta warke kamar ba ita ba ada bata iya tafiya amma yanzu kam komai ya dawo Normal sai dai muce Allah ya kiyaye gaba.
Haka suka dunguma suka kuma gida, Hajiya Kaka tayi ta tsokanan Nusaiba duk da bata fahimci abunda take cewa ba baisa ta tanka mata ba dan Nusaiba yanzu ta zama shiru-shiru babu wannam rawan kan da shegen surutu.
Tun daga ranar da wannam abunda ya faru da *Nusaiba* har yau ba a ƙara ganin Sado ba nam ko aka fara zargin shi yayi mata wannam danyan aiki. Shi ko Sado tun daga ranar ya kuma garinsu yaje ya bude wani shagon a chan yana ci gaba da lalata yaran mutane.
Umma ta koma rayuwar ƴanci a cikin gidansu kowa yana nuna mata ƙauna da kulawa sosai tana jin daɗin zaman amma duk randa ta tuna *Sultanah* sai ta zubar da ƙwalla. Shi ko *Majid* ko a jikinsa da ya ji labarin Umma ta koma gidan su. Amma ta wani ɓangare yaji bakin cikin hakan saboda a ranar da ta bar gidan yaso yazo ya aikata abunda yayi mata daga farko amma yace sai gobe kafin gobe ita kuma ta bar masa gidan.(Kaji Shaiɗani).*_BAYAN SHEKARA BIYU_*
Abubuwa da dama sun faru sosai ciki kowa hada Auren da Umma tayi ta Auri wani Malami dake anguwarsu matarsa ce ta rasu bashi da yara ko ɗaya kuma Allah ya haɗa sa da Umma ya Aureta. *Mujahit* kuwa kuɗi sun zauna masa dan ya rushe gidan Umman sa ya gina mata wani katafaren gida na gani na fada. *Hajiya Kaka* kowa ta dade da warkewa sosai kamar bata taba karaya ba. Sai tsokanar *Nusaiba* da take tana cewa babu wanda zai aureki haka zaki ƙareshi zaman ki. Nusaiba taji zafin abun saboda yanzu tana da wayo shekarunta yanzu 11year tayi kyau da ita kamar ba ita bace rigimammiyar gidan.
A kullum *Mujahit* sai mahiafiyar sa tayi masa maganar aure amma shi sam bai ga wacce ta dace ya aura ba. Amma a yaune yaga wata budurwa wacce ta kwanta masa sosai a cikin garin Abuja yanzu ma haka shiri yake shida Nura za su je wajen ta. Cikin kwalliya suka fito sunyi ankon wani yadi mai kyau da kuma tsada sai kamshi suke zubawa nam suka ɗauki hanyar gidan su *Malika* a yadda aka musu kwatance suuna cikin tafiya Mujahit shi ke zaune a kujeran mai zaman banza yana ta latsa waya kamar ance masa ya ɗago yana ɗaga kai ya hanyi wata budurwa wacce ta fito daga wani Super Market.
A lokaci ɗaya wani tsoro da fargaba suka ziyarce shi wani irin faduwa gaba yaji Nura yake son nunawa abun da ya gani amma sam ya kasa tsabar firgicin da ya shiga. Sai chan yayi jarumtar taɓa Nura cikin zare idanu yake nunawa Nura ita cikin firgita yace "Nura ka ga....
_To wai meye *Mujahir* ya gani ne haka ya firgita haka?_
#Vote
#Comment
#ShareONE LOVE💕🤞🏻
08132761212