CHAPTER 17&18

40 3 0
                                    

Bayan Alisha tayi wanka itama alwalar tayi, fitowarta ta tarar Jamy ta idar da sallah tana azkar, itama sallayarta ta shimfiɗa ta tada sallah,bayan ta idar tayi azkar anan suka buɗe babin hira suna sharar dariya hankali kwance.

Sun daɗe suna hirar Jamy sai hamma take Alisha tace "Yadai Jamy? Yunwa gajiya ko bacci?"
"Wallahi yunwa nake ji,bari kiga na sama mana abinda zamu sa a aciki" tana maganar haɗe da mikewa ta naɗe sallayar ta ajiye shi a mazaunin sa.

Alisha tace "Jamy acici daɗina dake bakya wasa da cikin ki"
"Ahhh to me ya fi raina? Idan na mutu ba shikenan ba so gara naci kawai"
Tabe baki tayi tace "Uhmnn gaskiyar ki fa"
"Ahtooh,sha'awar doya da sauce na kwai nake ji"
"Gaki ga su"


Nan ta fere doya ta ɗaura a gas,ta ɗauki kusan awa ɗaya kan ta kammala girkin,a plate ta juye musu sauce ɗin kwan na gefe,ta ɗauko musu pure water ta dere su a gaban Alisha nan suka shiga cika cikin su.bayan sun gama Alisha tace "Alhamdulillah saura fita lectures"
"Kashh ni wallahi na ma manta da wani lectures gaskiya na fara gajiya" faɗin Jamy.
Alisha tace "Chaaap ɗi me ma akayi? Kar ki manta fa yanzu muka fara so idan zaki ma sake jikin ki,ki sake yanzu tashi zakiyi muyi sallah by 4 za a shiga"

"Mtsww baza ki gane bane Alisha wallahi nikam ana shiga hakkina"
"Laaa to wani ne ya saki dole? Sai ki koma ki faɗawa su baba kefa baza ki iya makarantan ba kinga kuɗin da za a tura miki a makarantar sai a fara miki taru"
Dundu jamy ta kai mata ta kauce tana dariya ta shige ban ɗaki.

Jamy tace "zaki fito ki sameni ai"

*GOMBE*
Mummy ne zaune ta a katafaren parlor su ta ɗaura kafa ɗaya akan ɗaya tana taunar chewn gum, gefen ta kuma Aisha ne Rabi suna hira,da sallama daddy ya shigo bakin sa uku basu ji ba suna ta hirar su,Aisha da rabi ne suka amsa ɗago kai tayi kallo ɗaya ta masa ta kau da kanta kallon ta yayi ya girgiza ya nufi hanyar da zai sada sa da ɗakin sa, ya tsinkayo muryar su suna gaishe sa ba tare da ya tsaya ba bare kuma ya juya ya amsa musu haɗe da haura wa sama.


Sun ɗauki tsawon lokaci babu wanda yayi magana, Rabi tace "Hali baza ki bi bayan mijin ki ba?"
"Mtsww inje in masa me?" faɗin mummy.
"Allah Halima ina guje miki ranar da zaki kure Abdul,ina jiye miki ranar da zaki sa yaje ya auro miki wata idan ya auro wacce ta fiki kula dashi kina ji kina gani zata kwace miki shi don wallabi......"

"Ya haka?" Aisha ta katseta ta ɗaura da faɗin "Ai wannan muguwar fata ne"
"A'a ni ba fata nake mata ba gargaɗi nake mata idan bata gyara ba abubuwan da na lissafo ne zasu faru"
"Kinga Rabi wannan ba shawara bace kika bata akan me zaki rika faɗin hakan Ke kenan kullum da zaran an fara magana sai kiyi ta maganar biyayya biyayya,ke ki saurare ni kiji......" ta gyara zamar ta kana ta ɗanyi kasa da murya tace "Mazan yanzu fa sai da haka idan ta sake mishi dayawa sai ya raina ta amma hakan da takeyi shi zai sa ya rika jin shakkar ta"

Mummy tace "Hakane Qawata ai sai ya raina ni ,kuma maganar aure wallahi bai isa ba, sai dai bayan raina bazai ma fara wannan gangancin ba"

Baki a buɗe Rabi ke kallon su ta kalli wannan ta kalli wanchan, kana ta maida kallon ta ga Mummy tace "Sai yanzu na fahimci inda matsalar ki take haleema,amma haleema Allah ya gani kuma shine shaida na fita hakkin ki"


Ta ɗauki jakarta tayi hanyar fita sai da ta kai bakin kofa tace "Think Twice halima zaki zauna wacce bata san mene ne aure ba,bata san ya aure yake ba tana baki shawara da ilimin ki da tunanin ki? Kaico ina jiye miki ranar da zaki yi dana sanin actions ɗinki,Na barku lafiya tana kai nan ta buɗe kofar ta fice.

Rai a matukar bace Aisha ta miki ta ce "Kambu, Lallai Rabi ni zaki zaga ni zakiyi wa gorin aure banza shasha ke me auren ya tsinana miki aure sama da shekaru 15 baki taba batan wata ba,har ni zaki zaga?"


JINNUL KAMIL (A True Life Story Of Alisha)Where stories live. Discover now