RAFEEQ 1

69 5 0
                                    

*RAFEEQ*

*PAID BOOK....* #400

NA
*_ASMY B ALIYU_*
Da
*_HAJJA CE_*


Wata shahararriyar mota ce ƙirar zamani ash color da ta gaji da haɗuwa tayi parking a gaban katafaran store ɗin nan wato Sahad store. Sai da aka kusan shafe mintuna biyar kafin a ɓalle murfin motar wacce take ciki ta fito gabaki ɗayanta waje. Tafe take cike da nishaɗi da walwala sanye cikin shigar wata doguwar rigar jallabiya ƙirar ƙasar (Oman) kalar sararin samaniya. Kallo ɗaya zakayi mata kasan da cewar tana taƙama da kuɗin da Allah ya baiwa mahaifinta. Cikin isa da wata irin izza ta shiga ciki tana ware idanunta a cikin store ɗin. Duka-duka minti talatin tayi a cikin shopping store ɗin ta ɗakko duk wasu abubuwan da take da buƙata ta biya aka kai mata cikin mota. Maimoon Gwarzo kenan kyakkyawar yarinya ta gaban kwatance, farace tas irin farin nan na larabawan asali, haka kuma doguwa ce bata da jiki sosai, gabaki ɗaya dai zubinta irin wanda zaka kalleta ne ka kasa ɗauke idanunka a lokaci ɗaya. Ƴa ce ga Alhaji Mustapha Gwarzo wanda mutum ne shi mai kawaici da tawakkali, sannan shi mutum ne mai tausayin gaske, uwa uba kuma mai riƙo ne da addininsa. Yana da matuƙar mutunta jama'a da son maƙotansa fiye da tunanin mutane. Shi ɗin mai sakin fuska ne a wajan mutane, Allah ya bashi wani irin sihirtaccen kyau domin shi ɗin jinsin Fulani ne na asali. Matarsa ta farko ta rasu ne a wajen haihuwar ƴarsa Maimoonatu. Ɗansu na farko shine Abdul-Shaheed Gwarzo sai Moobarak Gwarzo sannan kuma Maimoonatu Gwarzo. Tun bayan rasuwar mahaifiyarsu da kusan shekaru goma sai lokacin Alhaji Mustapha Gwarzo ya ƙara yin wani auren yana da matarsa suna tare. Sai kuma yaron da yake riƙo a wajanshi wato ɗan ƙaninsa wanda tun yana ƙaraminsa iyayen sukayi haɗari suka rasu wato RAFEEQ Habeeb Gwarzo. Sosai Alhaji Mustapha Gwarzo yake riƙe dashi yana jinsa tamkar ɗan cikinsa da ya tsugunna ya haifa, haka kuma ya haɗeshi cikin yaransa baya taɓa nuna mishi wani banbanci a komai na rayuwarsu. Shekarun Maimoona huɗu a duniya ta fara zuwa makaranta, tana da shekaru goma sha ɗaya ta gama matakin primary school, a shekaru goma sha bakwai kuma ta kammala karatunta na secondary school. Babu yadda yayunta ba su yi ba akan mahaifinsu ya tura Maimoonatu karatu can ƙasar waje amma yaki, a cewarsa yana son yaga ƴan matan Nigeria suna kishin ƙasarsu. Dan haka ya samar mata gurbin karatunta a can (A.B.U Zaria). Suma kansu mazan dakyar yabarsu suka fita zuwa ƙasasashen waje karatun. Maimoonatu tun tana ss1 tayi saukarta ta karatun alkur'ani maigirma da kuma sauran wasu littattafai na addinin musulunci. Abdul-wahaab shine mutum na farko da ya fara shayar da ita zaƙi da kuma ɗanɗanon garɗi irin na soyayya. Wato Wahaab mutum ne mai matuƙar hakuri da sanin ya kamata. Abdul-Wahaab mutum ne da yake da ƙarancin haƙuri dan ya zamto ba komai Maimoonatu keyi masa ta ɓata masa rai ba. Gabaki ɗaya Wahaab ba kyakkyawa bane, sai dai kuma baya cikin layin da za'a kirashi da munana ba. Kalar fatarsa mai duhu ce, amman da kaganshi kasan cewar yana cikin hutu da jin daɗin rayuwa. Yazo bautar ƙasa ne cikin makarantar A.B.U, wanda a nan ne alaƙarsu ta fara shida Maimoona. Shekarar su uku tare. Tana komawa gida toilet ta shiga, cikin jacuzzi ta shige tana sakarwa jikinta ruwa mai ɗan zafi. Tana zaune a cikin ɗakinta taji kamar hayaniyarsu Yayah Shaheed, ta duba agogon bangon ɗakin lokacin ƙarfe goma na safe. Ta runtse ido da sauri kafin ta ƙara buɗewa dan san tabbatar da cewar ba wai mafarki take yi ba. Da gudu ta fita daga ita sai kayan bacci a jikinta na riga da wando masu ɗan kauri, ko hula babu a kanta sai kananun kalabar dake ta faman reto a tsakiyyar bayanta. Sosai nayi matuƙar tsaye a wajan dan ganin Yayuna guda biyu a wajan, daman Moobarak Gwarzo ba ƙasa ɗaya suke karatu ba. Shi yana Germany su kuma suna ƙasar Cyprus. Da gudu ta ruga ta faɗa cikin jikin Yayah Shaheed tana ta faman dariyar farin ciki take faɗin. "Yaya kai ne kuwa? Anya kai ne Yah Shaheed?" Yana sake ɗago da fuskarta suna haɗa ido yake cewa. "Yeah ni ne nan mana autar Daddy me kika gani?" Ya faɗa yana ɗage mata gira ɗaya. Cikin murna take cewa. "Gaskiya Yaya ƙasar nan ta karɓeku kai da Yayah Rafeeq, Uhmmm kaga wani kalar haske da kuka yi kuwa?" Ta maida idanunta ta kalli gefen inda Yayah Rafeeq ɗin yake tsaye, ga mamakinta sai taga ya ɗauke kai daga kallanta. Ta marairaice fuska tare da kamo hannunsa cikin shagwaɓa take cewa. "I'm so sorry Yayana, kasan fa bama ƴar haka da kai, ko so kake Yayah Shaheed yayi mana dariya?"
Fisge hannunsa yayi wanda a dai-dai lokacin Daddy da Aunty suka fito. Da murmushi a fuskar Daddy yake faɗin. "Ku kuma haka ake zuwa babu wani sanarwa?" Dukansu suka juya tare da rungume Daddy. Rafeeq ne mai faɗin. "Mun gama komai Daddy har kwalayen karatun mu mun karɓa munyi bankwana da ƙasar Cyprus." Da farin ciki Daddy yake faɗin "Alhamdulillahi Allah yasawa karatun naku albarka." Duk suka haɗa baki. "Ameen." Suka amsawa Daddy. Haka Aunty ma ta tayasu murna. Tare suka shiga cikin kitchen da Aunty muka shirya masu abincin rana. Ƙarfe biyu suna gamawa Maimoona ta shige wanka, daman kuma tana son leƙawa gidan Aunty Amra wato ƙanwar Daddy. Har cikin parlor ta samu Daddy ta sanar dashi zataje yayi mata fatan sauka lafiya shi da Auntyn su. Harta shiga mota sai kuma ta fito da sauri ta nufi part ɗin su Yayah Shaheed, kai tsaye ɗakin Yah Rafeeq ta nufa, sai da taje sannan ta tsaya a bakin ƙofa tayi knocking kafin ta tura ƙofar ɗakin ta shiga. Ɗagowa yayi da sauri suka haɗa ido yayin da ya yiwa ruwan faron hannunshi wata irin kyakkyawar zuƙa. A hankali ta ƙarasa wajanshi ta karɓe jarkar ta  wurgata ta window sannan ta dubeshi cikin muryar damuwa tana faɗin. "Meyasa hakan Yah Rafeeq? Ashe daman baka daina yiwa ruwa irin wannan shan ba tun a lokacin daka kace ka dai na?" Ranta ya ɓaci ta juya zata nufi ƙofa yayi saurin riƙo hannuta ya zaunar da ita a gefenshi. Ta harɗe hannunta akan kirjinta tana faman shan toka. Ganin yadda tayi ne yasa saura kaɗan Rafeeq ya fashe da dariya amman ya danne dan yasan idan har ya yi dariyar ya ƙara takalo wata rigima ne. "Okay na dai na but ina zakije hakan?" Kawar da fuska tayi gefe "Gidan Aunty Amra zanje." Ta faɗa still shaye da toka. Kallonta kawai yake with out blinking kallonta kawai yana sake faranta ranshi domin bashi da wani burin da ya wuce a duniyar nan Maimoonatu Gwarzo ta zama matarsa ta aure ba. "Me kake tunani haka?" Yaji sassanyar muryarta ta sake dukan cikin kunnanshi. Ya sake cijewa yace. "Babu komai, ina zaki hakan?" Sai da ta miqe tsaye sannan take faɗin. "Zanje gidan Aunty Amra ne." Numfashi yaja mai sanyi tare da faɗin. "Alright muje na rakaki toh." Ba tayi musu ba yabi bayanta su nufi motarta. Maimoona ke driving ɗin shi kuma yana gefenta da waya a hannunsa yana dannawa. Har ƙofar gidan Aunty Amra ta ajiye su sannan suka jera suka shiga cikin gidan. A falo Maimoona tayi sallama, da gudu Suhaila ta fito tana mata Oyo-yo-yo. Maimoona ta ɗagata sama tana zagaye parlorn da ita, wanda kuma hakan da tayi yasa Rafeeq Gwarzo ya harɗe hannayenshi akan kirji yana kallonsu yaji tankar a lokacin Maimoonatu matarsa ce da kuma ƴarsu. "Suhaila ina Mami take?" Cikin fara'a take faɗin. "Mami tana ɗakin Abba." Sake janyo hannunta tayi tana cewa. "Okay Suhal fa.?" Tace shima yana ɗaki yana buga game. Dai-dai lokacin Aunty Amra ta fito daga cikin wani ɗaki da fara'a take yi musu sannu da zuwa. Cike da mamaki kuma take tambayar Rafeeq yaushe a garin? Ya faɗa mata cewar ɗazu da safe. Da murna take faɗin. "Allah yasa wannan karon da matanku na aure a hannayenku kai da Shaheed? Dama ga auta nan Daddy na shirin yi mata aure banda ku. Da wani irin yanayi ya juya yana kallon Aunty Amra fuskarsa cike da tsantsar mamaki, kalmar auren da Maimoonatu zatayi yafi ko mai tsaya masa arai. Zai yi magana kuma aka kira Maimoonan a wayarta, dubawa tayi ganin yanayin yadda ta ɗora a jikin kunnan ta take wani amsa wayar ya tabbatar masa da cewa da namiji take wayar. Tashin hankalin da Rafeeq Gwarzon ya shiga a wannan lokacin ba zai faɗuba. Ya rinse ido yana lasar ƙasan lips ɗin shi da harshe yana cewa. "Aunty bari zanje na dawo zuwa anjima." Rafeeq ya faɗa yana ƙoƙarin barin cikin parlorn cike da tashin hankali yana kuma jin wani mugun sanyin na shigar masa duk wata ƙofa ta cikin jinin jikinsa. Tun daga tsakiyyar kansa har cikin tafin ƙafarsa haka yake jin sanyin. Sai da ya fita compound ya tuna baya tare da car key, juyawar da zaiyi ya hango Maimoona na fitowa da fara'a cikin fuskarta. Ganin yanayinsa yasa taji walwalar da take ciki na ɓacewa a hankali. Hannu kawai ya miƙa mata yana cewa. "Bani key ɗin." Kallonsa take ganin irin damuwar dake kwance a cikin fuskarsa yasa taji wata irin damuwa itama, dama kuma gashi duk cikin yayunta tafi jin Rafeeq Gwarzon har a ranta wanda batasan dalili ba. Jiki a sanyaye ta miƙa masa key ɗin tana faɗin. "Daman shi na fito na baka, but wai ina zaka haka kake ta sauri?" Batareda ya kalleta ba yake faɗin. "Yanzu zan dawo ba wani daɗewa zanyi ba." Daga haka ya shiga motar yai mata key yana yiwa mai gadi horn, tana kallon motar har tabar cikin compound ɗin sannan ta ɗan yi ajiyar zuciya ta juya ta koma cikin gidan tana jiran isowar Abdul-wahaab...

RafeeqWhere stories live. Discover now