Da sauri ta jaa da baya da niyar gudu daddy na ganin hakan yayi saurin rike ta ,tana ganin ya rike ta,ta buɗe baki da niyar ihu, murya a dake Daddy yace "Kul! Kar ki kuskura kimin ihu,kina min ihun sai na batar dake babu wanda zai kuma ganin ki mark my words"
Ji kuke tsit mariya ta kasa koda motsine banda numfashin da take yi babu abin da ya ke motsi a jikin ta "Maa my wod ɗin shima wani zagin ne kenan to wallahi ni bani ka zaga ba kan ka ka zaga" ta ayyana hakan aranta.
Daddy jin tayi shiru ya zazzaro ido waje "Au zagina ma kike?"
"Ni ni ban zage ba"
"To meyasa naga kina murguɗa min baki?"
"Wayyo kayi hakuri dan Allah ni ba zagin ka nayi ba"
"To me ya kawo kinan kike neman tsorata ni?"
"To ba baba bane ya ce na kawo maka man Zafi" ta karisa tana nuna man zafi dake hannun ta,ya mutsa fuska tayi kana ta marairace tace "Dan Allah ka sake ni hannu na ciwo yake min"
Sai a sannan ya tuna yana rike da hannayen ta yayi saurin sakin ta yace "Me ya faru ne a gidan naku nake ta jin ihu?"
Dariya ta kwashe dashi harda rike ciki ganin shi ba dariyar yake ba sai tayi tsit ta fara faɗin "Dama fa da na bar nan ɗazune cikina ya murɗa shine fa nayi gudu na shiga gida ,baba da mama suka tsorata........" tiryan tiryan ta bashi labarin duk abinda ya faru har izuwa inda yazo suka daka shi, a sannan ne daddy ya tuna bakin sa da hancin sa ya fashe amma labarin da take basa ba karamin dariya ya bashi yana kokarin danne wa amma ya kasa mariya sai ganin shi tayi ya zauna a kushin ɗin da yake dab da shi ta ɗauka gajiya yayi da tsayuwar sai ji tayi yana dariya sosai da sosai ya rike cikin sa a ransa yana mamakin irin wannan ahali, a yayin da soyayyar ta da kaunar ta yake karuwa a zuciyar ta sam yarinyar bata damuwa sai shirme, (Niko nace anya daddy Mariyan ce ba ta da damuwa? Wannan sai ta kashe mutum da bakin ciki tun kwanan sa bai kare ba)
Ganin yana dariya ita ma ta fara dariya, yana jin ta fara dariya ya tsaya yana kallon ta tsit tayi haɗe da mika masa man zafi tace "Gashi nan mama tace kar na daɗe"Kan sa ya ɗaga ya kalli agogon bangon dake ɗakin har 10 ya gauce yace "Dare yayi ki tafi sai da safe,amma ki sani sai na rama wannan" yana maganar haɗe da mikewa ya nuna mata fuskar shi, waro ido mariya tayi tace "Kayi hakuri dan Allah,ka yafe min kamar yanda ka yafe min wanchan karon"
"Hmm ai wanchan ma ba hakura nayi ba tara miki nake yi zaki sha mamaki ba ke kince baki da nitsuwa ba,zan gyara miki zamane" mariya ji take kamar ta kurma ihu baki buɗe take kallon sa.
Shi kuwa ya nufi hanyar bedroom bayan ya karbi man zafin ,har zai shiga ya waigo yaga tana nan tsaye tana kallon sa ,sai yaji ta bashi tausayi yace "Ki fice min daga ɗaki in ba so kike na zo na hukunta ki tun yanzu ba" ta sauri ta juya zata arce da gudu da ɗba karfi yace "Kul kul kar naji kar naga kin yi gudu wallahi kika yi guda kika kuma tsoratar da yallabai sai na saba miki"
Sum sum ta fara takawa kamar kazar da ruwa yayi wa duka yace "Bar min kofan zakiyi a buɗe sauro su shiga?"Tana fita ta ja kofar,girgiza kai yayi yasa kai ya shige ita kuwa tana jin motsin ya shiga ciki ta buɗe kofar ta gyara tsayuwar ta kana ta jaa kofar da dukkannin ƙarfin da Allah ya hore mata ji kuke garaaaaaam, a mugun razane daddy ya fito palor don ji yayi kamar karar bindiga da sauri ya leka ta window ya hangi mariya tana fal fala gudu kamar kafarta zai taba ƙeyar ta,girgiza kai yayi ya koma ya shiga bathroom ya watsa ruwa ya ɗauro alwala yayi sallah raka'a biyu haɗe da shafa'i da wuturi bayan ya idar ya fara jero addu'o'i yana gamawa ya naɗe prayer matt ɗin ya ɗale gado.
Kallon silin yake yi sabida bacci ya kaurace masa kwata kwata Halima ce ta faɗo masa a rai yana tuna irin soyayyar da suka sha kafin aure da kuma bayan aure lokaci ɗaya ta canza, shi wani abun da takeyi ma mamaki yake basa,amma ya ɗauki alkawarin sai yayi maganin ta duk ma yanda za'ayi sai ya auri mariya shirmen ta kaɗai zai sa ya manta duk wani bakin ciki da takaicin Halima, a haka har bacci yayi awun gaba dashi.
YOU ARE READING
JINNUL KAMIL (A True Life Story Of Alisha)
HorreurJINNUL KAMIL Labari ne da ya faru a zahiri, kuma ya kunshi abubuwan dake faruwa yau da kullum tsakanin mutum da Aljan. labarin yana cike da abin tausayi, mugunta da zamantakewar iyali, harda sakaci irin na iyaye musamman Mata.Koda wasa ba'ayi laba...