*RAFEEQ* 7

29 2 0
                                    


*PAID BOOK #400*

TEAM TAGWAYE NOVEL'S.

Na
_*ASMY B ALIYU*_
Da
_*HAJJA CE*_

7.....

"Mubishi a hankali har Allah ya kawo mishi wacce yake so tunda suma sauran duk sune suka kawo masoyan su da kansu." Da wani kallo Yakumbo ke kallan Daddy, cikin ɓacin rai take faɗin. "Sai kai ta wani cewa abishi a hankali, jaririne shi?" Daddy ya sake murmusawa yana wani kwantar da kai yake faɗin. "Kinsan maraya dole sai an bishi a sannu ba kamar yadda zaka tanƙwara sauran ba." Baki sake Yakumbo ke kallanshi wani haushi yana cika ta "Rafeeq ɗin ne maraya? Waye zai kalli yaron can yace yayi rashin uwa bare kuma uba?" Daddy ganin kamar ba zata fahimce shi ba yasa shi cewa. "Shikenan sai a tambayeshi aji idan yana da wacce yake so, idan babu sai a duba masa." Yakumbo ta sake taɓe baki tana cewa. "Ai ni wannan yaron ma idan ya yi auran bansani ba koshi zai zama matar, gaba ɗaya sullutu ne ga shegen faɗin ran jaraba." Girgiza kai kawai Daddy yai cikin san kawar da zancen Rafeeq yace da ita. "Gobe iyayen Abdul-Wahaab zasu kawo kayan lefe already Auntyn su ta bada aikin snacks, juice kuma gasu can a store tace za'a soya kaji ne ko naman rago oho dai sai kuma abinci da za a yi, toh a ganinki sai kuma meye za'a ƙara? Ko kuma meye ba'a yi ba?" Ta wani haɗe rai "Yo sai da matarka ta gama tsara komai sannan za'a nemi shawarata? Ai ta riga ta gama komai sai dai tukuici kawai da zaka ajiye musu." Ran Daddy ya ɗan ɓaci sai dai ko a fuskarsa bai nuna ba ya riga yasan Yakumbo da san girma da yasan maganar da yai zata canza mata manufa ba zai yi ba."Shikenan za a ɗora, kamar naira nawa kenan?" Ya faɗa yana san bata damar da take buƙata. Sai da ta kawar da fuska sannan tace ta wani hura hanci kafin tace. "Ahhh iya ƙarfin ka, sai ka duba kaga yanayin su dangin yaro, idan masu kwari ne sai ka basu da daraja, idan kuma gasu nan ne dai to sai ka basu ashirin ma tayi." Daddy ya jinjina kai daga nan sukaci gaba da hirar yadda abubuwan zasu kasance. Rafeeq na fita daga parlorn yaga Haneefa tsaye da alama shi take jira ya fito, sau ɗaya ya kalleta ya ɗauke kai yana nufar sashen su. "Yaya Rafeeq baka ganni bane ba?" Cewar Haneefa tana turo baki kamar zatai masa kuka. "Hanee na ganki mana me ya faru?" Ta wani matso kusa dashi har suna jin kusancin juna, wasa ta shiga yi da ƙasan rigar ta bata iya ce masa komai ba saboda wani mugun kwarjini da yake yi mata. Ganin kamar bata da alamar magana yasa shi tafiyarsa, ta wani buga ƙafafuwanta tana turo baki cikin muryar shagwaɓa yaji tace. "Yaya Rafeeq Maimoon." Ko jiran ƙarshen maganar beyi ba ya juyo da wani yanayi a fuskarsa yaga tana shagwaɓe fuska. "Bata nan ba abokin hira please Yaya nazo muyi hirar da kai?" Dawowa yai har gabanta yana wani haɗe rai tare da kai fuskarsa wajan ta ta kamar zai kai mata sumba, a gigice ta wani rintsa ido tana damƙe hannuwanta wani fitsari na taruwa a cikin mararta wanda ƙiris ya rage ya zuba kawai taji yace. "Jeki ki kwanta kafin kisa Yakumbo tayi min wata fassara akan ki." Da sauri ta kalleshi tana sake kallan kyakkyawan lips ɗin shi. Kafin tayi magana taga ya juya ya nufi side ɗin
Su. Bubbuga ƙafa tayi tana yatsina fuska, juyawa tayi zata koma ciki taji muryar Yaya Shaheed yana mata magana. "Menene Hanee?" Ta sake yatsina fuska cikin shagwaɓa wace gabaki ɗaya Yakumbo ce ta maida ita dan bata san ɓacin ran Haneefa ko kaɗan, sosai ta shagwaɓa ta. Cikin turo baki take faɗin. "Yaya Shaheed ba Ya Rafeeq ne ba ni bansan me yasa yake da shariya ba, ko magana fa sai yaga dama yake min." Dariya Shaheed yai shidai Rafeeq duk wanda zai zo gidan nan sai anyi korafi  akan shariyarsa, sai dai fa mutum ne shi mai matukar mutunci da girmama mutane, uwa uba abun hannunsa baya rufe masa ido yana da kyauta sosai  irin wacce ake so. "Toh Hanee sai ki hakura ai kinsan halin Yayan naku." Sake turo baki tayi. "Maimoon bata nan gidan ya sake yi min girma Yaya Shaheed." Bayan kansa ya shafa da murmushi a fuskarsa yake faɗin. "Ki kunna kallo mana sai ya ɗebe miki kewa, nima dan dai free call zanyi yau da na shigo na tayaki hirar." Haneefa ta rausayar da kai tana kallon wayar hannun Shaheed, kamar zatai magana sai kuma ta juya tare da shigewa masaukin su. Yakumbo ce ta shigo ɗakin, kallan Haneefa tayi wacce ke faman haɗe rai tana wani rufe ido Yakumbo tace. "Ke kuma meye hakan? Waye ya taɓaki?" Hafeefa ta shiga juya ido tana turo baki take faɗin. "Yaya Rafeeq ne." Ran Yakumbo ya ɓaci jin tace Rafeeq ne yasa ranta ɓaci. Da kulawa ta isa wajan Haneefa, kafaɗarta ta riƙo cike da soyayya take tambayarta. "Meyayi miki dan nasan da wannan shiru-shirun nashi yake yiwa mutane rashin mutuncin da yake so. Sanar min yanzu naje na sameshi har ɗaki." Da wani kallo Haneefa ke bin Yakumbo ta sake turo baki Yakumbo tasa hannu ta buge bakin cikin masifa take cewa. "Ina tambayarki zaki tsaya kina zumɓuro min baki, Toh ma wani shegen ne yace kije wajan Rafeeq ɗin da har yai miki abinda ya ɓata miki rai? Idan na sake ganinki tare da shi sai ranki yayi mugun ɓaci." Yakumbo na gama faɗa ta mike tana gyara wajan kwanciyarta wato kan rug dan bata san hawa gado ko a can gidan ta. "Kika ce na dena kulashi? Haba yakumbo  dan uwana ne  fa." Wani kallo Yakumbo ta sake wurgawa Haneefa tana faɗin. "Nafiki sanin hakan, kuma bawai mantawa nayi ba bare ki tuna min. Rafeeq ɗin ne bana son kina shige masa karki sake janyo min raini a wajan sa." Hawaye ne suka shiga yawo a saman fuskar Haneefa, da muryar kuka take cewa. "Yakumbo nida nake cewa zaku haɗa mu aure dashi? Ina son Yaya Rafeeq da ga...." Ai bata ƙarasa ba Yakumbo ta jefa mata pillow a fuskarta wanda yasa ta haɗiye sauran maganar da take yi. Kuka Haneefa ta saki tana faɗawa kan gado, Yakumbo taja tsaki tana sake gyara shimfiɗarta sai masifa take. "Kiyi kukan jini indai Rafeeq ne ina raye ba zaki aure shi ba, ko meye abin so a wajan mutum mai shigen faɗin rai? Kiyi kukan babu lallashinki da zanyi." Yakumbo ta faɗa so pissed up ta nufi makunnin fitilar ɗakin ta kashe ta duka tayi kwanciyarta tabar Haneefa cikin kunnar zucci dan har ta fara tunanin da gaske Yakumbo ta daina sonta tunda har zata iya yi mata iyaka da soyayyar Rafeeq Gwarzo. A hankali shesshekar kukan Haneefa ke tashi a dakin, shiru Yakumbo tayi duk da ba baccin take ba, a hankali kukan autarta tata ke wani taɓata, ko kaɗan bata son ɓacin ran Haneefa. Kai tsaye ta miƙe tsaye ta lalubi makunnin fitilar haske ya gama gauraye ko'ina, kai tsaye Yakumbo ta zauna gefen bed ganin haka yasa Haneefa ta wani kwantar da kanta kan cinyar Yakumbon hawaye na rolling cikin fuskarta tana sauke ajiyar zuciya a hankali. Yakumbo na shafa kanta a hankali cikin sanyi murya ta kira sunanta ba tare da Haneefa ta amsawa Yakumbo ba kawai runtse ido tayi. A hankali Yakumbo ta nisa kafin tace. "Nifa ba wai ƙinki nake da Rafeeq ba, a'a Haneefa idan ke kina sonsa ke kin san wacece a tasa zuciyar? Ko kina tunanin bashi da wacce yake so?" Da sauri Haneefa ta miƙe zaune ta wani rike hannayen Yakumbo tana faɗin. "Yakumbo bayan auren ni nasan zai soni, da gaske ina sonsa  Yakumbo idan ban aureshi ba zan iya mutuwa. Nidai kiyiwa daddy magana idan ba haka ba zan iya mutuwa ko na shiga duniya kowa ma ya huta." Da sauri Yakumbo ta rufe mata baki da hannunta tana wani zaro ido take faɗin. "Duk zuri'ar Gwarzo babu mai yawan bariki karma na ƙara jin wannan maganar ta sake fitowa daga bakin ki Haneefa. Ki goge hawayenki zanyi magana da shi baban nashi nasan zaiyi farin ciki da hakan. Shi kuma Rafeeq dole ya yadda ya aureki inhar yana son albarkar mu." Wani irin murmushi Haneefa tayi ta wani rungume Yakumbo jikinta, cikin jin daɗi take faɗin. "Dan haka nake matukar kaunarki Yakumbo, Allah yasa tare dake zamu mutu ga kabarina ga naki." Murmushi Yakumbo tayi tana faɗin. "Ki kwanta kiyi bacci mai daɗi gobe zamuyi magana da Baban ku Insha Allahu." Sai da yakumbo ta tabbatar Haneefa ta koma ta kwanta sa'annan itama ta koma makwancinta, amman a can ƙasan ranta damuwa ce fal aranta, ko kaɗan bata son Haneefa ta shiga cikin damuwa zata tsaya da kafafunta har sai ta tabbatar da auren Rafeeq da Haneefa ya tabbata. Ya kirata yakai sau goma amma har lokacin waya takeyi, nan take zuciyarsa ta bashi amsar waya takeyi kuma da Abdul-wahab. Haɗa kansa yayi a bango yana jin zuciyarsa na wani irin tafasa, a daren bai samu yin wani bacci ba. Suna dawowa Shaheed kawai ya faɗawa cewa zaije Zaria amma yace kar ya faɗawa kowa dan a yau zai dawo. Fatan sauka lafiya ya yi masa ko cikin gida bai shiga ba kusan ƙarfe 7:00am motarsa tabar cikin harabar gidansu dan ko kaɗan bai son haɗuwa da Yakumbo ta cika sakawa mutum ido da magana akan abunda bai shafeta ba, ga kuma ƴarta a gefe da ya lura tana ƙoƙarin shiga rayuwarsa karfi da yaji wanda shi kuma baya buƙatar hakan. Yau tunda safe ta tashi da wata irin murna cikin fuskarta jin kawai Yakumbo zatayi maganar aurensu da Rafeeq Gwarzo. Zaune take a parlor ta kurawa ƙofar shigowa parlourn ido da alamar akwai wanda takeso ta gani ya shigo...




#ASMY B ALIYU
#HAJJA CE👈
#TEAM RAFEEQ
# ƳAN TAGWAYE BIYAR 2023

ƘASAITATTUN LABARAI MASU DAƊI DA SANYA NISHAƊI, SABON SALO MAI ƊAUKE DA DARRUSA NA RAYUWA UWA UBA ƘASAITATTUN SOYAYYA MAI HUDA JIJIYA.

IYALINA (A'ILATY)
RAFEEQ
MUNƊO
ZAMANIN MU AYAU
FATHIYYA.

  DOMIN SIYAR GUDA BIYAR N1500.

DOMIN SIYAR DAYA N400.

Account Details
2083371244
Zenith Bank
Aisha m salis

Ga MUTANEN MU NA NIGER 🇳🇪

Tura ta Nita
Da sunan

Asma'u Buhari Aliyu
08086207764

SAI KI/KA TURA SHAIDAR BIYA TA DAYA DAGA CIKIN NUMBOBIN NAN.

+234 808 620 7764
07065283730
+234 705 124 4211
+234 704 040 2435

RafeeqWhere stories live. Discover now