*RAFEEQ* 15

96 2 0
                                    


*PAID BOOK#400*

LAST FREE PAGES#

NA

*_ASMY B ALIYU_*
DA
*_HAJJA CE_*

Zaune yake akan rug gafda ƙafafun Daddy ya saukar da kansa ƙasa, tun kafin ma yaji me daddy zai faɗa masa yaji zuciyarsa na wani irin rawa, da gaske yasan ko menene zai fito daga bakin Daddyn babu alkhairi acikinsa, hakan yasa duk yadda yaso samun natsuwa kasawa yayi hatta da yatsan kafarsa zufa yakeyi duk kuwa da sanyi ac dake jikin kowace kussurwa ta cikin parlorn. Rafeeq zufa kawai yake haɗawa tun kafin ma yaji me Daddy ya kirawo shi dan ya faɗa masa. "Rafeeq meke damunka haka ne?" Daddy yayi maganar cike da lallashi da kalamai irin na kowanne uba a wajan ɗansa." Dagowa yayi yana kallon Daddyn da idanunsa da suka juye saboda tsabar damuwa. "Soyayyar Maimoon Gwarzo ce Daddy." Rafeeq ɗin ya faɗa acan qasan ransa. Kusan sau uku yana buɗe baki dan ya faɗawa daddy gaskiyar abinda yake damunsa amman ga mamakinsa kalma ko guda ɗaya ta kasa fitowa daga bakinsa. Shiru daddy yayi yana nazarin yaron nasa. Kusan minti biyar babu wanda ya kuma cewa komai a tsakaninsu kafin yaji Daddy na faɗin. "Idan bazaka iya gaya min ba shikenan, sannan kuma Yakumbo tayi maganar a haɗa aurenka da Haneefa sai dai ban sani ba ko a ɓangarenka kana da wacce kakeso, zan baka ɗan lokaci saboda hakkinka ne, na baka nan da sati ɗaya kaje kayi tunanin magana ta, idan kuma kana da wacce kakeso kayi min magana nan da wata biyu masu zuwa zan haɗe aurenka dana ɗan uwanka Shaheed, idan yaso bayan auren sai ka fara shirye-shiryen komawa ƙasar Chaina tareda iyalinka saboda bana so kayi nisa ba tare da muharrama ba, nima haka nafi samun natsuwa Rafeeq idan har kana da iyali a tare dakai." Habawa tunda Daddy ya fara magana yaji dai maganar aurensa da Haneefa, daga nan kuma ya daina fahimtar komai da daddy ke fada masa. Sai da Daddyn ya kira sunan sa da ɗan karfi, a firgice ya ɗaga ido yana kallon Daddy zuciyarsa na sake hargitsewa. "Zaka iya tafiya." Daddy ya faɗa yana kallon Rafeeq ɗin da yanayin da yake hangowa acikin fuskarsa wanda ko kaɗan baya masa daɗi. Tunda ya fito daga parlorn daddy ya kasa fahimtar komai da kowa a cikin duniyar nan. Kai tsaye wajen motarsa ya nufa ga mamakinsa Zeeeee ya samu a wajen tana tsaye tana jiransa. Tunda tasan Rafeeq har kawo yanzu bata taɓa ganinsa a haka ba sai yanzu, wani abu take hangowa a cikin idanunsa wanda bata taɓa ganin kalarsa ba. Matsawa tayi daga jikin motar tana jin yadda kafafunta ke wani irin rawa, gabaki ɗaya tsoro lamarin Rafeeq ya bata, da gaske tsoron lamarinsa takeyi a wannan lokacin. Yau bata fito da motar gidansu ba, da sauri ta nufi gate tamkar zata faɗi ƙasa. Addu'a takeyi Allah ya bata abun hawa da wuri dan bata son ta wuce wannan damar da take da ita. Wani mai napep ne ya sauke wasu a kofar gidan Alhaji Mustapha Gwarzo, suna fita ta shige napep ɗin da sauri tana faɗa masa dan Allah yabi bayan wannan farar motar saboda tasan Rafeeq ba gudu yake da mota ba zai yi wuya ya ɓace musu.
Fuskar Rafeeq Gwarzo ke yi mata yawo a cikin idanunta tana jin yadda kirijinta ke wani irin bugawa, komai zai faru a yau bazata bari wannan damar ya wuce ta ba. (TAHIR GUEST PLACE) nan motar Rafeeq ɗin ta shiga, da sauri Zee Liman ta ciro 1k daga cikin handbag ɗinta ta miqawa ɗan sahun dake faɗa mata ta tsaya ta karɓi canjinta amma ko saurarensa bata tsaya yi ba.
Ko wane taku ɗaya da take yana tafiya ne tareda bugun zuciyarta, wannan qaron bata san ya Rafeeq Gwarzo zai qarbi zancenta ba. Sai da ya nufi entrance ɗin shiga wajen sannan tabi bayansa wanda akwai tazara a tsakaninsu. Rafeeq kuwa har ajikiinsa yana jin yadda ake binsa a baya, amman bai da natsuwar tsayawa yaga ko waye saboda bashi da case da mai bibiyar tashi. Key ya ciro ya shiga buɗe hotel room ɗin yana jin yadda jikinsa ke wani irin kaɗawa. Shiga yayi hannu yasa zai rufe ƙofar kawai Zeee ta riqe ƙofar itama tana kallonsa, girgiza masa kai ta shiga yi, mamaki yake taya akayi tazo nan wajan? "Zainab.!" Ya faɗa cike da gajiya a muryarsa. "Na sani Rafeeq baka so na biyo ka ba but magana zamuyi." Ta faɗa tana kallonsa. Sakar mata ƙofar yayi a hankali ko takalmin ƙafarsa bai cire ba, anan ya zube kan Rug bai san kalar tashin hankali irin  wannan ba sai yanzu da zai rasa Maimoon Gwarzo dukanta. Wata dariya ce ta kwace masa wacce bata da alaƙa da farin ciki ko kaɗan. Girgiza kai ya shiga yi tamkar wanda ya sami tabin hankali. Wai kamar shi Daddy aure zai yi masa kuma batareda ma Maimoon Gwarzo da soyayyarta take niyar haukatarwa, da wata daban zai masa auran, meyasa Daddy zai masa hakan?" Ya faɗa yana yarfe hannayensa. Dogayen yatsun hannunsa ya shiga ja. "Banda wurin kowa a zuciyata Daddy karka ɗora min nauyin da bazan iya yi maka alkawarin zan cikashi da farin ciki ba. Da gaske Maimoon Gwarzo ce kawai a zuciyata." Maganganun Rafeeq ɗin ke zauna mata a cikin zuciyarta da wani irin ciwo marar misiltuwa, tana jin yadda hawayen idonta suka kasa tsayawa. Wace irin marar sa'a ce ita? Ganin kamar Rafeeq ɗin baya cikin hankalinsa yasa ta isa gareshi, zube gwiwonta kasa tayi tana ganin yadda hawaye ke gudu akan fuskarsa tamkar an kunna ruwan famfo kuma wai duk adalilin soyayyar da yake yiwa Maimoon Gwarzo yake kukan, ita kam tayama za'a yi taso Maimoon Gwarzo a rayuwarta? yarinyar da ta hanata jin daɗin rayuwarta, yarinyar da ta shigo kai tsaye cikin rayuwarta ba tare da ta sani ba kuma tana juyata yadda taga dama. Wata irin runguma ya yiwa Zeeeee liman a lokacin abunda bai taɓa faruwa ba a tsakanin su. Wani irin shock Zainab ɗin keji a ko'ina na cikin jikinta, tana jin wani irin mugun feeling na soyayyar Rafeeq Gwarzon tana taɓa ko'ina dake cikin jikinta tana jin wani qalar dumi da jikinsa ya ɗauka. Murya a shake jikinsa na mugun rawa yake faɗin. "Zainab bazan iya rasata ba da gaske bazan iya rasata ba, zan iya mutuwa akan hakan." A hankalin take shafa sumar kansa tana faman rintsa ido, wani irin tausayinsu yana qara cika mata zuciya. Sunfi minti biyar a haka tana riqe dashi jin ya dawo dai-dai yasa ta raba jikinta da nashi a hankali. Tana kallon yadda fuskarsa ta zama lokaci ɗaya. "Kana ji kana gani zaka rasata Rafeeq tunda ga shawara na kawo maka cikin sauqi ta hanyar da zaka sameta babu mai tuhumarka amma kaƙi. Babu wanda zai san wannan sirrin fa dagani sai kai Rafeeq bana san wani abun ya sameke dan ba zan yafewa kaina na. Ta faɗa tana riqe da hannunsa. Gabanta na mugun faɗuwa saboda wannan karon idan bai yadda ba batasan me zai faru ba. Tana so ya amince da hakan, dan ta hakan ne zata samu ta ruguza duk wata alaƙa dake tsakaninsa da Maimoon Gwarzo ta hanyar mallakarsa ita kaɗai. Bata da damuwa koda duka familyn Gwarzo zasu san wannan sirrin, koda duka zasu juya masa baya tayi alƙawarin tana tare dashi a duk inda rayuwa zata kaisu. Tasan koda can Rafeeq ba wani damuwa yayi da arzikin mahaifin su Maimoon ba, saboda shima yana da nashi arzikin, yana da qaddarorin da mahaifinsa ya bar masa a matsayin gadonsa, tasan rayuwa bazata yi musu wahala ba koda basa cikin zuri'ar Gwarzo. "Zaka sameta Rafeeq idan kayi yadda na faɗa maka tun farko. Kasan Allah da tuni yanzu ta zama taka kai kaɗai. sauran kwana biyu a ɗaura mata aure zata zama mallakin wani bakai ba saboda zurfin ciki irin naka." Runtse ido yayi wani kishi na cika masa zuciya, yana da kishi sosai har addu'a yake Allah ya rage masa wannan kishin nasa saboda daga ranar da wani ya kai hannu jikin Moon ɗinsa yasan mutuwa kawai zai yi. "Tayaya zan sameta Zainab? kina ganin yadda security suke cike da gidan mu? tsoro nakeji da gaske Zeee kawai mu canza wata hanyar banda wannan." Da wata irin damuwa take masa magana. "Nasani zan taimakeka Rafeeq saboda jin daɗin ka kawai, zaka sameta ka bani dama kawai." Kallon cikin idanunta yake yana son ya yadda da abunda take faɗa masa, da ya bari ya rasata gara ya nemeta ta wannan haramtacciyar hanyar. Miqewa yayi har lokacin zuciyarsa na rawa yake faɗin. "Ki tafi Zainab zanzo gidanku da daddare muyi magana." Wani daɗi ne ya cika zuciyar Zeee ɗin, lokaci ɗaya ta miqe tsaye. Ɗan murmushi tayi tana kallonsa ta saukar da murya tana faɗin. "Da gaske zaka zo na jiraka?" Ɗaga mata kai kurum yayi batareda ya kalleta ba. Acan ƙasan ranta wani mummunan kishi ne ke danne mata zuciya, wai  itace zata baiwa Rafeeq Gwarzo damar yayi tarayya da wata ba ita ba, wannan ranar kawai Zainab tasan komai zai zame mata dai-dai. Wata zuciyar ta faɗa mata hakan. Har bakin ƙofa ya rakata. "Ka kula da kanka dan Allah." Ta faɗa cikin rawar murya dan har lokacin bai gama dawowa dai-dai ba. murmushi kurum yayi harta fice. Anan bakin ƙofa ya zube yana jin yadda kirjinsa ke wani irin harbawa, idan kuma ya tuna da maganganun Daddy sai yaji komai ya kwace masa yana neman rasa kwarin gwiwarsa. Shikam da ya auri Haneefa a wannan yanayin ai ƙara ya auri Zeeee liman yayi maneji da ita a haka, da dai ya auri ƴar wajen Yakumbo. Yana gama parking motarsa acikin Gwarzo mantion ya fitar da wayarsa ya kirata, Haneefa ce ta miqo mata wayar ganin mai kiranta a waya sai da taji wata faduwar gaba wacce bata taɓa jin kalar ta ba, tana ɗagawa yake faɗa mata ta sameshi a part ɗinsu, yana faɗin haka batareda ya jira me zatace ba ya sauke wayarsa yana jin yadda kafafunsa sukayi masa wani irin nauyi na ban mamaki, dakyar ya taka kafafunsa zuwa cikin part ɗinsu. Anan parlor ya zauna ko minti goma bai yi da zama ba Maimoon ta bayyana cikin falon, wani irin kamshinta ne ya fara bayyana masa cewa ta shigo cikin parlorn kafin yaji muryarta a kansa tana faɗin. "Yaayaah!" Muryar tata kuwa har wani shaking takeyi saboda yadda tayi kewarsa. Miƙewa tsaye yayi yana kallonta da wani irin shauƙi wanda ya fito tun daga cikin zuciyarsa. Rungumeshi tayi da sauri kamar wacce akaiwa baki, wani irin bugawa kirjinsa keyi, jinta ajikiinsa ba ƙaramin kokuwa yake da numfashinsa ba wajan dakewa. "I miss You so much Yaya, da gaske nayi kewarka." Ta faɗa muryata na karyewa. "Karki kadamu Moon bakijin wani kalar nauyi da kika yiba?" Ya faɗa da muryar da ya kwana biyu bai yi mata magana dashi ba. Maimoon ta zare jikinta daga cikin nasa ta shiga turo masa kyakkyawan bakinta, a shagwabe take faɗin. "Bani da nauyi fa Yaya sai kace wata ƙatuwa zakace zan kadamu." Dogon hancinta yaja gamida ware mata mayyan idonsa. Murmushi takeyi sosai rabon da yaga wannan murmushin a kyakkyawar fuskar nan an kwana biyu. Numfashi yaja tare da jan karan hancinsa yake faɗin."Kinata min ƙorafi ban miki komai na gudunmawa ba, bansan me zan yi miki ba dan nasan anriga an gama miki komai." Hannunsa ya tura cikin ajihun rigarsa ya fito da wani ɗan qaramin kit ya buɗe. Sarqa ce ta goal da ƴan kunne sai kuma zobe sai wani irin walwali takeyi. Zata yi magana ya juyata ya ɗauki sarqar yana saka mata jikin wuyanta. Hakama ƴan kunnen yaci sa'a ko ƴan kunne bata dashi a lokacin. Bakinta gabaki ɗaya yaki rufawa, hannunta ya kama ya saka mata zoben yana kallonta da wani farin ciki da yake shimfiɗe acikin fuskarta. "Wishing u Allah khair Noor with blessings in ur new home little sis." Ya faɗa yana danne wani mugun abu a cikin wuyansa. Lokaci ɗaya hawaye suka cika idon ta. Rungumesa tayi cikin rawar murya take faɗin. "I love You so much Yaya Rafeeq ɗina, Allah nasan zanyi kewarka sosai." Ɗagota yayi ya sumbaci goshinta yana faɗin. "Duk lokacin da kike bukata ta ina nan kirana kawai zaki yi, oya jeki gida Moon bana son hawayen nan karki karya min zuciya." Ya faɗa yana kallonta. Da wani yanayi akan fuskarsa. Girgiza kai ta shiga yi tana faɗin. "Nagode Yayana." Juyawa tayi tabar parlorn da ido ya bita tana barinsa da fitinannen kamshinta dake sakashi cikin wani yanayi. Maimoon kuwa duk da ba wannane kawai zinarinta ba, tana da wanda aka bata gado na mahaifiyarta, ga kuma wanda Daddy ya siya mata dana cikin kayan lefe, amma wannan da Rafeeq ya bada yafi kowanne muhimmanci a wajanta. Tana tafiya tana kallon zoben da ya saka mata wanda take jinsa har cikin tsokar kwakwalwalta. A parlor ta tarar dasu Haneefa su Yakumbo da Aunty da kuma sauran ƴan uwa da abokan arziƙi. Wajan Haneefa ta nufa cike da farin ciki wanda ake iya hangowa a kyakkyawar fuskarta. Zama tayi cike da zumuɗi take cewa. "Finally mun shirya da Yaya Rafeeq yau, kinga ma har ya bani gudunmawar Aurenah." Abinka da zuciya tuni ran Haneefa ya ɗan sosu, gani take wannan abun da Rafeeq yayi ba daidai bane ba, ita ya kamata ya fifita akan kowa saboda tana sanshi kuma ita zata zama matarsa uwar ƴaƴansa nan ba da jimawa ba. Kallan Maimoon tayi bayan ta lalibo murmushi da farin cikin yaƙe wanda yafi kuka ciwo tace. "Kai amma fa sunyi kyau, lallai Yaya yana ji dake irin wannan uban kuɗi da ya kashe miki." Murmushi Maimoon tayi tana sake shafa wuyanta inda sarƙartake manne, kallan Haneefa tayi bata ce komai ba ta wuce upstairs tana jin wani irin nishaɗi. Tana zuwa ta tarar Wahaab Bammali yana kiranta a waya, da sauri tayi daga, yadda yaji muryarta cikin farin ciki yafi komai yi masa daɗi, cikin zolaya yake cewa. "Duk murnar an saki a lalle ne ko? Irin wannan murna haka Hayati?" Bata san lokacin da wata dariya tazo mata ba, cikin basarwa dan idan ta gaya masa murnar sun shirya da Yaya Rafeeq ne tabbas ba zasu kwana suna walwala ba. "Toh kai kaga laifina a nan?" Wahaab dake kwance a saman lafiyayyan gadonshi na gidanshi wanda zasu zauna shida ita . yayi  wani irin juyi yana rungume pillows, idanunsa ya lumshe yana jin ina ma ace a wannan lokacin suna manne da junansu tabbas da ya shayar da ita garɗin zumar daya tanadar mata. Cike da tsantsar soyayyarta dake sake huda kowacce ƙofa ta jikinsa yake faɗin. "No babu laifi sai ma jin daɗi. Hayati na gaji da gadin gidan nan ji nake kamar na janyo jibi ta dawo gobe kodai a matso da ɗaurin auran nan gobe?" Dariya ce ta sake kwace mata, lallai Wahaab a ƙagare yake ita har ta fara jin tsoro domin tunda satin bikin yazo taji yana Allah-Allah ranar auran su tayi. Cike da shagwaɓa take cewa. "Nifa ɗazu naje na cewa Daddy a ɗaga zuwa next month kuma yace zai je wajan Abban ku gobe suyi shawara." Kamar a gabansa take maganar domin yana daga kwance kawai ya ganshi a zaune yana ware idanuwa. Ji tayi yana cewa, "Amma dai Hayati mafarki kike yi ko? Wane irin next month ana zaune ƙalau. Please kidena min irin wannan wasan Bazan iya dauka ba wallahi." Sake turo baki tayi tana kuma karya murya take cewa. "Kaga fa lokacin mun gama exam yanzu fa ana ɗaura aure ran Saturday Monday zan koma school kaga babu wani isashen lokaci shi yasa na bada shawarar nan ta a ɗaga bikin." Wahaab ya shafa doguwar fuskarshi tare da jan numfashi yake cewa. "A'a a ɗaura ɗin zuwa exam kuma bazai gagara ba insha Allah. Hayati bazan iya jure har wani month ɗin ba bamu kasance a cikin gidan nan ni dake a matsayin mata da miji ba. Idan kuma ba haka ba ni a gobe ma zan iya sawa a ɗaura auran nan saboda naƙagu ki zama mallakina." Murmushin farin ciki ta saki, lallai Wahaab ba ƙaramin so yake mata ba ita kam dole ta sake godewa Allah da ya haɗata dashi. "Yaji tsoro abashi ruwan maɗaci." Yaji ta faɗa da salon tsokana. Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya sake kwanciya sukaci gaba da hirarsu irin da masoya masu tsantsar son juna.......

_#Shawarar Zeee Liman ta shiga dawo masa cikin kansa akan shawarar da take bashi. Girgiza kai ya shiga yi, a fili yake furta "No hakan bazata taɓa faruwa ba_.

_#Abu ɗaya ne ya rage masa wanda zai bashi damar mallakar Maimoon Gwarzo shine ya saceta kawai subar kan idanun duk wani wanda yake da alaka dasu._

_#Tunda ya baro gidansu Zainab Liman yaji alaqar rayuwarsa na juyewa da wani irin yanayi na ban mamaki wanda bai taɓa tsintar kansa a cikin wannan yanayin ba. Shine yanayin namene? A kuma kan meye yakejin sauyin?_

_#Shin Rafeeq Gwarzo zai yi nasarar lalatawa Maimoon Gwarzo rayuwa kamar yadda Zeee Liman ta bashi shawara? ko kuma dai zai bi shawarar zuciyarsa ta hanyar bin shawarar zuciyar na saceta? Toh wai zata so shine ko yaya?_

#Tsakanin Maimoon Gwarzo, Zeee Liman da kuma Haneefa wacece zata yi nasarar auren Rafeeq Gwarzo?

#Anya auren Maimoon Gwarzo da Abdul-wahab Bamalli zai tabbata? Shin Maimoon Gwarzo zata amince tabi Rafeeq Gwarzo zuwa wata duniyar ta daban dan suyi aure subar mahaifar su? Shin zatama amince da soyayyarsa?_

*Tabbas sai dai ku biyo alkamin HAJJA CE da ASMY B ALIYU acikin wannan doguwar tafiyar mai ɗauke da kalubalen rayuwa kala-kala. Muna tabbatar maku da bazakuyi da nasanin wannan tafiyar ba kamar yadda kuka karanta littafan mu a baya kamar Zo gareni, Nida Raheema, Waminal Hub, Albi (zuciya ta), Muhabbatil Qalb, ga kuma Tafiyar Rafeeq a gefe.....

#FAMILY
#LOVE
#REGRET AND PAIN....

ƳAN TAGWAYE BIYAR 2023

ƘASAITATTUN LABARAI MASU DAƊI DA SANYA NISHAƊI, SABON SALO MAI ƊAUKE DA DARRUSA NA RAYUWA UWA UBA ƘASAITATTUN SOYAYYA MAI HUDA JIJIYA.

IYALINA (A'ILATY)🔥
RAFEEQ🔥
MUNƊO🔥
ZAMANIN MU AYAU🔥
FATHIYYA.🔥

DOMIN SIYAN GUDA BIYAR N1500.

DOMIN SIYAR ƊAYA N400.

Account Details
2083371244
Zenith Bank
Aisha m salis

Ga MUTANEN MU NA NIGER 🇳🇪
Tura ta Nita da sunan

Asma'u Buhari Aliyu
08086207764

SAI KI/KA ISAR DA SHAIDAR BIYA TA ƊAYA DAGA CIKIN NUMBOBIN NAN.

08086207764
07065283730
07051244211
07040402435

#ASMY B ALIYU
#HAJJA Ce
#Rafeeq Gwarzo
#Moobarak Gwarzo
#Team Tagwaye

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: May 05, 2023 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

RafeeqWhere stories live. Discover now