*KUMO*
Daddy da Baba na hango a gindin wato bashiyar neem dake tsakiyar compound na gidan, zaune suke akan plastic chair da alama suna magana ne mai muhimmanci "Yallabai na gama duk abubuwan da zanyi ina ga gobe zan koma gida in sha Allah" Daddy ke wannan maganar.Malam Dauda yace "Toh toh Hameedu har ka gama kenan?"
"Eh yallabai"
"Toh madallah gaskiya ina jin daɗin aiki daku ina samu kuma kuna samu"
"Nima haka yallabai, amm dama nace......" sao kuma yayi shiru yan tsosa kai, baba gyara tsayuwarsa yayi kana yace "Faɗi mana ina jinka kar ka damu yi magana kai tsaye"
"Akwai magana mai muhimmanci da nake so muyi da kai amma ba yanzu ba""Ikon Allah magana mai muhimmanci hameedu kuma ba yanzu ba,ai kawai muyi ta yanzu"
"A a yallabai zan dawo musamman don wannan maganar"
"Toh ai hikenan Allah ya gwada mana"
"Ameen"*BAUCHI*
Bayan sun idar da sallan ne ko waccen su tayi wanka suka shirya suka shiga cikin school,inda yace su jira shi suka nufa suka zauna har suka ɗauki kusan mintuna 30 amma shiru bai zo ba Alisha ne tayi tsaki tace
"Mtwss Jamy kinga haryanzu bai zo ba ko nifa gaskiya na gaji bana son jira" Alisha ta faɗa tana turo baki girgiza kai Jamy tayi tace "To ke banda abinki wa ya gaya miki me nema yana fushi?""Don ina so ya koya min abu ba shine ya bashi damar wulakanta mu ba ,tun fa ranar da muka masa magana na lura guy ɗin nan yana da rainin hankali shi idan an bar shi yana taka ma ne dakyau mtsww to waye bai da kyauwun......"
Salma tace "Alisha kiyi shiru" yayin da Jamy na mata alama da ido tayi shiru amma ina sai zuba take ita a lallai an wulakanta su."Nifa tafiya zanyi bazan iya jiran nan ba"
Juyawar da zatayi taji ta faɗa a kirjin mutum turus tayi zata cigaba da masifa tana ɗaga kanta idanun ta suka mata tozali da shi rawa bakin ta ya fara yi ta rasa abinda zata ce shi ko murmushi yayi kana yace "Kiyi hakuri Rankishidaɗe na tsaya cin abincine ba niya na bane na shanya ku" ya haɗa hanayen sa wuri guda alamun roko, sun kuyar da kanta kasa tayi ta kasa ko da motsine.
Rabewa yayi ta gefen ta ya zauna a kujeran da ta tashi yace "Am Sorry jamy na shanya ku na ɗan......"
Jamy tayi saurin katse shi da faɗin "laa wallahi kar ka damu tunda kazo ai shikenan"
"Toh ai gani nayi zakanyar taki har ta bata rai" ya karasa maganar yana murmushi salma tayi charaf tace "Kayi hakuri Alishan ce wani lokacin sai a hankali"
"Bakomai so where were we? Wasu courses zamuyi ne?"
"Stats muke so a fara mana amma dai dukka courses din ma fa muna bukata ko Alisha?"Alisha da haryanzu take tsaye tayi ƙirkirerren murmushi tace "Eh hakane"
"Okay kun fito da material din ko?"
"Eh gashi nan" jamy ta faɗa haɗe da mika masa handout ɗin dake hannun ta kar ba yayi ya dan duba kana yace "Okay bara mu fara ko"
Jamy tace "Alisha ki zauna mana"
Da jaan kafa ta zauna a kujeran da yake kusa da S Adam , ajiyar zuciya yayi ganin duk a takure take yace "Ummm Alisha ko please ki sake jikin ki naga duk a takure kike" murmushi kawai tayi nan ya fara musu introduction dallah dallah ,yana musu bayani da turanci haɗe da hausa Salma da ba course ɗinta ba amma ta nutsu tana sauraron su da alama ita ma tana fahimta , sun dauki tsawon awanni biyu kana ya numfasa yace "I think zamu tsaya anan kar yayi yawa kuma azo ba a gane ba ,amma da fatan am not fast kuna fahimta ko?"
Jamy da Salma suka amsa da "Eh" jin Alisha tayi shiru ya maida duban sa gare ta yace "Kefa Alisha?"
"Eh ina fahimta"
"Okay good da kwai mai tambaya ne? Ko da kwai wani abu da baku fahimta ba?"A tare dukkan su Uku sukace sun fahimta ,mikewa yayi haɗe da faɗin "Okay sai gobe naga dare yayi kunga ku matane bai kamata kuna dare a waje ba"
Suma mikewa sukayi suka masa godiya ya amsa da bakomai yayi tafiyar sa suma suka kama hanyar komawa hostel, sun kusa shiga hostel Alisha fa waiga da faɗin "Na'am"
Salma tace "Ke kuma fa ke da wa?"
Alisha tace "Ji nayi kamar an kira suna na" ta cigaba da waige waige amma bata ga kowa ba.
YOU ARE READING
JINNUL KAMIL (A True Life Story Of Alisha)
HorrorJINNUL KAMIL Labari ne da ya faru a zahiri, kuma ya kunshi abubuwan dake faruwa yau da kullum tsakanin mutum da Aljan. labarin yana cike da abin tausayi, mugunta da zamantakewar iyali, harda sakaci irin na iyaye musamman Mata.Koda wasa ba'ayi laba...