#DANDANO

129 5 1
                                    

#Family
#Love and Romance
#hate
#fate and Rape


Dandano

Yana gaban mirror dressing yana shafa kalar turarrukan da yake using,tana tsaye a bakin wardrobe tana Ciro kalar mayafin da sukayi shige da kayan jikinta,yana gamawa ya nufi kofa batareda ya kalli inda take ba.muryarta na mugun Rawa take fadin."Yaya Rafeeq ba tare zamu tafi wurin kamun ba.?"Ya juyo yana kallonta da rashin fara'a cikin fuskarsa yake faɗin."ki zauna gida babu inda zaki fita,da sauri ta katsesa tana jin wani sabon kuka yana zo mata,nafa tambayeka tun jiya kace yau zamu fita a tare meyasa ka canja."ta faɗa hawayenta na sauka cikin fuskarta wanda bata damu data goge ba,dan Runtse ido yayi yana jin wani iri acikin zuciyarsa idan akwai abunda yafi tsana a duniyar nan ba baifi yarda hawaye ke zuba cikin fuskarta ba,Yana mugun fushi da kadddarar da ta kawo su stage din da bai taɓa tunanin zasu zoba,cikin shesshekar kuka take faɗin bikin yaya Moobarak fane ?"ta faɗa hawayen idanunta na kasa tsayawa....bana son yawan jan magana,kin san naci na ɗaya daga cikin abunda nafi tsana.

"Meyasa baka son nayi zumunci da yan uwana tunda na Aureka Yaya RAFEEQ idan kai ka katse zumunci na ni dakai su yayan uwannane fa?"daman saboda daddy ka yarda ka Aureni."a tunani na tun bayan abunda ya faru dani da kaddarar da ta hau kaina,Ban taba tunanin zanyi aure anan kusa ba."da ka bijirowa Daddy da zancen Aurenmu na zata kaunarmu tasa kayi haka,na zata zaka binne wannan sirrin har abada har jikokin mu da yayamu zaka karbeni a duk yadda nake,ashe ba haka bane Yayaa?"meyasa ka Aureni kasan bazaka iya jure zama Dani a nakkasar da nake tare daita.tamkar an kafa Rafeeq gwarzo a wajen
Idan ya cigaba da tsayuwa a wajen komai zai iya faruwa,da sassarfa ya fice daga parlorn.hade kansa yayi jikin motar wasu hawaye Masu zafi na sauka akan fuskarsa yana jin Wayarsa na Ringing ya kasa cirota daga cikin aljihunsa baranta na yasan wanda ke kiran nasa.

Sosai Ruwan saman da ake yake sauka akanta
Shigowarsa kenan cikin gidan ya hangota tsaye ruwan sama na dukanta
Sai wani kankame jikinta
Take ,bazai iya cewa karfe nawa ba a lokacin yasan goma na dare har ta wuce,da sassarfa ya Nufeta ruwan na Dukansu.hannunta ya shiga ja ta fisge a tsawace yake faɗin."Meye haka maimoon sai wani ciwon ya kamaki meyasa zaki tsaya cikin ruwan sama."Ya faɗa yana jin numfashinsa na dan fisga duk da akwai Kayan sanyi ajikinsa,Amman ruwan yakeji suna tabasa suna shiga jikinsa saboda lalurarsa.
Ka tafi Yaya rafeeq kabarni anan karka yiwa kanka illah."Ta faɗa hawaye na Rolling cikin fuskarta.idan bazaka iya haɗa gado Dani ba kayi Aure yaya Rafeeq ta faɗa tana girgiza ƙafadarsa,
Nima nasa daudar dake manne Dani kawai zata cutar dakai ko kaɗan ban taba ganin laifinka ba ban taɓa ganin laifinka ba yaya,ta faɗa tana fadawa jikinsa tana fashe masa da wani kuka mai sosai rai.dan lumshe ido yayi zuciyarsa na mugun bugawa ga wani sabon ciwo da yake jin yana shiga a hankali.

RafeeqWhere stories live. Discover now