*RAFEEQ* 12

23 1 0
                                    


*PAID BOOK#400*

NA

*_ASMY B ALIYU_*
DA
*_HAJJA CE_*

TEAM TAGWAYE.....

12...

"Menene kike so a wajan shi har kike damuwa akan shi?" Tambayar daya jefo mata kenan wanda tasa ta yin murmushi a karan farko tun shigowarta parlorn. Hannunta tasa tare da riƙo nashi a hankali ta zaunar dashi kan soofa tana sake yin murmushi. "Yaya Wahaab fa shine dai-dai ni, saboda yana da hakuri yana shanye duk wani laifi da zanyi masa, ko a Islamiya malamai na cewa miji mai shanye fushin matarsa abun so da tinƙaho ne." Kallonsa take da wani irin rikici da take hangowa acikin idanunsa, tasha jin yadda familyn Gwarzo ke faɗar rikicin Yaya Rafeeq da rigimarsa babu mai irinta. "Zanje naga Zainab kar abarta ita ɗaya." Ta faɗa tana ƙoƙarin miqewa tsaye dan bazata iya tarar rigimarsa a wannan lokacin ba. Har ta fice daga cikin parlon ya kasa motsawa. Lokaci ɗaya kuma ya fashe da wata irin dariya yana girgiza kansa, bai san girman kansa da miskilancinsa ya girmama har haka ba, sai yanzu da ya kasa faɗawa Maimoon Gwarzo Gaskiyar soyayyarta dake wahalar dashi. Soyayyar tace ta kawo shi wannan stage ɗin da ko a mafarki bai taɓa hasasowa kansa hakan ba, yarinyyar da aka haifa a gaban idanunsa ce ya kasa faɗa mata cewa yana sonta, ya kasa furta mata cewa itace muradin zuciyarsa. Bai taɓa tunanin zai rasa kwarin gwiwarsa a gabanta ba, maganganun Moobarak Gwarzo yaji suna dawowa cikin kansa lokaci ɗaya inda yake cewa. "Ban san kalarka ba Yaya, da gaske ban taɓa ganin mai irin miskilancinka ba. Irin wannan miskilancin naka zai iya zama matsala acikin rayuwarka, bana fatan hakan. Please ina so ka canza ka dawo yadda kowa yake rayuwarsa." Da wani irin kallo yake bin Moobarak Gwarzo. "So kake naje na hau titi na ɗauki microphone ina baiwa mutane labari ko? ai yin hakan da zanyi shine karshen surutu." Moobarak zai yi magana Rafeeq ya nuna masa kofa yana faɗin. "Ka fita... ka fita karka sakamin ciwon kai da yamman nan." Fita kawai Moobarak yayi yana rufo masa ƙofar. Hannyensa ya shiga kallo yana sakin murmushin da bai da alaka da farin ciki ko kaɗan, gashi a gabanta ya kasa bayyana abinda ke cikin zuciyarsa, bai san meyasa ganinta ke karya masa zuciya ba. Bai san meyasa ko ya buɗe baki da nufin yayi mata maganar ba sai yaji tayi masa wani irin kwarjini ba. Dariya yayi idan da wani ne ya faɗa masa Maimoon Gwarzo nayi masa kwarjini bazai yadda ba. A haka Zeeeee ta gama ganin lefen da murmushi a fuskarta take kallon Maimoon ɗin wacce tana fitowa wajen Rafeeq ɗakin ta shigo kai tsaye. "Allah ya sanya alkairi sis ya nuna mana lokaci lafiya." Da wide smile akan fuskar Maimoon take faɗawa Zeeeee ɗin ta gode, ta lura da yadda Zeeeee ɗin takeda saurin sabo da mutane, kuma a ɗan zaman da tayi na mintuna a tsakanin su ta lura Zeeeee ɗin bata da wata matsala, amman bata san meyasa wani ɓangaren na zuciyarta take jin sam batayi mata ba, haka kuma da gaske bata son Rafeeq Gwarzo ya aureta har aranta tafi hango soyayyarsa da Haneefa fiye da Zainab ɗin. Anan Zainab ɗin ta faɗa mata tana son ta shiga toilet. Batareda tunanin komai ba suka koma ɗakin Maimoon ta nuna mata ƙofar toilet ɗin, sai da Zainab ɗin ta shiga tayi tunanin kawo mata ruwan sha ganin tun da ta shigo basu bata koda ruwan sha ba ne bayan kuma wannan ba halayyar familyn Gwarzo bane na rashin daraja baki. Fita tayi dan kawo mata ruwan, koda ta fito ganin Maimoon bata cikin ɗakin yasa da sauri ta buɗe handbag ɗin ta, sannan zuciyarta ta riga ta faɗa mata nan ne ɗakin Maimoon ɗin ganin pictures ɗin ta manne a bangon ɗakin. Ƴar ƙaramar Camera ta fitar tana juyata a hannunta wannan shine plan ɗin ta na farko akan alaƙar dake tsakanin Rafeeq da Maimoon. A gaggauce take duba ko wace kusurwa ta cikin room ɗin wanda ta tabbata duk inda ta sakata zata riƙa ɗaukar mata record ɗin komai, Idan tunaninta yazo a lissafi yanzu baifi sauran sati biyu ba bikin Maimoon Gwarzo, ta wajen ac taje ta makala na'urar da sauri ta sauko jin ana ƙoƙarin buɗe ɗakin yasa ta zauna gefen bed gabanta na mugun faduwa. Da murmushi Maimoon ta aje mata ruwan sha da kuma Cup cake mai chocolate. Ruwan kawai Zainab tasha tace mata ta gode ta miƙe tsaye ta ɗauki handbag ɗinta, har ɓangaren Aunty Maimoon ta rakata tayi mata sai anjima anan kuma Zainab ta karbi lambar Maimoon ɗin tace mata ta turo mata da anko idan sun fitar. Tun lokacin da Aunty ta faɗawa Yakumbo Zainab budurwar Rafeeq ce komai dake cikin kan Haneefa ya kwance. Yakumbo taɓe baki tayi tana faɗin. "Oh matan yanzu sam babu kunya a tare da su, to yanzu meye na wani biyo shi har gidan? kunya tamkar Aunty zata nutse da sauri ta faɗawa Yakumbo ai ba wurinsa tazo ba, ana faɗar haka Haneefa ta shige toilet bata sake fitowa ba har sukabar ɗakin. Suna fitowa cikin compound Zainab ta kira wayar Rafeeq, yana ɗagawa ta faɗa masa gata ta fito, murya can ƙasa ya faɗa mata yana zuwa. Ba'a jima ba suka hango Rafeeq ɗin yana tahowa inda Zainab tayi parking motarta har lokacin suna tsaye da Maimoon, daga Zainab har Maimoon kallonsa suke har ya qaraso wajensu, batareda ya kalli Maimoon ba ya buɗewa Zeeeee ɓangaren driver, ɗan sanyi taji aranta ganin yadda ya girmamata a gaban Maimoon Gwarzo. Tana kallonsa take faɗin. "Da yamma ka shigo muyi magana." Ɗaga mata kai yayi ta kalli Maimoon tana yi mata godiya. Murmushi kurum Maimoon ɗin tayi mata dukansu suna a tsaye har motarta ta fita daga gidan. Juyawa Rafeeq yayi ya nufi ɓangarensu batareda ya kalli Maimoon ba. Shi kuwa har addu'a ya rinqayi Allah yasa ta biyoshi sai dai har yayi nisa baiji ta biyo shi ɗin ba tamkar yadda yake tsammani. Batayi mamakin ganin Haneefa a ɗakin ta ba sai dai yadda taga idanunta sunyi ja alamar tayi kuka yasa ta karaso da tashin hankali a muryarta take faɗin. "Hanee meya faru? keda waye?" Cikin rawar murya Haneefa ke faɗin. "Ki faɗa min gaskiya Maimoon da gaske Zainab budurwar Rafeeq ce?" Ɗagawa Haneefa kai kurum tayi alamar ehhhh. Wani irin kuka mai ciwo Haneefa ta fashe dashi tana jin yadda wutar kishi ke rura cikin zuciyarta, Maimoon kam bata da zabi illah na jawo ƴar uwartata jikinta bata san kalmomin da zatayi amfani dasu wajen rarrashinta ba. "Nima a haka na tarar dasu tare Hanee, kuma wallahi nima ba son Zainab ɗin nan nake ba, Amman na kula daga Aunty har Yaya Shaheed duka suna son Zainab ɗin tareda Yaya Rafeeq. Ni dai bana sonta ganin farko bata yi min ba ko kaɗan dan ba kalarsa ba ce, duk da har yanzu na kasa yadda dashi ɗin yana sonta kin san halinsa wani irin bahagon mutum ne. Ki cigaba kawai da lallaɓashi kina haɗashi da Allah wata kila hankalinsa ya dawo kanki nima ban san ya zanyi da Yaya Rafeeq ba Haneefa idan nace miki halinsa baya damuna nayi maki karya. Zan tayaki neman soyayyarsa." Dakyar ta samu ta lallaɓa Haneefa ɗin. Da magrib tana zaune a ɗakin ta kan sallaya tana azkar taji shigowar sako wayarta, tana dubawa taga Abdul-wahaab ne. Da sauri ta shiga dubawa dan ba ƙaramin kewarsa tayi ba. "Ki fito gani cikin compound." Wani irin sanyi taji har acikin ranta, a parlor suka haɗu da Aunty wacce ke kai da kawo daga kitchen zuwa parlor dan har lokacin daddy bai shigo ba, ta faɗa mata Abdul-wahaab ne yazo zataje wajan shi, Aunty tace ta gaishe shi. Farin yadi ne ajikiinsa fari sol wanda baida zane ko kaɗan, kansa babu hula tun kafin ta isa wajensa taji ƙamshin Collections ɗinsa na cika mata hanci. Da murmushi a fuskarta ta gaishesa tana kallon yanayinsa, ya amsa batareda ya kalleta ba, tasan har yanzu fushi yake da ita. Cikin sanyin murya take faɗa masa su qarasa parlon baki, ya girgiza kai yana kallon agogon dake kwance acikin damtsen hannunsa yake faɗin. "Nan ma is okay ba jimawa zanyi ba wucewa zanyi." Yadda yayi maganar sai taji duk babu daɗi da alamar har lokacin ransa a ɓace yake. Ta shagwaɓe fuska cike da rigima take faɗin. "Kawai kace baka da lokaci na shine kawai, gashi nan tun kafin ayi auren ka fara yi min wulakanci, ka fara nuna min halinku na maza." Ta karasa maganar da rikici a muryarta. Runtse ido yayi yana jin kalamanta na taɓa sa, ya buɗe ido yana kallon kyakkyawar fuskarta. "Kin san kinyi min laifi ko? meyasa Maimoon?" Ya faɗa da damuwa a saman fuskarshi. Ta girgiza kai tana faɗin. "Motar haya na shigo ba tare muka zo Kano ba." Yanayin yadda take maganar ya gano gaskiya take faɗa masa. "Muje daga ciki muyi magana kafafuna sun fara yin sanyi kasan kuma bana iya jure tsayuwa.
Bai yi musu ba suka jera suka nufi entrance ɗin shiga gidan. Suna tareda Abdul-wahaab sako ya shigo wayarta kuma saqon daga Rageeq ne. "Ki haɗo min coffee, idan kinzo ki ajemin a parlor karki shigo min ɗaki." Murmushi ta tsinci kanta da yi, saqo itama ta turawa Haneefa akan ta haɗawa Yaya Rafeeq coffee kuma kar ta saka sugar da yawa dan tasan baya shiri da zaki. Kiranta tayi tace ta duba wayarta ta turo mata saƙo yanzu dan batason tayi maganar Rafeeq ɗin a gaban Abdul-wahaab dan bata son ƙara ɓata ransa. Tamkar a mafarki ta shiga duba saqon Maimoon ɗin. Kan gado take a kwance amma  bata san lokacin da ta sauko da kafafunta kasa ba, wani iri farin ciki ta tsinci kanta aciki ba tareda dogon tunani ba kai tsaye kitchen ta nufa cikin mintinan da basu gaza goma ba ta haɗa masa coffee ɗin, doguwar riga ce ajikinta da ɗan ƙaramin mayafin da tayi rolling kanta dashi. Babu kowa a parlorn nasu sai karar Ac. Kai tsaye stairs ta nufa zuwa ɗakunan baccinsu. Kai tsaye ɗakin Rafeeq ɗin ta nufa, aje tray ɗin hannunta tayi ta tura ƙofar, jin ƙarar buɗe ƙofa yasa ya ɗago yana kallon ƙofar duk a tunaninsa Shaheed ne. Tun da ya dawo daga sallar magrib yake kwance a ɗakin, ido biyu yayi da Haneefa dake yi masa wani irin murmushi lokaci ɗaya gabansa ya faɗi aransa yake faɗin Moon ta raina masa wayo. Wato yasa ta kawo masa abu Shine zata bawa wata aikin saboda shi bai isa da ita ba ko? lallai ta raina shi da yawa, wai a hakan ma bai fallasa mata sirrin zuciyarsa ba yasan kila da rainin da zata yi masa ya yi yawa. Haneefa kuwa tunda ta kalleshi taji gabaki ɗaya tana neman rasa nutsuwarta, kirjinta ya shiga bugawa wata irin soyayyarsa tana sake mannewa a cikin ranta. Addu'a ta farayi Allah ubangiji ya bata Rafeeq koda kuwa baya santa ita zata iya zama dashi a duk yadda yake. Laptop ɗinsa ya sake janyowa yana cewa. "Ita wacce nasa aikin tafi karfin tayi min sai ta saki? Ko ban isa da ita ba?" Yai maganar da murya marar sauti wacce ke nuni da ɓacin ran abinda Maimoon tayi masa. Haneefa ta kalleshi karo na biyu da dara-daran idanunta bakinta yana ɗan rawa take cewa. "Ba haka bane Yaya Rafeeq, bako tayi shine dalilin da yasa tace na kawo maka." A firgice ya tashi zaune yana kallon Haneefa zuciyarsa na bugawa yake cewa. "Waye bakon?" Tayi mamakin yadda taji muryarsa a kaurare, tsawa ya daka mata yana sake tambayarta. "Bakya ji ne?" Cikin firgici tace. "Wanda zata aura." Kamar zai fashe saboda bakin ciki ya buga mata wata tsawar. "Get out." Haneefa ta fara murza idanuwa zata saki kuka ya kalleta ganin bata tafi ba, ganin yanayinta yasa shi tunowa da Yakumbo yasan idan ya bari ta fita a haka yanzu zata zo ta sauke masa kwandon rashin mutunci, duk da zuciyarsa na wajan Maimoon da Abdul-Wahaab hakan bai hanashi controlling nutsuwarsa ba yace. "Ku me yasa idan kuna tare da wasu bakwa bawae  mutanen da suke tare daku muhimmanci? Ke a ganinki abinda tayi min ta kyauta? Ta nunawa wani banza can cewa ni ban isa da ita ba ko? Yayi kyau tafi sai da safe." Haneefa ta buɗe baki zatai magana taga ya sakko daga bed ɗin ya shige toilet da alama baya san wani surutu. Babu yadda zatayi dole ta juya tana jin kamar laifin nata ne ita kadai tunda itace ta kawo coffee ɗin......

ƳAN TAGWAYE BIYAR 2023

ƘASAITATTUN LABARAI MASU DAƊI DA SANYA NISHAƊI, SABON SALO MAI ƊAUKE DA DARRUSA NA RAYUWA UWA UBA ƘASAITATTUN SOYAYYA MAI HUDA JIJIYA.

IYALINA (A'ILATY)
RAFEEQ
MUNƊO
ZAMANIN MU AYAU
FATHIYYA.

  DOMIN SIYAR GUDA BIYAR N1500.

DOMIN SIYAR DAYA N400.

Account Details
2083371244
Zenith Bank
Aisha m salis

Ga MUTANEN MU NA NIGER 🇳🇪

Tura ta Nita
Da sunan

Asma'u Buhari Aliyu
08086207764

SAI KI/KA IS TURA SHAIDAR BIYA TA DAYA DAGA CIKIN NUMBOBIN NAN.

+234 808 620 7764
07065283730
+234 705 124 4211
+234 704 040 2435

#ASMY B ALIYU
#HAJJA CE
#Rafeeq gwarzo
#Abdul-wahaab
#Haneefa
#Zeee
#maimoon gwarzo

RafeeqWhere stories live. Discover now