Ba a ɗauki Mintuna 20 ba Malam Dauda Ya dawo yayi ma Daddy iso, Yar karamar jakar sa na ratayawa a baya ya ɗauko a bayan motar sa, tare suka shiga gidan, Babba gidane part biyu ne a gidan sannan akwai boys quaters, Wani madaidaicin ɗaki ya kai sa parlor ne da bedroom sai Toilet a ciki daga wajen Gidan baza kayi tunanin ɗakuna sun haɗu haka ba sai ka shiga ciki.
Kallon ɗakin Daddy yake yana murmushi ɗakin yayi kyau sosai maganar Malam Daudane ya dawo dashi daga tunanin da yake "Yauwa ga ɗakin nan akwai ruwa aciki sannan Idan kana bukatan ruwan ɗumi akwai heater ko kuma ka tura cikin gida matar gidan ta aiko maka"
"Gaskiya nagode sosai Allah ya saka da alhairi"
"Aaa kar ka damu kar ka damu,yanzu dai motar takan nan zaka shigo da ita cikin gida akwai fili a ta baya ka ajiye ta a wajen a chan nake ajiye tawa motar kan na sayar da ita"
Murmushi kawai daddy yayi ya ajiye jakar hannun sa fita sukayi a tare daddy ya shiga motar Shi kuma Malam dauda ya wangale masa gate ɗin.Bayan ya shigo ya maida gate ɗin ya rufe,bayan yayi parking na motar ya fito ya koma masaukin sa, wanka ya shiga bayan ya gama ya ɗauro alwala ya yi sallar La'asar ya zauna yaba azkar,tunanin yarinyar nan fal aransa yana tunata sai ta tsinci kansa yana mai murmushi a bayyane yace "What's wrong with you Abdul? Kai da ya kamata kayi fushi da abinda ta maka? Hmm koma ina ta shiga sai na nemo ta in ji dalilin ta nayi min haka"
Yana nan zaune aka kira sallar magrib anan yayi sallar Magriba da isha,bayan ya idar ya kwanta a farlor ya tattara dukkan nitsuwar shi yana duba laptop ɗinsa.
Mariya sai da akayi sallar magrib ta dawo cikin gidan ta tarar da Mama na zaune a tsakar gidan ta gama wanke-wanke kenan.
"Assalamu alaikum walaikumussalam, Mama wanke wanke kike yine?" da wani irin kallo mama ta bata amsa tana faɗin "Mariya wai dan Allah meyasa ba ki jin magana ne? Tun safe da kika sa ƙafa kika bar gidan nan ban sake ganin ƙeyar ki ba sai yanzu ina kika je?"
"Wallahi mama babu inda naje gidan Kaka inna naje" faɗin mariya sai jujjuya ido take irin ko a jikin ta ɗin nan.
"Babu inda kika je? Wato ni ɗin makauniya ce? Ko kuma bani da hankali da bazan san kina nan? Gidan kaka inna na nufin gidane kenan?" mama ta faɗa a hasile.
Turo baki gaba tayi tace "Ni dai bance ba, Kuma ai chan da nan duk ɗayane gidan mune ehe""Mariya ni kike juyawa baki?"
"dan Allah mama surutun ya isa haka ke bakya gajiya ne tunda na shigo gidan nan fa kike ta faɗa" ta karisa maganar haɗe da kauda kanta gefe.Rike ha'ba mama tayi haɗe da faɗin "Iyeee lallai mariya wato ma ni ce nake ta surutu ko?" ko kallon ta mariya ba tayi ba bare ta bata amsa sai muzurai take ɗan dukawa mama tayi daga tsayen da take,mariya razana tayi ta ɗan ja da baya daga zaunen da take girgiza kai mama tayi ta mike "Zauna ni ba dukun ki zanyi ba Mariya na san ko na dake ki ma a banza nayi don bashi zai sa ki canza hali ba,tsakanina dake sai addu'a don bazan bari ki kashe ni da bakin cikin ki ba"
Wani irin kallo mariya tayi wa mama kana ta kawar da kanta "lallai ma maman nan wato nice ma zan kashe ta.......?"
"Zagina kike mariya?" mama ta katse ta.
Murguɗa baki tayi haɗe da mikewa kana tace "Ni ba zagin ki nayi ba,akan me zan zage ki mama"
"Ai da wasu abubuwan da kike yin da zagin nawa kikayi nasan kin rika ja'irar yarinya kawai."Hanyar cikin ɗaki ta nufa mama tace "Zonan ina zaki?"
"Ɗaki kwanciya zanyi"
"Eh dole ai an gama karaɗa gari sai kwanciya ai baki ma Maganar sallah to dawo nan aikan ki zanyi" kumbure kumbure take tana jan kafa ta tsaya daf da mama tace "Gani"Murmushin takaici mama tayi kana tace "Ki shiga kitchen akwai food flask dana ajiye a kan try ki ɗauko min"
Da jan kafa ta shiga kitchen ta ɗauko mika wa maman tayi da ta zauna tace "Gashi" mama da haushin mariyan take tace "Au ɗaura min zakiyi a ka? To ɗaura tunda baki da hankali." ai kuwa mama na rufe baki sai ji tayi ta ɗaura mata a ka,try ɗin ta tangal-tangal zai faɗi mama tayi saurin rike shi baki ta ɗauke da salati "oh ni ƴasu Mariya ke wace irin shasha ce haka,baki san gatse bane? Daga nace ki ɗaura sai ki ɗaura min maza sauke min aka"
Zumburo baki tayi tasa hannu ta sauke.
YOU ARE READING
JINNUL KAMIL (A True Life Story Of Alisha)
HorrorJINNUL KAMIL Labari ne da ya faru a zahiri, kuma ya kunshi abubuwan dake faruwa yau da kullum tsakanin mutum da Aljan. labarin yana cike da abin tausayi, mugunta da zamantakewar iyali, harda sakaci irin na iyaye musamman Mata.Koda wasa ba'ayi laba...