CHAPTER 15&16

31 3 0
                                    

Tsaye suka tarar da ita hannun ta na dama a kunkumin ta yayin da ɗayan hannun nata tana rike da hannun wani yaro, kana ganin yanayin tsayuwar ta da jijjiga jikin da take kasan ba lafiya ba, wani irin kallon take bin su da shi mai wuyan fassarawa, Cike da mamaki Mama Talatu ke kallon Mero dillaliya tace "Lafiya Mero na ganki haka?" a ɗan ɗaɗɗare tayi mata tambayar tamkar an sata dole.

"Ina fa lafiya yarinyar nan taki mai kama da aljanu ta samin yaro a gaba da zaran yaron nan ya fita sai ta dake shi ko ta kwace mishi goruban da na sayarwa ne kuma baza ta biya ba akan me? Goruban na kanin Uban tane?" cike da masifa take maganar baba kuwa jikin sane ha hau rawa an tab'a ƴar lelen sa ,nuna ta ya yi da yatsa yace "Ke Mero har cikin gidana? Har cikin gidana zaki shigo kina zagin ƴar tawa sabida ba kunya kike dashi ba ko? To sai me don taci goruba nawa ne gorubar?" yana magana haɗe da zura hannu a aljihu ,cike da mamaki Mama ke kallon sa haka ma Mero ya ɗaura da faɗin "kar kari na san ba zai haura duba ashirin bako ko? To gashi" ya watsa mata kuɗin cikin da zafin nama ,kuɗine wanda zasu kai dubu ashirin ko fin hakan ma,yan dubu dubu ne, baki a buɗe Mero ke kallon kuɗin da ya watsar. Mero na ganin kuɗi duk matsifar da ta shigo dashi duk sai taji ya kau ta haɗiyi wani irin yawu tana rarraba ido tana kallon kuɗaɗen.

Mama tace "Haba Malam wannan ba dai dai bane ka mata ai ka tsawatar ma yarinyar nan ,tunda ai kara ta kawo maka ba wani abu ba,ni a gani na idan yaro yayi laifi kamata ai a hukun ta.........." bata kai ga karashe maganar ta ba a tsawace yace "Daka ta Talatu ,kin san ni kin san Halina bana son haka akan me? Wai ace kamar ni ,ni za'a shigo har cikin gida na ana kiran ƴata da Aljana,da kuɗina da mutuncina, sanin kanki ne cikin garin nan kaf babu mai irin dukiya ta amma wai akan goro ba"
"Amma malam....."
Hannu ya ɗaga mata "Ya isa haka kar na kuma jin kince komai" ya juya ya fuskanci inda Mero dillaliya take yace "Ki fice min da ga gidan"

Jikina rawa ta shiga Tattara kuɗin Ɗanta na taya ta,ya juya zai koma ɗaki ya tsinkayo muryar Mama na faɗin da "Allah mero kiyi hakuri insha Allah zan mata faɗa kiyi hakuri dan Allah,ban san meyasa yarinyar nan bata jin magana ba"
Mero kuwa sai washe baki take tana faɗin "Ahh ba komai ba komai wallahi ai haka yara suke,zata daina yarinta ne"

Da saurin sa ya dawo yace "Wallahi wallahi na dawo na tarar dake anan sai na saba miki munafukar banza da kin san cewa yarinta ne kika zo ki nai mana tijara, a dai dai nan ta gama tattara kuɗin ta ɗan duka kaɗan haɗe da faɗin "Ayi Hakuri Alhaji Na bar ku lafiya"

"Da kar ki bar mu lafiyan mana" duk da ta fice amma hakan bai hana shi cigaba da magana ba yana ɗaga muryar yana ɗaga hannu shi a lallai an tabo sa.

Mariya da tun shigowar mero dillaliya tana labe tana kallon duk dramar da suke yi sai faman murmushi take tana yagan naman ta hankali kwance, har wani rurrufe ido take alamun naman ya mata daɗi, Mama girgiza kai tayi kawai ta juya da niyar komawa ɗakinta ta hango ta tana tsaye tace "sannu mariya kin kyauta hankalin ki ya kwanta ko? Allah ya baki sa'a" tana kai nan ta yi shigewar ta ɗaki.

Baba kuwa na jin maganar da mama take yayi shiri tsit kamar anyi ruwa an ɗauke ,cikin sanyin murya yace "zonan mamana"
Fitowa tayi daga ɗakin hannun ta rike da Ledan tsiren tana tafiya tana ci bakin nan a ciki dakyar take iya taunawa,dafa kanta yayi yace "Haba Mamana ci a hankali mana ba mai kwacewa idan ma bai ishe ki ba sai in sa a karo miki" girgiza kai kawai ta kasa magana.
Yace "Shiga ciki ki zauna ki ci abincin ki" girgiza kai tayi alamun to ta koma cikin ɗaki ta cigaba da cin naman ta.

*BAUCHI STATE UNIVERSITY*
Bayan sun gama lectures suka koma hostel a gajiye, Alisha kwanciya tayi yayin da Jamila ta faɗa ba ɗaki bayan tayi wanka ta fito ganin Alisha a kwance ta baje tace "Madam Ya haka baza kiyi wankan ba?"
"A a gaskiya bazan iya ba na gaji sai na tashi daga bacci"
"A a baccin Bayan la'asar bakyau nasan kin sani,ki daure dai kiyi wankan in yaso idan mukayi isha sai kiyi baccin" amma alisha lumshe idon ta kawai take tayi ta mata magiya kan ta mike tana tura baki ta shige ɗakia duk abinda suke yi Salma na kallonnsu, tana son yi musu magana amma Girman kanta ya hana ta suma kuma haka sukayi kamar nasu san tana gun ba.


JINNUL KAMIL (A True Life Story Of Alisha)Where stories live. Discover now