"Da fatan Wannan abun baya nan ko?"
Cike da rashin fahimta Mummy take kallon ta tace "Wa kenan fa Aisha?""Hameed mana" ta faɗa da serious face.
"Mtsww bana son iskanci fa mijin nawane zaki cewa abu? Ke nifa duk lalaci ina son mijina"
Tabe baki tayi "Shirmen banza ina soyayya anan? Zanyi maganin ki ne" ta faɗi hakan a zuciyar ta a bayyane kuwa tace "Allah ya baki hakuri,dama na zo ne akan maganar da mukayi dake"
Gyara zama mummy tayi kana tace "Wace magana kenan fa?" ta maida hankalin ta akan chatting da take yi."Kan uba kaji min ƴar rainin hankali,bazan nuna miki true color na ba tukunna sai na gama dake tukunna...."
"Kinyi shiru?" mummy ta katse ta ƙirkirerrem murmushi tayi kana tace "sorry nayi mamaki da kika ce kin manta ne bayan kin san muhimmancin abun nan a gare ni"
Ajiye wayar tayi kana ta maida hankalin ta gare ta tace "Sorry ƙawata kin san abubuwan kaina dayawane wallahi yi hakuri ki ɗan tuna min"
"Uhmn dama maganar aron 5m da mukayi magana dake ne kin san ina so ne nima na tsaya da ƙafana ba aure ba ,ba aiki ba kuma ga rashin abin yi duk na kasa gane kaina wallahi"
Dafe goshi mummy tayi kana tace "Kaai afwan mtsww duk na sha'afa ne yanzun ya kike so cash ne ko transfer? Ko kuma muje banki mu cire miki?"
"A a kiyi min transfer ɗin dai"
"No case ki turo min da acct numb ɗin ki Via whatsapp,anjima zan tura miki in sha Allah"
"To qawata godiya nake"
"haba qawata ni ai mai baki kyautar 5m ne kawai dai kayana da har yanzu suke kan ruwa basu iso bane da na baki kyautan sa wallahi"
"Wai kina nufin haryanzu kayan nan basu sauka ba? Idan ban manta ba kusan 3 months kenan fa?" ta faɗa da tsananin mamaki a fuskarta."Wallahi kusan 4 months ma dai ke dai abun babu daɗi amma zan san abinyi"
"Allah ya rufa asiri,amma ni kina bani mamaki ace duk yawan kuɗin Abdul amma kina zaune nikam inda nice hmmm""Ban gane in da kece ba? Kuɗi kike so kuma na baki me kuma ya saura?"
"Ina mamaki ne kawai nasan dai Abdul idan ba a sa company dinsu a farko ba za'a sa na biyu karki manta fa Hameed agriculture limited kaɗai ma ya isa bare sauran kananun abubuwan da yake yi a gefe, Ba ma wannan ba shawara nake so na baki amma ina tsoro ban san ya zaki ɗauki maganar tawa ba"
"Ina sauraron ki"
Gyara zama tayi kana ta cigaba da faɗin "Me zai hana ki rika satan kuɗin sa daga asusun bankin sa?"
Waro ido mummy tayi tace "What kina da hankali kuwa Aisha? Me kike faɗine sata fa kika cewa nayi? Kuɗin Abdul kike so na sata to sabida me?"
"Haba halima me ne naga duk kin tada hankalin ki Abdul fa ake magana anan ba Wani ba kuma fa mijin kine,and ba don komai zakiyi hakan ba sai dai ki samu extra money for savings ba,by the way idan kika tara kuɗi dayawa ko ya rabu dake baki da wata matsala ta kuɗi"
"Mtswww shirme me zai sa Abdul ma ya rabu dani kar ki manta yana sona fa sosai so hakan ba mai yiwuwa bane"
"Uhmn na miji kike wa wannan shaidan ko? To bari kiji akwai mata dayawa da suka fiki da class da aji,kyau asali kai wanda suka fiki da komai da komai ma me zai hana bazai bisu ba kawai ƴammata kiyi amfani da daman ki tun kina da ita"Shiru tayi tana nazarin maganar Aishan, Aisha tace "Kinyi shiru babu wani tinani da zaki tsaya yi fa ƙawata,kawai ki ai watar"
"To amma idan ya gane fa"
"Ta ina zai gane? Kina transaction ɗin sai ki goge message ɗin ba shi kenan ba?"
"Amma ai zai iya zuwa ya cire bank statement kuma zai gane"
"Kamun a kai ga wannan matakin kin kwashi abinda zaki kwasa kinga daga nan nima ai zaki min ihsani ko?" ta karasa tana wani murmushi mai wuyan fassarawa.Dariya Mummy tayi tace "Allah ya shirya ki qawata" nan suka cigaba da hirar su.
"Da fatan Wannan abun baya nan ko?"
Cike da rashin fahimta Mummy take kallon ta tace "Wa kenan fa Aisha?"
YOU ARE READING
JINNUL KAMIL (A True Life Story Of Alisha)
HorrorJINNUL KAMIL Labari ne da ya faru a zahiri, kuma ya kunshi abubuwan dake faruwa yau da kullum tsakanin mutum da Aljan. labarin yana cike da abin tausayi, mugunta da zamantakewar iyali, harda sakaci irin na iyaye musamman Mata.Koda wasa ba'ayi laba...