CHAPTER 19&20

29 3 0
                                    

A zauren gidan taji taci karo da mutum da sauri ta jaa da baya ganin Baba ne hakan yasa ta washe baki haɗe da faɗin "laa baba kaine dama"
"Nice ƴar baba ina zaki ne haka da gudu?"
"Wallahi baba mama ce fa ta takurani wai naki nayi aure ni kuma gani nayi haryanzu ni yarinya ce,baba kaifa kace min shekaruna 16 bara kuma mama sai kwatantani take da akuya"
Dariya ya fashe dashi "Haba akuya kuma mama na?"
"Eh fa wai da haihuwar akuyace da ba haifi yara dayawa to in ba haka take nufi ba mene ne?"


Ciki muryar dariya yace "Baki dai fahimce ta ba ne,abinda take nufi da ace ke akuyace da kin haihu"
"Auuuu dama haka take nufi? Baba ai kasan maman ne hausan nata bata gama nuna ba shiyasa"
"Allah ya shirya min ke mamana yanzu ina zaki?"
"Rumfar Ɗan liti zani ina sha'awar bredi sa shayi"
"A a akwai su a gida ai da kayan shayin da bredin duka harda madara."


Tunda ya fara maganar ta turo baki gaba cike da shagwaba tace "Baba nifa nashin nake so ai nasan akwai a gidan"
"Toh to ai duk ɗayane da fatan kin ɗauko kuɗi ko?"
"A a baba ai ni yanzu zuwa zanyi ya bani in zauna in cii sai na gama na gudo" ta karisa maganar tana dariyar shekiyan ci.


"Uhmn uhmn mamana ba za'ayi haka ba bayan Allah ya bamu arzikin da za mu iya sayan rumfar ɗan litin ma gaba ki ɗaya sai kisa ya raina mu ai"
"Kuma hakane fa shikenan baba zan biya shi"
Zaro dubu Biyu yayi a aljihun sa yace "Ga wannan"

"A a baba barshi ina da kuɗi a jikina wanda ka bani da safe ban taba su ba"
"Toh shikenan Amma dan Allah mamana idan kika karbi abin sayarwa ki biya su idan baki da kuɗi kizo ki faɗa min duk kuɗaɗe na naki ne,ke kaɗaice Allah ya bani dan Allah ki rage wasu abubuwan da kikeyi" ya karasa maganar a sigar lallama.

"Kar ka damu Baba zan daina idan na girma" tana kainan ta arce da gudu yace "Ki na saya ki dawo gida" ba tare da ta tsaya ba tace
"a'a Baba sai na gama ci a chan yafi daɗi"
Girgiza kai yayi kana yace "Ko yaushe mariya zata girma?" yasa kai ya shige gida.


Tana zuwa rumfar me shayi tace "Ɗan liti a haɗa min shayi da madara,sannan a soya min kwai guda 5,ka sa madara yaji fa"
Kallon baki da hankali ya mata hannayen ta ta ɗaura a kugun ta tace "Bura uban nan ni kake yiwa kallon nan don kawai nace ka haɗa min shayi ,to ba kyauta zaka bani ba da kuɗina"

"Sau nawa kike zuwa sai kin gama ci ki gudu? Na gaji da asara saboda haka ba zan bayar ba"
"Kasan dai da kuɗina ko,kowa a garin nan yasan waye ubana,sai mu saye rumfar kan ma gaba ki ɗaya kai har ma da mutanen da ka tara a ciki"
"Ke mariya bana son iyayi ki tafi kibar nan kan na saba miki,duk ranar da kika zo nan sai kinyi min tijara kin kora min kwastoma"
Bakin zanin ta ta kwance ta ciro kuɗi yan dubu dubu,dubu 3 ta zaro ta mika masa haɗe da faɗin "Ungo nan,ka cire kuɗin da kake bina sannan ka haɗa min shayi me kauri idan kuɗin basu isa ba sai na kara maka"


Karba yayi yana washe baki "Ai ma sunyi yawa wannan ai harda indomie zan haɗa miki"
"Ni ban saka ba mallam akan me zaka ce zaka min abincin yara ni bana so shayi da bredi nace maka"
"Toh bari na haɗa miki"
"Na bari"
Ta koma daga gefe,bai daɗe ba ya haɗa mata ganin tana neman gun zama yace "Aaaaa ba gida zaki tafi ba?"
"Anan zanci ko kana da matsala da hakanne?"
"A a wane ni,kawai dai naga nan duk maxane idan kin koma gida zaki fi sake wa a chan"
"Ni anan nake son ci,kaai nifa bana son shishigi sai in fasa kuma ka biyani kuɗina"
"Aci lafiya"
Ta amsa da "Amiin" yayi saurin barin gun ya koma cikin rumfar.


Sai da ta gama cinyewa tasss tayi gyasa harda shafa tumbin ta maxan dake gun suna kallon ta suna magana kus kus, mikewa tayi ta mika masa kofi da plate ɗin ta tsaya kallon su tana son jin maganar da suke ai kuwa taji sunyi shiru,ta tintsire da dariya tace "Shegur Mariya ashe kananan marasa kunya ne ku ai da sai ku cigaba da gulmata wawaye kawai"

JINNUL KAMIL (A True Life Story Of Alisha)Where stories live. Discover now