Hiran su suke hankali kwnace,chan naji Mummy tace "Yauwa Rabi fa tace min zata zo amma haryanzu shiru"
Ta'be baki Aisha Tayi kana tace "Kin santa ai sarauniyar jiji da kai,ta nuna ta fi kowa sanin komai"Gigiza kai mummy tayi tace "wallahi ina mamaki yanda akayi baki son Rabi kwata kwata tunfa muna school fa ko dai ta kwace miki saurayine ban sani ba?" ta karasa maganar cikin tsigar zolaya.
"Eh mana ,kin manta ne nifa nace ina son jafar amma yarinyar nan taje suna soyayya abun har ya kai ga ta aure shi,gashi har yau Allah bai basu haihuwa ba" ni ko nace wato Rabi da ake magana akai tun ɗ'azu matar jafar ce? Abokin daddy muje zuwa.
Mummy Tace "Matar mutum kabarinsa fa akace miki,inda mijinkine wallahi da sai ya aure ki kuma haihuwar da kike magana akai ɗin ai Allah ke bayarwa ba mutum ba,ba a yiwa mutum gorin aure da haihuwa sabaida kamar yarda baki san ranar mutuwar ki ba haka suke"
"Idan na fahimce ki so kike ki gaya min magana sabida kunyi aure ni banyi aure ba?"Kama baki mummy tayi haɗe da faɗin "Niii rufa min asiri yaushe nace miki haka? And by the way rashin auren ki kece kika jawa kanki kintsaga rawar ido,ke sai me kaza sai me kaza ga irin ta nan ai"
Cike da takaici Aisha tace "Hmm yanzu fa kika gama faɗin cewar lokacine ba a yiwa mutum gori amma kuma kike min?"
"Ni ba gori na miki ba gaskiya ce kawai bakyaso,ohh ashe ba daɗi"
"Ba laifin ki bane laifi nane da na ɗauki ƙafata na zo inda kike" tana kai nan ta mike ta ɗauki jakar ta,miƙewa mummy tayi ta sauri ta rike ta "Haba qawata me yayi zafi kiyi hakuri dan Allah ni wallahi ba da wata manufa na faɗi hakan ba,yi hakuri ki zauna dan Allah"
Ba ta ce mata komai ba ta ajiye jakar ta zauna,Wani irin kallo take yiwa mummy wanda ita mummy hankalin ta na kan wayar ta, ciza leben ta Aisha tayi tace "Zanyi maganin kine"Sun ɗauki tsawon lokaci ko wacce na latsa wayar ta,babu abinda kake ji a ɗakin sai karan saukan AC da chewn da Mummy ke taunawa,turo kofar da akayine ya sa mummg ɗago kanta yayin da Aisha kuma ta ɗan waiga kasantuwar ta bawa mashigar office ɗin baya,Ganin Wacce ta shigo duk suka sakewa juna murmushi.
Aisha ce tayi saurin faɗin "Oyoyo friend" cike da mamaki baki a buɗe mummy ke kallon ta a ranta tace "Kamar ba itace take zagin ta yanzu ba ,Aisha halin ta sai ita" ganin kallon da take mata yayi yawane ta harereta haɗi da faɗin "Wannan kallon fa?"
Girgiza kai tayi tace "Allah ya kyauta" nan suka shiga gaishe gaishe, Rabi tace "Hope lafiya ko amina kike neme ni?"Kan mummy ta bata amsa charab aisha tace "Ina fa lafiya Hameed yayu yaji"
Cike da rashin fahimta tace "Bangane yayi yaji ba?"
"To ya bar mata gidan ko ince sun bar mata gidan........"
Nan dai ta zayyana mata abinda mummy ta faɗa mata,Rabi tace "kinga abinda nake gaya miki ko Haleema? Ki guji fushin me hakuri yanzu hakan ya gaji da abubuwan da kike masa ne ya bar miki gidan, na tabbata yanzu hankalin ki ba a kwance yake ba ,shi kansa nasan babu yanda zayyi ne sabida mijin ki na kaunar ki yana son ki kawia dai halayyar da kika canza ne baya so,amma kiyi wa kanki faɗa before ia too late,ki bishi ki bashi hakuri sannan na daɗe ina bin ki akan kije ki bawa hajiyar sa hakuri tunda dukkan mu mub san laifin kine ,yanzu da ace baki mata rashin kunya ba ai da kin bisu gidan kema kinga daganan dole ya sauko"Mummy tace "Nifa na gaya miki tun ba yau ba wallahi bazan bawa kowa hakuri ba wallahi,kar ta hakuran mana ita ta sani,kima br maganar bana so"
Aisha tace "Ai Mrs Jafar haka take, sai dai tayi tawa mutum wa'azi kamar wata malamar islamiya"Girgiza kai tayi in da sabo da saba da irin maganganun su ba halin tayi magana sai suce mata tana musu wa'azi ,idan taci sa'a su fahimce ta wataran kuma suyi chaaa akanta sai tayi shiru ta kyale su ta zuba musu na mujiya.
Mummy ta shiga tunani shin shawarar wa zaya ɗauka acikin shawarin kawayen nata? Zuciyar ta ta amince mata da Maganar Rabi amma kuma Aisha gaskiya ta faɗa hameed zai raina ta,a haka ta yanke shawarar baza ta sake neman shi ba har sai ya gaji don kansa ya neme ta.
YOU ARE READING
JINNUL KAMIL (A True Life Story Of Alisha)
HorrorJINNUL KAMIL Labari ne da ya faru a zahiri, kuma ya kunshi abubuwan dake faruwa yau da kullum tsakanin mutum da Aljan. labarin yana cike da abin tausayi, mugunta da zamantakewar iyali, harda sakaci irin na iyaye musamman Mata.Koda wasa ba'ayi laba...