Ciza leb'en tayi tana huci cikin tsananin 'bacin Rai Tace "Wai ni yau Hameed yake wa tsawa? Ba laifin kowa bane illa na Alisha , yau sai Naga gatan ki a gidan Nan" mikewa tayi ta shige d'akin tana kananun suratai ita kad'ai.Bangaren su Alisha kuwa bayan sun gama cin abinci suka zauna suna Kallo, Alisha ta Mike Tace "Granny Wallahi wanka nake son yi gashi Kuma babu kayan da Zan canza inna yi"
"A a akwai kayan Balki(Balki Yar Cousin din Hameed ne) inaga ai kayan ta zai miki tunda Jikin ku kusan d'ayane"" Eh zeyi duk da ma ta d'an fini cika"
Mikewa granny tayi Alisha Kuma a biye da ita suka shige cikin d'akin Granny, wardrobe d'inta ta nufa ta d'auka Kaya sun Kai kala biyar Tace "Duk nata ne tunda tazo ta manta su anan Kuma ta kasa zuwa ta d'auki tsummakaran ta"
Yar karamar dariya Alisha tayi Tace "Kai Granny ki dubi kayakin Nan fa sabbi ne Amma kike cewa tsummakarai......wani atamfa ta hango tasa hannu ta d'auka Tace "kiga wannan fa sabo ne kamar ma bata saka ba"Tab'e baki granny tayi Tace "Ku kuka sani Baku da aiki sai d'inke d'inken banza da na wafi Kuna cinye min kud'in Yara"
"kaai Granny ki duba kiga wardrobe d'inki fa acike makali ni Wallahi kayana Basu Kai naki ba Amma Kuma mune muke cinye miki kud'in yarana?"
"mtsww..... Alisha bakya magana Amma idan surutun ki ya tashi manta jiki kike Shiga kiyi wankan bari na koma parlor" tana Kai Nan tayi ficewar ta, girgiza Kai Alisha tayi ta shige ban d'aki.Ta ɗauki kusan mintuna goma kana ta fito daga wankan,Jin and fara Kiran sallar la'asar tayi saurin komawa ban ɗakin tayi alwala bayan ta gama ta fito,Man Granny da ta gani agaban Mirror ta ɗauka ta shafa kana ta ɗauki powder ta shafa sama sama, Waldrope ta nufa ta zaro hijab ta saka,kana shimfiɗa prayer Matt ta fara sallah,tana idar da sallah ta zauna don yin azkar, ta idar Kenan Granny da Nawal suka shigo,Suma alwalan sukayi,suka tada sallah,Bayan sun idar da sallan ne duk suka koma parlor,zaman su ke da wuya Fa'eez da Hisham suka shigo gidan da sallama. Nan suka cigaba da hirar su hankalin su kwance Amma Banda Alisha ta rasa dalilin da yasa take Jin Fad'uwar gaba,lokaci zuwa lokaci takan hango irin masifar da zata Sha agun mummy idan sun koma gida.
Tun da magrib daddy ya shigo unguwar su Amma ganin an fara Kiran sallah sai ya ratse masallaci Bayan an idar da sallan ne ya shigo gidan, kusan tare Papi, Fa'eez da Hisham suka shigo gidan.
Papi na ganin Murmushi ɗauke a fuskan sa, Yana faɗin "kaga manyan mutane" Hisham da gudu yayi tsalle Jikin sa yana "oyoyo papi"
Fa'eez ma da gudun sa yayi tsalle a Jikin papi har Saida ya kusa faɗiwa Fa'eez ɗin yayi saurin rike shi , Daddy tun Kan ya karaso inda suke cikin ɗaga murya Yana faɗin "Kai!! Kaai!! So kuke ku hallaka min shi?"Murmushi papi yayi yace "ina mamakin Fa'eez Wallahi shikam baya girma , jibi fa Kato dashi yazo Yana so ya karya Ni"
Fa'eez tamke fuska yayi yace "Nikam dama ai bana gwanin ta" Hannayen sa yasa a aljihun wandon sa ya shige cikin gida, ya tarar babu kowa a parlor, Kallo ya cigaba da yi har suka shigo.
Daddy yace "Kai Fa'eez Kai baka Isa a maka magana Bako sai ka nuna kafi kowa zuciya , ka kiyayi kanka da wannan mugun halin"
Papi ne yayi saurin fad'in "A'a bar shi kaji ai na mijine da zuciya a ka sanshi"Muryar granny suka tsinkayo tana faɗin "au ma a Haka zai nuna mazantakar tasa? Yaje filin daga Mana ai maza suna Chan a sambisa forest" dariya Papi yayi yace "Baki da dama hajiya"
Tace "to ai gaskiya ne,sannu da dawo wa"
Ya amsa da "Yauwa sannu"
Hannu tasa ta karb'i jakar dake hannun sa ,da niyar kai ɗaki Alisha ta karb'a ta ce "Bari na Sami ladar angona"
Yar ƙaramar dariya papi yayi yace "Ashe harda ke aka Zo"
Ta amsa da "Eh" ta nufi ɗakin tana ajiyewa ta dawo.
Yace "House Full"
Fa'eez yace "sunan wani film" babu wanda ya kulashi hakan ba karamin kara bata masa rai yayi ba.
YOU ARE READING
JINNUL KAMIL (A True Life Story Of Alisha)
HorrorJINNUL KAMIL Labari ne da ya faru a zahiri, kuma ya kunshi abubuwan dake faruwa yau da kullum tsakanin mutum da Aljan. labarin yana cike da abin tausayi, mugunta da zamantakewar iyali, harda sakaci irin na iyaye musamman Mata.Koda wasa ba'ayi laba...