Wani Kataferen ɗaki ne da sai idon ka ya gane maka, domin ɗakin yayi matuƙar ƙayatuwa. Komai na wannan d'akin kalarsa ta kasancs pink color ne,Mai d'aukeh da wani ƙayataccen Royal bed, A kwance take baccin ta cikin nitsuwa da kwanciyar hankali. Tamkar wata sarauniya..
Kwankwasa kofar da akayi ne yasa ta bud' lumsassun idanta ,muryar mummy taji tana fad'in "Alisha bazaki tashi daga wannan baccin asarar da kike yi ba? kinajin gari yawaye Amma kin kasa tashi ko?"
Mikewa tayi had'e da fad'in "Gani Nan zuwa Mummy."
Bathroom ta fad'a ta watsa ruwa, tun da Asuba Daddy ya tada ta tayi sallah tana idar da sallar ta koma bacci.Fitowar ta Kenan daga bathroom tana kokarin saka kaya bata an Kare ba sai taji saukan duka a bayan ta, wani yar karamar Kara ta saki a tsorace ,cikin kuka take fad'in "Mummy am Sorry yanzu zan fita."
"Don ubanki Ni sa'ar kice, ko Ni baiwar kice da ina Chan ina aiki a kitchen kina Nan kina shirme?"Taji zafin bugun da ta kaima ta hakan yasa hawaye ya tsiyayo mata har kuncin ta,mummy na ganin hawayen ta kama hab'ar ta Tace "jimin ja'irar yarinya me na miki kike kuka?"
Cikin muryar kuka tace "Mummy ba kuka nake ba."Wani gigitacciyar mari ta mata had'e da fad'in "Yanzun Ubanki kikeyi ne, Wallahi Alisha ki kiyaye ni,bana son munafurci,yanzu me na miki da kike kuka?"
"Kiyi hakuri Mummy, Wallahi bazan sake ba"
"Ya dai fi miki,dama kiyi sauri ki tashi ki sa kaya ina jiran ki a kitchen"
Ciki ciki ta amsa da "Toh."Ban 'daki ta koma, ta wanko fuskar ta, ta zauna a gaban mirror tana kukan zuci a gaggauce ta shafa mai, ta nemi Riga da wando jeans ta saka sannan ta d'auki karamin baby Hijab ta sa , tayi sauri ta fita ta nufi kitchen, a hanyarta ta zuwa kitchen ta hango daddy a parlor yana zaune.
Ta nufi inda yake, cikin girmawa ta durkusa har kasa ta gaishe shi, ya amsa cikin sakin fuska, Murmushi yayi yace "Mamana kin tashi lafiya?"
"Lafiya Lau daddy, kana zaune kana hutawa"
"Eh kin San weekend, sai da haka.""hakane a huta lafiya, Bari na Shiga kitchen"
Murmushi yayi yace "Alisha ina jinki da mummyn ku, me Kika yi mata ne da sanyin safiyar Nan"Kai a kasa Tace "Babu komai daddy"
"Na sani dama baza ki fad'a ba, maganar da na saba fad'a miki shi Zan sake fad'a miki, ki cigaba da hakuri da mummyn ku, sannan nasan ko baki fad'a ba kina kokonto akan ba itace ta haife ku ba ko?"Kai ta d'aga alamun eh, yace "To ba haka bane, Haleema itace mahaifiyar ku, ke da kannen ki, abinda nake so dake shine ki cigaba da hakuri akan Wanda kikeyi, Kinga ke mace ce, a ko ina ana son mace Mai hakuri, kin...... "
"Alisha!!! Alisha!!! Suka tsinkayo murya mummy cike da masifa take Kiran sunan Alisha.
Girgiza Kai yayi yace "Tashi kije, ina ga tana so ki taya ta wani aikin ne"
Mikewa tayi tace "Toh Daddy." Da sauri ta Mike da niyar Shiga kitchen d'in.Juyawar da tayi ta hango Mummy ta nufo su, Saida ta ji zuciyarta ta fara bugawa uku uku, ga mamakin ta sai taga mummy na Murmushi tun Kan ta karaso inda suke tace "Daddy and Daughter,Kuna Nan Kuna abinda aka saba,nasan gulmata kuke."
Yar karamar dariya yayi yace "A'a mu ba gulmar ki muke ba, gaisawa mukeyi Kuma kin San yanzu sun kusa rubuta WAEC d'insu, ranar Monday nake so nayi mata registration"
"Hakane Allah ya kaimu,ya basu sa'a"
Ya amsa da "Ameen" a tsawace Tace "Alisha kin San Allah ki kiyaye ni,ki wuce Kitchen kije ki daga min sakwara, sannan idan kin gama kije ki ta da Fa'eez da Hisham, baccin ya Isa Haka"Ta Masa da to had'e da barin gun, tana Shiga kitchen ta Fara aikin da ta sata, bayan ta gama kirb'a sakwarar ta sa a leda ta jera a food flasks, bata fita a kitchen d'in ba sai da ta gyara shi tsaf sannan ta wanke kwanukan.
YOU ARE READING
JINNUL KAMIL (A True Life Story Of Alisha)
HorrorJINNUL KAMIL Labari ne da ya faru a zahiri, kuma ya kunshi abubuwan dake faruwa yau da kullum tsakanin mutum da Aljan. labarin yana cike da abin tausayi, mugunta da zamantakewar iyali, harda sakaci irin na iyaye musamman Mata.Koda wasa ba'ayi laba...