CHAPTER 27&28

42 3 0
                                    

"Yauwa Alisha kinga wanchan shine gayen da nake faɗa miki" tana mata nuni da wani saurayi Baki ne amma bakin sa na sheki gashi dogo mai faffaɗan kirji,gashin kan nan nasa a gyara baki ƙirin sai sheki yake yana kyalli,sanyaye da riga da wando na kaftan sky blue an masa irin ɗin kin nan da maza keyi wanda bai kai gwiwa ba hanun rigar kuwa guntu ne ya rike shi ɗam ɗam.
   Cike da rashin fahimta ta kalli wanda take nuna mata kana ta maida kallon ta ga jamyn tace "Wane ne shi ɗin?"
"Kya jiki da wata magana dan Allah malama to shine wanda nace miki zamu mishi magana ya rika mana tutorial mana"


"Au oohhh wallahi na manta nema da zancen kwata kwata Toh yanzu yaushe zamu masa magana?
"Ko yanzu ma" faɗin Alisha

   
      Salma tace "da alama maganar ba tawa bace"
Alisha tace "Gaskiya ba naki bane gaskiya,don ɗan department ɗin mune"
"Oh to Fatan alhairi"

     Jamy tace "Muje man mu mishi magana yanzu"
Da toh ta mike Alisha tace "Muje mana salma"
"Aa kuje ni ina nan ina jiran ku"
"Okay tohm"


         Hannun Alisha jamy ta rike suka nufi inda suke ,su biyune da Alama  karatu suke da sallama a bakin su suka isa inda suke.

Ɗago kai kai samarin suka yi a tare Ya sauke idanun sa akan alisha haka kawai ya tsinci kansa da sakar mata murmushi.
"Barka dan Allah idan baza ka damu ba muna son magana da kai"
Nuna kan sa yayi haɗe da faɗin "Da ni kike ko abokina?"
"Da kai nake dai"
"Oh to ina sauraran ku"
"Please ba a nan mu ɗan koma daga gefe"
Kallon abokin nasa yayi kana yace "No kar ki damu wannan aminina ne kuna iya magana a nan ba matsala"

Kallon Alisha jamy tayi,Alisha ta mata ido.da su tafi amma jamy sai tayi kamar bata fahimci me take nufi ba.
        Alisha a zuciyar ta tace "Guy ɗin nan da na rainin hankali hmmm"
Murmushin gefen baki jamy tayi kana tace "Ni suna na jamila Auwal wannan kuma qawata Alisha Abdulhameed Adam,dama magana ne akan......." Saurin rike hannun Jamy Alisha tayi tace "Jamy bari kawai mu tafi nikam na fasa"
"Ban gane kin fasa ba?"
    "Ta ina wannan zai mana abinda muke bukata daga gare shi ki duba kiga fa magana ma mukace zamuyi dashi amma ya fara wulakanta mu ina ga kuma yaji abinda muke so ya mana gaskiya na fasa mu tafi kawai"
"A a Alisha tunda mun zo ai shikenan" maida kallon ta tayi garesa tace "Am sorry please magana ne dama akam Tutorial muma computer scince muke akwai courses ɗij da suke chaza mana kai shiyasa muka yanke shawarar mu nemi wanda zai rika guiding ɗin mu sai aka mana kwatancen ka,an sanar damu kaine Best student a department ɗin gaba ki ɗaya shiyasa ba muyi ƙasa a gwiba muka neme ka"

Waro ido yayi yace "Laaah ni ɗin wai? Anya ni kuwa aka ce miki?"
Ƴar karamar dariya tayi da yanayin da yayi maganar murmushi tayi tace "Eh kai ba kai bane Saifullahi Ibrahim Adam wanda akewa lakabi da S Adam ba? Ko ba kai bane"
Abokin sa yace "Tabbas shine bakiyi kuskure ba"
"Yauwa na sani ai daga majiya mai karfi naji labarin"
Dariya sukayi dukkan su yace "kamar yadda kika ce suna na Saifullahi wannan kuma Aminina ne Sunan sa Isma'il,yanzu abinda za a yi ki bani number ki zan nemi ki  zamu yi magana"
"Alright 090............" Bayan ya gama shigarwa ne yace "Jamila ko?"
"Eh hakane jamila"
"To nayi saving zan kira ki"
"Thank you so much sai na jika,Alisha ya naga........" waigawar da zatayi taga babu kowa cike da rashin fahimta tace "Ahh ina kuma take"


    Isma'il dariya yayi yace "Ai ta daɗe da tafiya tunda tace ku tafi kika ki tafiya tayi tafiyar ta,Amma ƙawar nan naki tana ji da kanta" ya karishe maganar murmushi ɗauke a fuskarsa.

      "Allah sarki Alisha na da saukin kai da daɗin zama amma fa sai ka zauna da ita zaka fahimci hakan,bari naje na duba ta sai anjiman ku" ta karisa maganar haɗe da juyawa.

  

        S Adam yace "A miki magana a whatsapp"
"Okay tohm" tace haɗe da fara tafiya.

JINNUL KAMIL (A True Life Story Of Alisha)Where stories live. Discover now