*RAFEEQ* 9

34 2 1
                                    


*PAID BOOK#400*

Na

_*ASMY B ALIYU*_
DA
_*HAJJA CE*_👈

9...

Cike da murnar hangoshi suka ƙarasa wajan da yake, sama-sama suka gaisa da Aysha kafin ta nufi hostel dama kuma can jininsu bai wani haɗu da Rafeeq ɗin ba. A tunanin Ayshaa yana cikin mutanen da suka kasance masu mugun ji da kai da wani irin faɗin ran tsiya, wanda idan aka gaisheshi ma dakyar yake iya amsawa mutane babu walwala acikin fuskarsa. Saɓanin Yaya Shaheed da suke wasa da dariya idan ya kawowa Maimoon ɗin ziyara a yawancin lokutta. Ayshaa na wucewa Maimoon ta buɗe gaban motar ta shiga tare da saka hannunta ta rufe motar, bata kalleshi ba tunda ta shiga, hannu kawai ta saka tare da rage sanyin ac motar sannan ta kallesa tana faɗin. "Yaya wannan sanyin ai ya yiwa jikin ka yawa sosai, wai bakaji me likita ya faɗa maka ba ne?" Rafeeq ya share yaki kula maganar da take yi masa, cikin takaici yake cewa. "Please Moon idan zaki zo wajena ki rinƙa zuwa ke ɗaya bana son wannan ƙawar taki tayi ta bin ko'ina na jikin mutum da ido tamkar wata mayya." Ya faɗa mata so pissed up a muryarsa. Maimoon ta langabe kai tana kallon cikin fuskarsa ganin yadda yake wani haɗe rai. A hankali ta kamo hannunsa batareda tunanin komai ba ta riqe cikin nata hannun. Wani irin shock yaji lokaci ɗaya tun daga tsakiyyar kansa har cikin tafin ƙafarsa. Muryarta mai sake rikita masa lissafi yaji tana masa magana. "Yaya ko dai ko dai?" Cewar Maimoon fuskarta ɗauke da fara'a tana son tabbatar da zargin zuciyarta. Da sauri ya kalleta yana wani ƙara haɗe rai tamkar ba'a taɓa halittar dariya acikin fuskarsa ba. Murmushi Maimoon tayi wanda ya kusan narkar da zuciyar Rafeeq Gwarzo. Hannunta ta saka taja gefen kuncinsa fuskantar ɗauke da murmushi tana son jin amsa lokaci ɗaya kuma ta ɗage masa gira, da farin ciki a muryar ta take magana. "Kodai kana son Ayshaa ne Yaya Rafeeq? Naga duk lokacin da kuka haɗu sai ka samu abunda ka kushe a tattare da ita. Kasanfa Yaya a wani ɓangaren ana fara soyayya da tsana da hantara kafin ta rikiɗe zuwa wata irin soyayya mai ban mamaki da burgewa, irin wannan soyayyar Yaya Rafeeq tana burgeni sosai, saboda na sha karanta irinta a novels ɗin Hausa da na Turanci.  Kasan taya soyayyar mu nida Wahaab ta fa?" Saurin katseta ya yi tare da fisge hannunsa daga cikin nata, lokaci ɗaya ya kwantar da kansa cikin seat yana sauke wani irin numfashi mai matukar zafi. Haka kuma numfashinsa yaji yana wani irin sexing, gabaki ɗaya hirarta zafi take ƙara masa, wato ita bama soyayyarsa akanta take ganowa ba, wasu daban itace a ranta. Ganin haka yasa hankalin Maimoon ɗin ya ɗan tashi, hannunta duka biyu ta ɗora akan kirjinsa dake wani irin dokawa ta shiga dannawa tana faɗin. "Innalillahi Yaya breath! breath please." Haka take ta maimata masa kirjinta yana bugawa tana tsoran kar wani abun ya sameshi. Lumshe ido ya yi a hankali har na kusan minti biyu sannan ya samu numfashinsa ya dawo normal ya buɗe fararen idanunsa masu cike da kaunarta da suka fara canja kala suna kuma ƙanƙancewa yake faɗin. "Daga zuwa na babu wani gaisuwa kin fara min zancen da ban tambaye ki ba. Ya kike ya test ɗin? kun gama ne?" Sai da ta ɗan turo baki tana haɗe rai kafin tai magana. "Mun gama koda ka kirani muna class muna yi." Ta faɗa tana jan dogayen pingers ɗin ta. Satar kallonta yayi ta yadda ko ita ba zata gane yana kallanta ba. "Yaushe zaki koma Kano? ba yau bako?" Ta girgiza kai tana faɗin. "Eh ba yau ba Yaya saboda akwai abinda zan ƙarasa zuwa anjima, sai dai zuwa gobe idan Allah ya kaimu." Ɗan shiru ya yi yana faɗin. "Okay zan jiraki zuwa goben sai mu wuce, yanzu zanje na kama hotel Dan ko breakfast ban yi ba yunwa nake ji." Ya faɗa yana kallonta da idanuwanshi da suke ɗauke da wasu sinadarai da kowace mace zata so ganin hubby ɗinta dashi. Wani abu taji yana tsaya mata arai, wani haushi ne ya kamata, akan me Yaya Rafeeq zai jirata har zuwa gobe? Yanzu ya zata yi da Abdul-Wahaab wanda sun riga sun gama tsara cewa gobe zasu tafi tare? yanzu ma haka yana Kaduna gobe zai zo ya ɗauke ta, me zata faɗa masa? Idan kuma ta faɗa masa cewa Rafeeq Gwarzo ne yazo ya ɗauke ta Allah kaɗai yasan irin rikicin da zata ɓallo. Idan kuma ta faɗawa Yaya Rafeeq cewa zata koma tare da Wahaab tasan halin zuciyarsa kuma ciwonsa ma na iya tashi akan hakan saboda abu kaɗan zai ɓata masa rai ciwonsa ya tashi, shi yasa duk familyn Gwarzo ke lallaɓasa, babu wanda baya lallaɓashi kan lalurarsa. "Nima yunwa nake ji Yaya." Ya taɓe baki yana faɗin. "Muje ki rakani na kama ɗaki daga nan sai nayi mana ordern abincin da zamuci." Yai maganar yana ɗagowa daga seat da ya jingina bayansa. "Okay tom ka jirani naje na yiwa Ayshaa sallama sai na nazo mu tafi." Bai ce komai ba amma yanayin fuskarsa ya sake canzawa ta fice daga motar tana murmushi ƙasa-ƙasa dan tasan sunan Ayshaa da ta kira ne ya canza shi. Baki Ayshaa ta buɗe tana kallon Maimoon Gwarzo tana ganin yadda take sakewa Rafeeq Gwarzo jiki tamkar abun ya yi yawa. Aysha ta zauna bakin bed tana kallon Maimoon ɗin da ta ɗauki handbag ɗinta tana cewa. "Wai da gaske binsa zaki yi har hotel? Haba Maimoon ke bakya jin wani iri a ce kinje hotel? Rafeeq bafa muharamminki bane kamar su Yaya Shaheed ya kamata ki dinga tunawa da wannan." Da wani irin mamaki cikin fuskar Maimoon take kallon Ayshaa ɗin tamkar bata fahimci me take faɗa ba. Ɗan murmushi Maimoon ɗin tayi tana faɗin. "Har yau da sauranki baki gama sanin waye Yaya Rafeeq Gwarzo a wajena ba, da gaske babu abunda zai faru ko ɗaki ɗaya zan iya kwana tare dashi saboda Yayana ne babu abunda zai faru da mu na rashin da cewa. Ke baki san har wanka ya yi min lokacin da ina ƙarama ba Ayshaa? So ki daina yi masa irin wannan fassarar dan Allah bana jin daɗi, sannan yana da tsantseni  shigewa mace ba ɗabi'arsa ba ce ba." Daga haka Maimoon ɗin ta fice daga room ɗin ba tare da ta yiwa Ayshaa sallama ba. Baki a sake Ayshaa take kallon Maimoon ɗin har ta fice. Kai tsaye mota ta buɗe ta shiga zuciyarta na ɗan yi mata zafi saboda maganganun Ayshaa akan wannan fitar da zata yi da Rafeeq mutumin da har a jikinsa zata iya yin bacci ba tare da fargabar zai cutar da ita ko kanshi ba. Duk da yaga a yanayin da ta dawo hakan baisa ya tambayeta dalilin sauyawar fuskarta ba yaja mota suka tafi. Cikin gari suka shiga ya kama hotel anan ya yi musu order breakfast, tare sukaci abincin anan kuma ta ɗakko masa hirar Haneefa wacce ta kirata tace sun shigo Kano amma bata gari kuma ni nasan ba saboda kawo lefe na Haneefa ta wanko ƙafa tazo gidan ba, Yaya Rafeeq saboda kai tazo." Cikin rashin damuwa yana sipping tea ɗinsa yake magana. "Oh ai nima saboda ita na bar Kano nazo nan." Dariya Maimoon tayi wacce tayi mata matuqar kyau da yasa Rafeeq ɗauke kai tana buɗe hannuwa take faɗin. "Toh saboda me Yaya?" Ya yatsina fuska yana faɗin. "Tana sakani ciwon kai ne bata gajia da surutu, komai nata bata yinsa da aji ina son mace mai class." Maimoon ta juya ido tana faɗin. "Saboda kai kasan kana da class ba? Aini da Haneefa ta daina kulaka kana wani yarfa ta. Hmmm Yaya Rafeeq zanso naga matar aurenka wallahi dan nasan akwai kallo, za a ga iyayi. Zai buɗe baki yayi magana wayarta ta fara ringing, Abdul-wahab ne mai kiran ta manta ya kirata bata kira ba tun kafin su fito daga class. Wani zufa ta shiga haɗawa na rashin dalili tana jin yadda zuciyarta ke wani irin bugawa saboda rashin kyautawa da tayi. Rafeeq kuwa kallanta kawai yake yana ganin yadda take faman kallon screen ɗin wayar, ganin ta kasa ɗagawa yasa shi jan dogon hancinsa yana faɗin. "Wayake kiranki?" Cike da shagwaɓa tana turo baki tana haɗe girarta take cewa. "Wahaab ne." Nan da nan Rafeeq ya haɗe rai. "Toh me yasa bazaki ɗaga ba?" Maimoon ta ɗago tana kallansa sukai ido hudu, saurin janye nata tayi tana sake shagwaɓa fuska da wata irin murya take cewa "Laifi nayi masa kuma bansan me zance ba yanzun." Wayar ta katse aka sake kira. Rafeeq ya kasa cewa komai saboda takaicinsu, rai a haɗe yace. "Ki ɗaga wayar nan karar ta dameni kuma kisa a hands-free." Zaro masa dararan idanunta tayi masu kama da farin kindirmo wanda baƙar kwayar dake tsakiya wacce ta sake ƙawata idanuwanta suka ƙara ƙawata muhibbatar, ganin yadda yake wani haɗe rai ne yasa ta sunkuyar da kanta tana faɗin. "Yaya sirrin mu nida mijina zaka ji? Ni dai a'a uhm." Ta ƙarasa maganar cike da shagwaɓa har tana jujjuya kai side by side. A wani irin haukace ya kalleta jin ta ambaci Wahaab a matsayin mijinta, wani irin mugun kishi ya taso masa cike da tsawa yake cewa. "Ki ɗaga kona fasa wayar." Kamar zatai kuka dan ba ta gama shirya amsa tambatoyin da Wahaab ɗin zai mata ba, cike da rigima a muryarta take amsa masa bayan ta sanya hands-free ɗin. "Na'am... A'a Honey lokacin fa muna test..." Daga can Wahaab yake faɗin. "Amma da kuka fito me yasa baki kirani ba? Kinsan yadda hankali na ya tashi kuwa?" Kamar yana gabanta haka take buɗe idanuwa tana sake shagwaɓewa abin da yake ƙara hautsina Rafeeq kenan da yake ta faman danne zuciyarsa dan kar yaje ya yi a binda bai kamata ba. "Kayi hakuri abubuwa ne suka hau kaina na manta." Wahaab dake tuƙi yace. "Tun yanzu abubuwa sun fara yi miki yawa ina ga kuma an fara hidimar biki sweetie? kice wayar ma bazamu samu damar yin ta ba ko?" Murmushi ta saki wanda yasa Rafeeq saurin miƙewa tsaye, gurin ya bari dan idan yaci gaba da zama yana jin muryar ƙaton can zuciyarsa zata iya bugawa. Gurin motarsa ya nufa yana zuwa buɗewa yai ya zauna ba tare da ya rufe murfin ba, kansa ya ɗora a jikin sitiyari yana rintsa ido. "Anya ban yi wauta ba na ƙin sanarwa Maimoon halin da nake ciki a kanta ba?" Ya tambayi zuciyarsa dake yi masa wani zafi da raɗaɗi. Shin me yasa yake jin nauyin sanar da ita kaunar da yake mata? Duk lokacin da yazo gaya mata sai yaga kamar zai shiga haƙƙinta tunda tana da zaɓin ranta ya kuma san bashi bane, sosai Rafeeq ɗin yake jin rashin dacewar hanata san abinda take so. Ya shiga cikin zurfin tunani wanda yasa har Maimoon ta buɗe ɗayan side ɗin ta shiga har ta zauna baisan tazo ba. Hannunta yaji ta riƙo nashi tana ɗan matsawa hakan yasa shi ɗagowa, ido suka haɗa ta lumshe masa na ta da wani yanayi mai cike da rigima ya kawar da kai yana zare hannunsa daga nata. "Shine ka taho nan ka barni ko?" Yai shiru ba tare da yace da ita komai ba. "Ina son komawa school Yaya akwai abinda zanyi." Kafin yai magana wayarsa tayi ringing, da kyar ya iya zarota daga cikin aljihu yana dubawa yaga mai kiran, da girmamawa ya ɗaga yana gaishe da shi da respect yake kuma faɗin. "Daddy ina zaria." Da mamaki Alhaji Mustapha Gwarzo yake faɗin. "Zaria kuma Rafeeq, Me ake yi?" Kallon Maimoon yai yana rasa abinda zai gaya masa, jin shiru yasa shi kuma tambayarsa. "Mekaje yi a zaria Rafeeq?" Lumshe ido yai gashi baya san yin karya sai dai dole ya yiwa abin kwaskwarima yadda ba za a gane shi ba kai tsaye. Cikin dauriya yake cewa. "Nazo wajan friend ɗina ne, Amma yanzu muna tare da Moon tace gobe zata dawo gida shine nake tunanin zan jirata sai mu dawo ba sai driver yasha wahala ba." Alhaji Mustapha Gwarzo yake faɗin. "Baka gaya min ba gashi baki sun zo an kawo kayan lefe duk bakwa nan daga kai har Shaheed ɗin. Shikenan Allah ya kaimu goben da rai da, lafiya." Da sauri Rafeeq ya dafe goshi yana jin wani irin kishi jin an kawo lefen, shikenan yasan Maimoon tayi masa nisa ya rasata a lokacin da yafi kowa buƙatar ta. Da kyar ya iya yiwa Daddy sallama ya sake kifa kanshi jikin sitiyari yana cije lips ɗinsa na sama......

(Anya Rafeeq zai kai labari kuwa? Me yasa Maimoon ta kasa gano labarin zuciyar Yayan nata akan fuskar sa? Soyayyar Wahaab ce ta hanata gane ta yayanta ko ya abin yake? Muje zuwa cikin alƙalamin Asmy da Hajja ce)




#ASMY B ALIYU
#HAJJA CE
#Rafeeq Gwarzo
#Maimoon Gwarzo
#Abdul-wahaab


ƳAN TAGWAYE BIYAR 2023

ƘASAITATTUN LABARAI MASU DAƊI DA SANYA NISHAƊI, SABON SALO MAI ƊAUKE DA DARRUSA NA RAYUWA UWA UBA ƘASAITATTUN SOYAYYA MAI HUDA JIJIYA.

IYALINA (A'ILATY)
RAFEEQ
MUNƊO
ZAMANIN MU AYAU
FATHIYYA.

  DOMIN SIYAR GUDA BIYAR N1500.

DOMIN SIYAR DAYA N400.

Account Details
2083371244
Zenith Bank
Aisha m salis

Ga MUTANEN MU NA NIGER 🇳🇪

Tura ta Nita
Da sunan

Asma'u Buhari Aliyu
08086207764

SAI KI/KA IS TURA SHAIDAR BIYA TA DAYA DAGA CIKIN NUMBOBIN NAN.

+234 808 620 7764
07065283730
+234 705 124 4211
+234 704 040 2435

RafeeqWhere stories live. Discover now