*PAID BOOK #400*Na
_*ASMY B ALIYU*_
Da
_*HAJJA CE*_8.....
Da mamaki Yakumbo ke mata wani irin kallo tana bin ƙofar da ta zubawa ido kamar mai nazarin wani abun, bata ga komai ba a hanyar hakan yasa ta kiran sunanta da kulawa. "Haneefa." Ba tare da ta ɗauke ido daga bakin ƙofar ba ta amsawa Yakumbo "Na'am." Mamaki ne ya kama Yakumbo, anya yarinyar nan lafiyarta ƙalau kuwa? Wannan fa duk ba ɗabi'unta bane amma taga tunda suka zo gidan nan ta fara canzawa komai nata juyewa yake yana komawa kalar mamaki. "Ki tashi daga parlorn nan kije kiyi kwanciyarki kin zauna kina tunani." Yakumbo ta faɗa tana ƙoƙarin shiga kitchen dan haɗo ruwan tea tasha.Haneefa ta shiga turo baki ita kam bazata iya kwanciya ba sai taga shigowar Rafeeq Gwarzo da take jin bugun zuciyarta yana sake canzawa saboda wata soyayyarsa da take shigar ta a hankali. Aunty ce ta fito daga wajan Daddy zata nufi kitchen taga Haneefa kamar gunki ta zubawa hanyar shigowa parlorn idanuwa, mamaki ya kama Aunty cike da kulawa take faɗin. "Haneefa tunanin me kike haka?" Haneefa ta ɗan juya gani take kamar an gano abinda yake damunta, rausayar da kai tayi gefe tana gaida Aunty ta amsa da kulawa kafin tace. "Gidan ne yayi min girma Aunty saboda rashin Maimoon." Aunty na wucewa kitchen take cewa. "Aikuwa bata nan wai test gareta shine ta koma makarantar." Bata jira me Haneefa zata faɗa ba tabar wajan. Yakumbo ta tarar tana zuba tea cike da girmamawa kamar yadda Daddy ke bawa Yakumbon girma itama ta gaishe da ita tana cewa. "Yakumbo maimakon ki kirani na haɗa miki? Kawo a ƙarasa kije parlor kiyi zamanki." Aunty ta fara ƙoƙarin karɓar mug ɗin Amma Yakumbo ta janye tana cewa. "A'a kibarshi ai na gama haɗawa, ga Lami can ma ta fara shirya kayan karin ni da yake kinsan ba jira nake yi ba da safe." Ta ƙarasa maganar tana buɗe fridge ta ɗakko bread kai tsaye ta dawo parlor tana sake kallon Haneefa da duk ta rasa nutsuwarta.
Yana tuƙi yana shafa haɓarsa dake ɗauke da wani ƙawataccen (beard) bakin gashi da ya sake ƙawata kyawun hlittar fuskarshi, tunani ne fal a cikin zuciyarshi na yadda zai kawo karshen alaƙar maganar auran Maimoon Gwarzo da Abdul-Wahaab wanda za a yi shi kwana nan, amma ya rasa mafitar da zata hana ayi shi gashi har yau za'a kawo kayan auranta yana ji kuma yana gani ba zai iya hanawa ba. Babbar damuwarsa a wannan lamarin itace Maimoon ɗin wani irin kallo takeyi mishi irin wanda take yiwa Shaheed Gwarzo da Moobarak Gwarzo, abin nufi da kallon anan shine babu aure a tsakanin su tana mishi kallon sun haramta wajan yin soyayya irin ta aure. Banda haka Rafeeq Gwarzo namiji ne da ba kowacce mace zata iya gani bace ta kyale saboda tsarin halitta da ubangiji ya bashi. Kai ya shiga juyawa yana jin zuciyarsa na wani irin nauyi, duk da cewa gudu yake yi mai cike da nutsuwa da babu wanda zai zageshi ko ya aibatashi, amma shi gani yake yi tamkar baya saurin. Ƙaguwa ce cike a zuciyarsa na san ganin Moon Yana ganin kamar sunyi watanni basu haɗu da juna ba. Wayarsa ce ta fara ringing ya ɗan ja ƙaramin tsaki dan shi a yanzu baya san ana damunsa, gani yake komai yai masa zafi a cikin duniyar. Gudun motar ya ɗan rage sannan ya zaro wayar daga cikin aljihun gaban rigarsa yana duba sunan mai kiran. Zeeeee ce, Rafeeq ya ɗan cije leɓe yana sake yatsina fuska, baya buƙatar kiran kowa idan ba na Maimoon ba kuma yasan ba kiranshi zatai ba sai dai ta kira Wahaab tunda shine zabin zuciyarta. Kamar anyi masa duka haka ya kara wayar jikin kunnansa yana riƙe da sitiyarin motar da ɗan karfi saboda wani irin nauyi da yaji kansa nayi, yaji muryarta tana cewa. "An tashi lafiya?" Yace, "Uhmmm na tashi." Zee ta sake jan pillow ta rungume a jikinta idanun ta a lumshe babu abinda take hangowa sai kyakkyawar fuskar Rafeeq, cikin nuna kulawa tace. "Naji kamar baka ma gida, kana ina da sassafe haka?" Sai da yaja numfashi yana wani lumshe idanuwa ya sauke sannan yace da ita. "Ina hanyar zuwa zaria." Gaban Zee ne ya wani irin bugawa dan tasan tabbas Rafeeq wajan Maimoon zaije a wannan lokacin duk da bata da tabbacin ta koma makaranta. Shin takoma ne dama ko kuwa dai ba wajanta zai je ba? Shin wai me yasa Rafeeq Gwarzo ya sadaukar da duk wani lokaci nashi da jin daɗinsa, walwalarsa duka a wajan wacce bata ma san yanayi mata wata kalar soyayya ba? Anya babu bakin ciki a cikin wannan lamarin? Ita ya kamata Rafeeq Gwarzo yaiwa wannan kulawar da nuna tsantsar soyayya tunda tana sonshi ta kuma damu dashi ya sani, sai dai ya kasa bata muhimmancin da take buƙatar samu a wajansa bare har ya mallaka mata komai nashi kamar yadda ya miƙawa wacce take shirin fara yin rayuwa mai daɗi tare da wani ba shi ba. "Lafiya dai ko?" Zee ta daure tare da jefa masa wannan tambayar wacce tasan ita kaɗai ce zata raba shirun da sukai na ɗan lokaci. Kuma damƙe sitiyarin yayi zuciyarsa na sake hasaso masa Maimoon Gwarzo a cikin idanunsa. "Zanje na kaiwa Moon wani saƙo ne, kuma kinsan menene Zee?" Bai jira tayi magana ba yaci gaba da cewa. "Yau za a kawo kayan lefenta ina cikin damuwa bansan wanda zan gayawa yadda nake jin zuciya ta ba. Please pray for me ko zan samu sassaucin yadda nake jin raina." Wani irin kishi ya tasowa Zee tana jin duk wata kalma dake fitowa daga bakin Rafeeq nayi mata nauyi cikin zuciyarta. Ita kam yanzu me zata cewa Rafeeq Gwarzo ya gane cewa ya hakura da Maimoon tunda tayi masa nisa? Tasan yanzu idan ta nuna bata bayanshi kila ya dena kulata abinda ita kuma ba zata iya jurewa ba. Cikin dauriya hannunta dafe saman kirjinta take faɗin. "Ka gaya mata sirrin zuciyarka kawai mana Rafeeq, dan wannan shirun da kake yi babu abinda zai ƙara maka sai damuwa tunda kaga dai wani yana shirin mallaketa gaba ɗaya." Ɗan shiru yayi yana cije leɓansa na sama, haka kawai bai san meyasa ba sai yaji maganganun Zee ɗin suna yi masa rashin daɗi a cikin ranshi. Ya sake jan ajiyar zuciya kamar tana gabansa yake cewa. "Zainab ki gaida mutanen gidan idan na dawo zamu yi waya." Ya faɗa yana datse kiran ba tare da ya jira me zata faɗa ba. Tuki ya cigaba da yi cikin natsuwa yana son kuma ya samu hanyar da zai fallasawa Maimoon Gwarzo cewa yana tsananin kaunarta a yau ɗin nan, sannan ya tabbatar mata da cewa dan shi kawai aka halicceta. Amma wani ɓangaren na zuciyarsa tamabayarsa takeyi shin ta ya ya zai gaya mata? Ya manta ne tana da zaɓin zuciyarta? anya kuwa Rafeeq bakayi zurfi dayawa ba a lamarinka da Maimoon? ji yayi zuciyarsa na qaryewa a hankali, haka kuma yaji tamkar ya juya kan motar ya koma gida ba sai yaje gurinta ba, sai dai yasan idan ya koma gidan damuwace zata qara cika masa zuciya, gara ya lallaɓa yaje ya ganta, fatansa Allah ya buɗe bakinsa a yau ya faɗa mata sirrin dake ransa watakila zata amince ta karbi soyayyarsa fiye da wancan baren dake gefe yana wasa da zuciyarta.
Tana jin yadda Ayshaa ke ɗan buga pillown da tayi matashi dashi, a hankali ta soma buɗe fararen idanunta wanda basu gaji da yin baccin ba, ta kalli Ayshaa tana ware mata ido tana faɗin. "Kina kallon agogo kuwa? Toh ko tashi dan bai wuce minti talatin ba mu shiga test ɗin kin san kuma halinshi ba kirki ne dashi ba kar ya sa muyi missing wannan gwajin." Miƙewa zaune Maimoon tayi tana ƙara murza idanunta take faɗin. "Kaina ciwo yake min Ayshaa, gashi ko'ina na jikina ciwo yake yi na rasa meke yi min daɗi yau." Ta ƙarasa maganar tana ɗaukar wayarta taga miss calls ɗin Abdul-waahab sai dai bata bi ta kansu ba saboda tasan idan ta kirashi zai tsareta da magana ne har su makara. Da sauri ta aje wayar kai tsaye toilet ta faɗa a gurguje tayi wanka ta shirya cikin ɗinkin doguwar rigar atamfar gillter wacce tayi matuqar yi mata kyau. Duk yadda Ayshaa taso ta tsaya tasha ko da tea ne ƙin tsayawa Maimoon tayi tana faɗin suje kawai idan suka fito sai ta samu abunda zataci.
Suna cikin rubutu text ɗin saqo ya shigo wayarta amma babu halin ta duba saboda kar ai mata magana ko a korata ma. Dole ta hakura sai da suka gama suka fito suna ɗan maida maganar yadda gwajin yai musu, ta buɗe jakar ta ɗakko wayar daman ta sakata a silent ne shi yasa ma ba'a lura ba sai ita kadai. Da mamaki take duba saƙon tana kuma ware ido. Rafeeq ne ya mata sakon akan cewa yana cikin makarantar su ta fito, sai kuma ga kiransa kusan kira 5 wanda har ta fara hango yanayin fuskar Rafeeq ɗin a wannan lokacin, tasan tabbas yana can ya cika ya yi fam kiris yake jira a taɓoshi. Ta kalli Ayshaa tana faɗin. "Zo muje ku gaisa da Yaya Rafeeq shine yazo tun dazun." Ta sake kallan Ayshaa da fuskar tausayi take faɗin. "Idan muka je dan Allah kiyi masa bayani idan ba haka ba wallahi canyeni zai yi da faɗa saboda ya kira ban ɗauka ba, komai zan faɗa masa ba ganewa zai ba zai yadda ba." Ta faɗa tana mai da hannayenta baya. Murmushi Ayshaa tayi tana faɗin. "Da gaske wannan Yayan naki sonki yake yi sosai, Allah Maimoon soyayya ta musamman yake yi miki ko ki yadda ko karki yadda idan ba haka ba meye na biyoki har Zaria yau? baga waya nan ba me yasa ba zai kiraki ya gaya miki koma meye ba? Yaushe kika baro gida da har za a zo miki ziyara? Idan har kinga irin wannan tana faruwa toh tsantsar kauna ke janyowa wallahi. Gaskiyyar Abdul-Waahab ne da yace Yayanki Rafeeq yana da wata manufa tsakanin ku." Lokaci ɗaya fara'ar dake cikin fuskar Maimoon Gwarzo ta ɗauke gaba ɗaya, cikin yanayi na ɓacin rai take cewa. "Meyasa kika kasa yadda Yaya Rafeeq baya min soyayyar aure Ayshaa? sai dai yana min soyayya ne irin ta ƴan uwantaka kawai, karki manta matsayinsu ɗaya ne da na Yaya Shaheed a wajena. So ki daina ma wannan tunanin naki ki daina biyewa Wahaab kuna ƙoƙarin rugurguza kyakkyawar fahimtar dake tsakanina da Yaya, shima idan munyi aure zai daina zargi ya gane. Shakuwace kawai kuke ganin kamar Yaya Rafeeq yana sona. Karki manta yasan ina da wanda nake so, karewarta ma yau ne za a kai lefen Wahaab gidan mu, please mu tafi karki ɓatamin rai da sanyin safiyar nan." Maimoon taja hannun Ayshaa tana wani haɗe rai dan karma ta ƙara jan maganar, da ita da Abdul-Wahaab ta rasa me yasa suke hango cewar kamar Rafeeq Gwarzo yana yi mata soyayyar aure ba soyayyar Yaya da ƙanwarsa ba. Abun yana bata mamaki tare da ɗaure mata kai, da gaske ita kam bata yiwa Rafeeq Gwarzo soyayyar aure, tana jin matsayinsu ɗaya a zuciyarta kamar yadda takejin matsayin Yayanta Shaheed da Yayanta Moobarak..#ASMY B ALIYU
#HAJJA Ce
#Rafeeq gwarzo
#maimoon gwarzoƘASAITATTUN LABARAI MASU DAƊI DA SANYA NISHAƊI, SABON SALO MAI ƊAUKE DA DARRUSA NA RAYUWA UWA UBA ƘASAITATTUN SOYAYYA MAI HUDA JIJIYA.
IYALINA (A'ILATY)
RAFEEQ
MUNƊO
ZAMANIN MU AYAU
FATHIYYA.DOMIN SIYAR GUDA BIYAR N1500.
DOMIN SIYAR DAYA N400.
Account Details
2083371244
Zenith Bank
Aisha m salisGa MUTANEN MU NA NIGER 🇳🇪
Tura ta Nita
Da sunanAsma'u Buhari Aliyu
08086207764SAI KI/KA IS TURA SHAIDAR BIYA TA DAYA DAGA CIKIN NUMBOBIN NAN.
+234 808 620 7764
07065283730
+234 705 124 4211
+234 704 040 2435