*PAID BOOK #400*NA
*_ASMY B ALIYU_*
DA
*_HAJJA CE_*TEAM TAGWAYE.....
13...
Sai da ya tabbatar da ta fita sannan ya buɗe ƙofar ya fito yana jin wani irin ɓacin rai. Da gaske Maimoon tafi bawa Wahaab muhimmanci akansa, yanzu kenan haka zai zauna ya zuba ido yanaji yana gani ta auri wani ba shi ba? Maimoon ba Alkhairi bace a gareshi? Rintsa ido yayi yana fatan cireta daga ransa ko zai samu sassaucin kishin da yakeji yana shirin kasheshi. Turo baki tayi tana maƙe kafaɗa ɗaya, murmushi yake yana sake hango lokacin da za a ce ta zama mallakinsa gaba ɗaya, ya ɗan shafi kanshi yana kallanta da idanunsa da suke cike da tsantsar bukatarta yace. "Na ƙagu ranar ɗaurin auran nan tazo nifa, wannan shagwaɓar ina jin haushin barinta babu lallashi na musamman." Buɗe idanuwa tayi cike da mamakin kalamansa, ganin yana ɗage mata gira yasa ta saurin kauda fuska da rigima a muryarta take faɗin. "Nifa bana shagwaɓa sai kace wata baby girl." Wahaab ya sake narkewa da salon yadda take masa, gyara zama yayi yana ciro wayarsa ya hau yi mata video yana cewa. "Bari nayi miki video saboda nasan idan na koma dole zanyi missing shagwaɓar nan." Da saurin ta cusa fuskarta cikin kujera tana sake buga ƙafa tare da cewa ita dai gaskiya ya dena. "Zan so ace wannan rigimar akan bed ɗin mu ake yinta." Ya faɗa yana mikewa tsaye. "Yar rikici na zan wuce tunda nazo da wayo da wayo an lallasheni." Maimoon ta mike tsaye kamar zatai kuka. "Ni bana so ka tafi." Ware ido ya yi, "Toh ya kike so ayi tunda naga yau da gaske rigima za'ai min?" Hannu tasa tare da holding ɗinsu a kirjinta tace. "Ka kwana anan please." Wata iri dariya ce ta kwacewa Abdul-Wahaab ya yi ta yin ta sosai dan ba ƙaramin dariya maganar ta bashi ba. "Hayati a nan zan kwana? So kike a kaini ana yaɗawa a social media. Ko kuma so kike wannan ɗan uwan naku ya sake tsanata?" Duk da tasan da Rafeeq yake amman sai da tace. "Ba wanda zai yi magana, Daddy kuwa murna zai taya ni." Tafiya ya farayi yana zura wayarsa cikin aljihu yake cewa. "Zan kwana wata rana, yanzu dai ki bari mu zama mata da miji komai ma zai zo mana da sauki." Har wajan mota ta rakashi ya buɗe passinger seat, wata leda ya ɗakko yar madaidaiciya ya mika mata tayi masa godiya cike da soyayyarsa. Har ya fice daga gidan tana tsaye sai da mai gadi ya rufe gate sannan ta juya zuwa cikin gidan.sai lokacin ta tuna da Aunty ta faɗa mata ya shigo su gaisa da Yakumbo. Tamkar zatayi kuka haka take ji dan tasan mitar Yakumbo sai tafi kwana biyu tana korafi, duk da a wani ɓangaren taji daɗin yadda ta manta ɗin, dan tasan yakumbo zuba zatayi kamar mai ruɓaɓɓan baki a gaban Abdul-Wahaab ɗin har ta kai ga sakata jin kunyar wata maganar da zata fito daga bakinta. Addu'a take Allah yasa babu Yakumbo a parlon kuma Allah yasa babu wanda ya faɗa mata zuwan Abdul-Wahaab ɗin. Kai tsaye kitchen ta nufa ta tarar da ƴan aiki nata gyaran wuri, ta kalli ɗaya daga cikin ƴan aikin nasu mai suna Suwaiba ta tambayeta Aunty fa? ta faɗa mata tana sashenta. Sanin Aunty a irin wannan yanayin da sun gama aiki wanka take shiga shi yasa bata nufi sashen nata ba, kai tsaye room ɗinta ta nufa, tana tura kofar sukayi ido biyu da Haneefa wacce ke zaune kan soofa gabaki ɗaya yanayinta ya canja. Maimoon ta ƙarasa ciki ta aje ledar da Abdul-Wahaab ya taho mata dashi, sannan ta cire hijab ɗin jikinta tana kallon Haneefa wacce da alamar tunani takeyi dan sai da ta ɗaga murya ta kira sunanta sannan ta ɗago a zabure. Haneefa ta kalli Maimoon, ƴar ajiyar zuciya Haneefa ta sauketa yamutse fuska tana faɗin. "Irin wannan kiran Maimoon Gwarzo ai sai ki fasawa mutum dodon kunne." Maimoon ta girgiza kai tana zama gefen bed take faɗin. "Kin kai masa coffee ɗin kuwa? Dan kin san bayason jira indai Yaya Rafeeq ne." Haneefa ta ɗaga kai da wani yanayi a tattare da muryarta take faɗin. "Na kai masa sai dai dakyar ma idan zaisha, ni kam ban san me zanyi Yaya Rafeeq ya soni ba wallahi. Maimoon ban san me zanyi ba wanda zai burgesa sam." Ta qarasa maganar a hankali cike da karaya. "Hakuri zaki kara yi Haneefa ki ɗauka har aranki cewa haka halinsa yake, da kin saba ba zaki kara wahala ba." Wani murmushi mai ciwo Haneefa tayi tana hango maza masu wani irin class dake binta suna rokon ta basu soyayyarta amman a makance take kallon su,
RAFEEQ Gwarzo ne kurum takeyiwa wani irin so da take tunanin ko kanta bata yiwa shi."Baya kulani fa taya zan iya jure ɗauke kan da yake min? Anya ba wata ce ta mallake mana zuciya da gangar jikinsa ba?" Maimoon dariya tayi har tana faɗawa kan bed. "Shi yasa nace miki idan kika jurewa halin Yaya Rafeeq tabbas zaki samu soyayyarsa, kawai dai dan ba tare kuke ba kullum shi yasa kike jin bazaki iya ba Hanee but, koma wacece ta shiga zuciyarsa sai ta fito tunda kina son shi. Muci gaba da addu'a Allah ya tabbatar mana da alkairi." Haneefa ta jinjina kai tana sake hasko yanayin yadda suka kare dashi. Washe gari drivern Daddy ya maida Yakumbo garin Gwarzo, acewarta nan da sati ɗaya zata dawo sai dai tabar Haneefa wacce itama already sun samu hutun makaranta. Shirye-shiryen biki akeyi gadan-gadan tun lokacin da Maimoon ta aiko Haneefa wurinsa ya rage mu'amala da Maimoon ɗin ya fara jan baya-baya da dukan lamurranta, a ganinshi hakan shine zai samu sauqin abunda yakeji aransa game da ita, ko cikin gidan ya rage zama. Iyakarsa da safe ya shiga ya gaishe da Daddy idan sun haɗu da Aunty ya gaisheta idan kuma basu haɗu ba shikenan bai takurawa kansa akan lallai-lallai sai ya gaisheta dan tana matar Daddy. Itama Maimoon hidima tayi mata yawa gabaki ɗaya ta rage zuwa dakinsa ta dubashi bare tasan halin da yake ciki. Sai dai kuma a rana tana yi masa kira fiye da goma ta tambayi lafiyarsa ko tace. "Yaya duk yau ban ganka ba. Me zakaci na saka a kawo maka?" Irin wannan tambayoyin take yi masa a waɗansu lokutta. Shi kuwa wataran da gangan yake ganin kiranta ya share, sai dai yasan ko ya shareta nacinta bazai barsa ya zauna lafiya ba dan zatai ta damunsa da waya har sai ya ɗaga taji muryarsa. Shi kuma avoiding ɗinta da yake ya zata shine zai sa ya daina jinta aransa musamman da yasan ta kusa zama matar wani. Sai dai a kwanakin nan ya kula ba ƙaramar azaba yake sha ba na rashinta a kusa dashi. Gabaki ɗaya duniyar ta hargitse masa baya jin daɗinta kwata-kwata.
Zeeee Liman ta kirashi a waya tace masa Maimoon zata bashi anko ɗinta ya kawo mata dan Allah. Bai ce komai ba ya sauke wayar, tasan haushi yaji, murmushi kurum tayi a lokacin saboda tasan yana cikin tashin hankali. Ana sauran sati ɗaya biki Rafeeq yayi wani irin fita daga hayacinsa, ya sake zama shiru babu inda yake fita yana ɗaki yayi karatu ya shiga media yaga abubuwa duk dan ya samu sassaucin zuciyarsa. Da sassafe sai gashi a ɓangaren daddy lokacin daddy yana zaune a parlornsa yana duba littafin addu'oi ya daga kai yana kallon Rafeeq ɗin kafin ya amsa masa sallamar da ya yi masa, sai da gaban daddy ya faɗi a lokacin ganin irin ramar da Rafeeq ɗin yayi lokaci ɗaya ta ban mamaki. Har kusa da Daddy ya isa ya zauna akan rug gamida tankwashe kafafunsa waje ɗaya. Zuba masa ido daddy yayi batareda ya ce masa komai ba shima, addu'a kurum daddy keyi Allah yasa Rafeeq ɗin ya faɗa masa damuwarsa. Sun kai minti biyu a haka babu wanda yace komai, shi kuma zurciyarsa wani irin bugawa take yana jin yadda yake kokuwa da numfashinsa. Kusan sau uku yana buɗe baki dan ya yiwa daddy magana amman sai ya kasa. muryar Daddyn yaji akansa ya kira sunan sa a hankali. Dagowa yayi yana kallon daddy kafin ya ɗauke idonsa daga cikin na daddy da sauri dan baya iya jure kallon kwayar idon daddy da fuskarsa ma baki ɗayan ta dan wani irin kwarjini daddyn keyi masa. "Akwai abunda kake bukata ne Rafeeq?" Ɗan sosa kai yayi cike da karfin hali yake faɗin. "Daman daddy maganar business ɗinkane dake ƙasar Chaina ko zaka yi min izini na koma companyn ka dake can sai na ci gaba da kulawa dashi." Tun da ya fara magana daddy ke kallonsa, ɗan murmushi daddy yayi yana faɗin ya tashi ya tafi zai yi tunani akai. Duk da RAFEEQ ɗin so yayi a ce a kwanaki biyu ma masu zuwa ya tattara ya tafi, haka yabi umarnin Daddy ya tashi ya bar wajan yana neman hanyar da zai zillewa ganin auran Maimoon da Wahaab Bammali. Ana sauran kwana biyar a sakata a lalle Moobarak Gwarzo ya iso Nigeria. Lokacin Rafeeq na a gida wanda sai yaga dama yake zuwa office, shi ya kira a waya yaje ya ɗakko shi daga air port. "Ka rame da gaske Yaya wata cuta ke damunka haka ne? Amma shine daddy da Yaya Shaheed basu kai ka asibiti aka duba lafiyarka ba? muje gida na dubaka tunda na dawo." Yayi maganar sounding so very serious a muryarsa, daman kuma shi kaɗai ne ya karanci fannin likitanci. Jin surutun Moobarak Gwarzo na saka kanshi na ɗaukar wani irin dumi yasa ya kalli Moobarak ɗin yana faɗin. "Zoka karbi tukin nan ka daina yi min magana haka." Murmushi Moobarak ɗin yayi ya karbi car key ɗin hannun Rafeeq yana jinjina miskilanci irin na Yayan nasu wato Rafeeq Gwarzo. Akai-akai Moobarak na driver yana kallon gefen Rafeeq ɗin wanda ya kwantar da kansa cikin seat ya lumshe ido har suka isa gida. Jin Moobarak yana biyo shi a baya ba tare da ya nufi cikin gidan ba dan gaishe da su Yakumbo yasa ya ɗan juya da mamaki yana kallon Moobarak ɗin. "Nasan meye aranka Yaya, Zan fara duba lafiyarka tukuna sai naje mugaisa." Wannan qaron da mamaki cikin fuskar Rafeeq ɗin yake faɗin. "Wai meke damunka haka? waya faɗa maka bani da lafiya ne? Toh lafiya ta kalau Moobarak karka sakamin wani ciwon kai kaje kayi abinda yake gabaka." Bai san Moobarak da gaske yake ba sai da yaga ya bishi har ɗakin baccinsa. "Ka zauna zamuyi magana Yaya kafin nasan meke damunka." Moobarak Gwarzo ya faɗa da wani irin tone a muryarsa wanda zaka ɗauka shine babba ba Rafeeq ba. "Da gaske akwai abinda ke damunka kana avoiding ɗinsa ne tamkar baka son kowa ya sani, but jikin ka fuskarka komai naka ya nuna haka Yaya tell me meke faruwa da zuciyarka?" Girgiza kai Rafeeq Gwarzo yayi yana kallon Moobarak ɗin, duk cikin su yasan shine mai naci da bin diddigi, zai yi wuya ya barshi muddin baiji damuwarsa ba. Saɓanin Maimoon da Shaheed idan yace baya so zasu barshi ne bazasu takura masa ba. "Kaje kayi wanka ka huta da daddare zamuyi magana." Yadda Moobarak ya tsareshi da ido ne yasa ya wani yamutse fuska ganin kallon da yake masa ya tabbatar alkawari yake so yayi masa. Rafeeq ya mike tsaye da car key a hannunsa yana faɗin. "Fita zanyi idan kana bukatar wani abu ka kirani." Ya faɗa yana nufar kofa. Hakan yasa Moobarak ɗin binsa da ido, yasan yayi haka ne dan ya zille masa. Sai da ya isa kofar gidansu sannan ya ɗaga waya ya kirata, cikin mintunan da basu wuce goma ba sai gashi ta fito, wannan karon babu hijab ajikinta mayafi ne ta yafa sai dai tayi masa kyau sosai cikin shigar atamfar da tayi. Fitowa yayi daga motar ta jingina bayanta da motar tana kallon yadda ya zama wani iri lokaci ɗaya, addu'a take akan Allah yasa shawarar da zata kawo tayi mata amfani itama. Murmushi mai ciwo tayi tana kallonsa tana qara jin wani sabon sonsa fiye da ko yaushe, tana hango irin ramar da yayi duk kuwa akan Maimoon Gwarzo ne da kwata-kwata bata ma san yanayi ba. Ɗan zaman da tayi da Maimoon cikin hidimar bikin nan ta kula da tana matuqar son Abdul-Wahaab wanda zai yi wuya tabarshi. "Maimoon ce koh?" Ta faɗa cikin qaryewar murya tana kallon Rafeeq ɗin yana kallonta da idanunsa da suka faɗa lokaci ɗaya. Ɗan guntun murmushi ya yi. "Na yiwa daddy magana Allah yasa ya amince, Zainab wannan qaron zanyi nisa da gida wanda zai yi wuya na waiwayo, bani da tabbas akan ko zan warke akan zazzafar soyayyar da nake yiwa Moon. Zee akwai ciwo sosai akan abinda kake so amma ka kasa furtawa, kila yin shirun shine mafi alkairi a gareni, but is so painful Zee." Hankali a tashe cikin rawar baki Zeeee tayi saurin katseshi ta hanyar cewa. "Mai kake tunanin zakayi Rafeeq? karka fara gwada min wannan wasan dan Allah. Zaka sameta cikin sauqi ni nayi maka wannan alkawarin. Amman ban sani ba ko zaka bi shawarar da zan baka. Da sauri Rafeeq ke faɗin. "Kwana biyar ya rage ta zama tashi taya zan sameta Zainab?" Ya faɗa da rawar murya. Murmushi samun nasara tayi kafin ta tattaro dukkanin jarumtarta tana faɗin. "Hanya ɗaya ce idan zaka yi." Cikin zumudin son jin hanyar yake cewa. "Faɗa min Zainab kai tsaye dan Allah." With full confidence take cewa. "Ta hanyar yi mata fyade..!" Ai gabaki ɗaya ji yayi kalmar fyaɗe na zauna masa ta wurare daban-daban acikin zuciyarsa. Kallon tabin hankali yake yiwa Zainab ɗin a wannan lokacin, zuciyarsa na zafi yake cewa. "Ƙanwar tawa zan yiwa wannan mummunan aikin? Tabbas ban taɓa tunanin baki da hankali ba sai yau. Toh wallahi da na yi wannan abun ƙara na jure rasata akan na jefa rayuwarta cikin mummunan haɗarin da zai yi wuya ta warke. Tsarkakakkiyar soyayya nake yiwa Moon ba wai wani son zuciya ba. Zainab zan koma gida." Ya faɗa yana kama murfin motar ya buɗe ya shiga ya yiwa motar key. Zainab tana kallonsa yabar gate ɗin gidansu haushi da takaici suka isheta lokaci ɗaya. Tabbas dole ma ta samu taje gidansu Beeba tun da gashi nan bai qarbi shawarar taba sai kallon marar hankali yake yi mata. Jiki sanyaye ta koma gida a gefe tana tunanin ƙaryar da zata yiwa Ammi dan ta samu fita taje gidan Beeba su sake wani plan ɗin....ƳAN TAGWAYE BIYAR 2023
ƘASAITATTUN LABARAI MASU DAƊI DA SANYA NISHAƊI, SABON SALO MAI ƊAUKE DA DARRUSA NA RAYUWA UWA UBA ƘASAITATTUN SOYAYYA MAI HUDA JIJIYA.
IYALINA (A'ILATY)
RAFEEQ
MUNƊO
ZAMANIN MU AYAU
FATHIYYA.DOMIN SIYAR GUDA BIYAR N1500.
DOMIN SIYAR DAYA N400.
Account Details
2083371244
Zenith Bank
Aisha m salisGa MUTANEN MU NA NIGER 🇳🇪
Tura ta Nita
Da sunanAsma'u Buhari Aliyu
08086207764SAI KI/KA IS TURA SHAIDAR BIYA TA DAYA DAGA CIKIN NUMBOBIN NAN.
+234 808 620 7764
07065283730
+234 705 124 4211
+234 704 040 2435#ASMY B ALIYU
#HAJJA CE
#Rafeeq