Dukkannin Jikin su bari yake yi, Jamy ta ja da baya tana faɗin "Wallahi jini ne ta mutu,Inna lillahi wa'inna ilaihir raji'un" ta karisa maganar tana mai ɗale kan gadon ta,ta dafe kirji sai zazzaro ido take.
Alisha kuwa kasa motsi tayi sai matsar kwalla take,ta daɗe a tsaye a kanta kana tayi karfin Halin ɗaga skirt ɗin salman,Jini ta gani yana kan zuba,waigowa tayi ta hango Jamy a saman katifa ta rungume pillow,Alisha dariya ce ta so kufce mata amma ta matse tace "Jamy ki zo mana mu gyara mata jiki mu kaita school clinic"
Kara waro ido Jamy tayi tana faɗin "Wa? Ba dani ba nikam bazan taba gawa ba kika san me taje tayo ta zo ta mutu mana a ɗaki nikam bazan taba gawa ba wallahi""Dallah chan wa ya ce miki ta mutu? Tana fa numfashi dan Allah kizo mu tai maka mata"
Saukowa tayi tana faɗin "Dan Allah da gaske tana numfashi?"
"Eh wallahi zo ki ganewa kanki"
Tafiya take kamar kwai ya fashe a cikin ta,cikin sassarfa har ta isa gun su, ta daɗe tana kallon ta kana ta maida kallon ta ga Alisha tace "Yanzu me abin yi?""Taimaka min zakiyi na mu kaita ban ɗaki mu gyara ta"
"To mu ɗaga ta"
Dakyar da makyar kyasa Jamy ta rike ta ,sa'an su ɗaya Salma irin matan nan masu karamin ruwa kuma basu da jiki hakan shine ya basu damar ɗaga ta chak suka kaita ban ɗaki.Wasu abubuwa ne ta gani suna zubawa daga jikin ta bayan sun cire mata gajeren wandon dake jikin ta, Jamy kara tsorata tayi tace "Na sani dama za'a rina wallahi abortion tayi nikam bazan taimakawa karuwa ba"
"Subhannallah haba Jamy meyasa kike hakane kar ki manta fa kaddara ce kuma babu wanda ya isa ya tsallaka tashi kaddarar""Kaddara kaddara kaddara duk sanda wani mugun abu ya faru sai muce kaddara ce bayan mu muke ɗaura wa kanmu wahala,yanzu dan Allah ki duba kiga yanda yarinyar nan tunda muka zo ban taba ganin ta a cikin school da sunan lectures ba ina take zuwa? Ni da ke mun san abin da takeyi duk da cewar ance shi zato zunubi ne amma gaskiya ce a faɗe ta yarinyar nan bin maza take ga nan kuma shaida"
"Jamy ni daɗi na dake idan kika fara magana ba comma ba full stop, idan kina wani abun yanda kika san wacce bata san rayuwa ba,yanzu duk ba wannan ba dan Allah mu gyara ta idan kuma baza ki iya ba ki fita idan na gama sai ki shigo mu fitar da ita"
"Da yafi kam" tana faɗin haka ta juya ta fice daga ban ɗakin ta koma parlor ta zauna.
Jinin ya daina zuba sai kaɗan kaɗan,Alisha ta ɗauki kusan mintuna talatin tana gyara jikinta kasantuwar jinin dayawa gashi wasu sun bushe da alama tun safe ta fara bleeding ɗin.Bayan ta gama ta kira Jamy suka ɗaure mata jiki da towel kana suka fito, Alisha na hango kan katifar Salman yanda suka bari taje "haba Jamy na ɗauka zaki gyara mata kan katifar"
Tabe baki jamy tayi tace "Na faɗa miki bazan taba kayan kazantar nan ba wallahi ke da kika damu sai ki gyara mata"Ajiyar zuciya Alisha ta sauke ta girgiza kai tace "To mu ajiye ta anan" tana mata nuni da gadon Jamy.
"Tabɗi wallahi ba dai a gado na ba"
"To mu kaita nawa"
"Better"Nan suka kaita kan gadon Alishan suka kwantar da ita nan alisha ta shiga gyara kan katifar Salman, Zanin gadon da blanket ta kai ban ɗaki ta wanke su tass ta fita waje ta shanya su,kana ta koma ta buɗe locker ɗin salman ta ciro zanin gado ta shimfiɗe mata sai da ta gyara mata ko ina kamin ta ciro mata kaya ta ɗauko mata Gown mara nauyi da pant da bra ta dawo inda take ta shiga ta saka mata kayan.
Pad ta ɗauko a jakarta ta saka mata,sai da ta gama gyara ta saf tace "Jamy mu kaita asibiti"
"Nifa yanzu yunwa nake ji wallahi ki bari naci abinci tukunna""Haba jamy ni gaskiya ban sanki da haka ba meyasa kike hakane kar ki manta fa ƴar uwar kice"
"Allah ya tsare ni wallahi ni kam ba ƴar uwa ta bace"
"Ko kin ki ko kin so musulunci ya haɗa ke ƴar uwar tace wallahi jamy idan yarinyar nan ta mutu to kema da sa hannun ki"
YOU ARE READING
JINNUL KAMIL (A True Life Story Of Alisha)
HorrorJINNUL KAMIL Labari ne da ya faru a zahiri, kuma ya kunshi abubuwan dake faruwa yau da kullum tsakanin mutum da Aljan. labarin yana cike da abin tausayi, mugunta da zamantakewar iyali, harda sakaci irin na iyaye musamman Mata.Koda wasa ba'ayi laba...