*PAID BOOK#400*NA
*_ASMY B ALIYU_*
DA
*_HAJJA CE_*TEAM TAGWAYE.....
Kayan jikinsa ya shiga ragewa jin yayi idanuwan Shaheed na yawo akansa, ko kaɗan baya son magana dan wani irin ciwon kai ke damunsa, ji yake tamkar kan zai fita saboda ciwo. "Kashe kanka zaka yi?" Shaheed Gwarzo ya faɗa da damuwa a muryarsa. Girgiza kai Rafeeq ya shiga yi "Babu abunda ya faru wanka nakeso nayi Yayaaaah." Da wata kalar murya da yasa Shaheed ɗin kallonsa sosai, ba zai iya tuna wane lokaci ne da Rafeeq Gwarzo ya kirashi Yaya saboda akwai kusan shekara ɗaya a tsakaninsu. Murmushi Shaheed ɗin ya yi yana shafa sumar kansa still yana kallon cikin fuskar Rafeeq ɗin wanda ya haɗe rai sosai tamkar bashi bane ya yi magana yanzu ba. "Dagaske baka da kirki wasu lokuttan, gaskiyar Yakumbo ne duk abinda take faɗa akan ka." Ƙara haɗe rai Rafeeq ya yi yana turo bakinsa irin yadda yara keyi ɗin nan. Girgiza kai kawai Shaheed yayi ya nufi ƙofa, juyowa yayi tamkar wanda ya manta wani abu yana riqe da ƙofa yake faɗin. "Ka kula da kanka banda wanka da ruwa mai sanyi." Bai jira me Rafeeq ɗin zai faɗa ba ya yi wucewarsa daman kuma ya san ba magana zai yi ba. Drivern gidan Aunty Bara'atu ne ya kawota har cikin harabar gidansu ya taimaka mata ta fitar da kayanta dake cikin Booth ɗin motar masu aikin gidansu sai sannu da zuwa suke yi mata, ɗaya daga cikin su suka ɗaukar mata bags ɗin ta zuwa cikin gida, ta juya tana yiwa drivern Aunty Bara'atu godiya kafin yaja mota yabar gidan. Hango motar Rafeeq cikin rumfar adana motoci tasan ya dawo kenan, a maimakon ta nufi ɓangaren su sai ta nufi ɓangaren su Rafeeq ɗin. Kasancewar da wuya ka tarar da kofar falonsu a rufe yasa kawai turawa tayi kamar kullum babu jira ai kuwa a buɗe take. Kai tsaye stairs ta nufa zuwa dakunan su na bacci dake jere da na juna, na Shaheed ne a farko sai na Rafeeq sa'annan na Moobarak Gwarzo. Har ta saka hannu zata yi knocking ko mai ta tuno kuma? Sai kawai ta wani ware fararen idanunta kafin ta yamutsa fuskarta gabanta na mugun faduwa dan har taga irin masifar da zai yi mata idan ya ganta. Batareda tayi knocking ɗin ba ta tura ƙofar room ɗin nasa. Tsaye yake gaban mirror dressing bayansa kawai take hangowa bata san me yake yi a tsaye ba. Tattaki tayi zuwa gabansa zuciyarta banda rawa babu abun da takeyi. Rungumeshi tayi ta baya tana kwantar da kanta a bayansa tana zagaye hannayenta a kirjisa, a hankali ta kira sunansa cikin taushin murya. Yasan ita ce kawai keyi masa haka duk cikin zuri'ar Gwarzo. Ji yayi wani abu nayi masa wani irin nauyi a kirjinsa. "Meyasa? meyasa zaki taho uhmm? meyasa kike wasa da zuciyata?" Ya faɗa murya can ƙasa, lokaci ɗaya kuma ya dawo da ita zuwa gabansa. Zata buɗe baki tayi magana kenan ya shiga jan hannunta, tasan duk lokacin da ya yi mata hakan tom ba ya son magana da ita ne, kuma ba zai yi magana ba. Har kofar ɗaki ya jata ta langabe kai tana kallonsa da fararen idanunta da suka fara tara hawaye. Sai da ya fitar da ita daga cikin bedroom ɗinsa sannan ya rufo ƙofar gamida murza mata key batareda da ya kalli fuskarta ba, yasan kallon fuskarta kawai zai ƙara hargitsa sa. Faɗawa ya yi kan bed yana wani irin jan numfashi, tun tea da yasha da safe babu abunda ke cikin sa, har abinci Aunty ta aiko masa dashi duk da ba shiga cikin gidan yayi ba, ya san Shaheed ne ya faɗa mata dawowarshi. Jikinta ya yi sanyi kiris ya rage ta fashe da kuka kawai ta fice daga side ɗin. Tana shiga parlor da Haneefa ta fara cin karo wacce ke kai da kawo acikin parlon duk da Shaheed ya tabbatar mata da cewar lafiyar Rafeeq ɗin ƙalau iskancinsa ne kawai, amma zuciyarta ta kasa samun natsuwa so take Yakumbo ta kauda kai ta zagaya taje ta gano halin da Rafeeq ɗin ke ciki duk da tasan halinsa bazai kulata ba. Maimoon ta rungume Haneefa gamida mintsinarta ganin tamkar hankalin Haneefa ɗin baya jikinta. Ɗan ihu Haneefa ta saka tana faɗin. "Kefa muguwa ce ta karshe." Dariya Maimoon tayi ta ɗage mata gira tana faɗin. "Lafiya ke kaɗai a parlor tamkar wata maigadi, ina Yakumbo?" Lokaci ɗaya ta jera mata tambayoyin. "Tana daki, kinga daman Yaya Rafeeq ne." Kallonta Maimoon keyi kafin Haneefa ta faɗa mata a yanayin yadda ya shigo gidan. Ɗan tabe baki tayi wasu lokuttan Haneefa na bata haushi wasu lokuttan kuma tana tausaya mata. Kai tsaye ɗakin da Yakumbo take suka nufa dukansu, tun kafin su isa Maimoon ke kwala mata kira. Zama Maimoon tayi tana gaisheda Yakumbo da respect, itama Yakumbo da fara'a ta amsa mata tana tambayarta makaranta kafin ta ɗora da faɗin. Wai ko anyi auren haka zata riqa gantali daga Kano zuwa Zaria shi mijin nata tayi ya ya dashi? Dariya Maimoon tayi tana faɗin. "Muna tare dashi Yakumbo ai yana da gida Zaria acan, so zan zauna idan ya samu lokaci sai yaje mugaisa." Yakumbo ta girgiza kai cike da takaici take faɗin. "Wannan auren babu komai acikinsa sai gantali, ai daga ranar da Haneefa tayi aure toh ta gama boko, sai dai kuma a zauna a gidan miji ai ta ibadah." Murmushi kurum Maimoon tayi kafin Yakumbo ta ɗora da zancen kayan lefenta akan sunyi kyau, tana ta sakawa Abdulwahab albarka, tana kallonta take faɗin. "Amman zuwa anjima zaizo mu gaisa kou?" Murmushi Maimoon tayi cike da jin kunya gamida miqewa tsaye tana fadawa Yakumbon cewa zataje ta watsa ruwa zuwa anjima zata shigo. Tare suka fita da Haneefa. Ɓangaren Aunty ta shiga suka gaisa kafin su nufi ɗakin Maimoon ɗin. Waya ta fitar ta kira daddy ta shaida masa dawowarta, haka ta gwada lambar Abdul-Wahaab har lokacin amma a kashe. Sako ta tura masa akan idan ya buɗe wayar ya kirata ko ya shigo zuwa anjima suyi magana. Bai san Shaheed Gwarzo bai da hankali ba sai yau, taya zai shigo masa da mace har a cikin ɗakin baccinsa? da sauri ya dauko jallabiyyarsa cikin closet ɗinsa ya saka ajikinsa. Wani irin kallo Zeeee take yi masa mai cike da buri kala-kala. "Zainab muje parlor." Ya faɗa yana ɗaukar wayarsa dake kan bed batareda ya kalleta ba. A parlor suka zauna ya kalleta yana faɗin. "Baki faɗa min zaki zoba Zeeee, bakya tunanin wani ya ganki anan musamman ma daddy mezaki ce?" Ta girgiza masa kai tana faɗin. "Na kasa hakura ne Rafeeq tun jiya baka kirani ba kamar yadda kayi alkawari shi yasa da mukayi waya da Shaheed ya faɗa min an kawo kayan auren Maimoon nace zanzo na yiwa Aunty Allah ya sanya alkhairi sai na ganka." Kasancewar Aunty ta san Zainab ɗin kuma Shaheed yana yawan faɗawa Auntyn cewa budurwar Rafeeq ce. Wani irin kallo Rafeeq yake yi mata dan takaici yama kasa yi mata magana jin wai tazo ne ta yiwa Aunty Allah ya sanya alkhairi kan kayan auren Maimoon Gwarzo. Kenan tana farin ciki da auren da Maimoon ɗin zata yi tabarshi?
Itace fa mutum ta farko wacce tasan yadda Maimoon Gwarzo take da kusanci a cikin zuciyarsa. Miƙewa tsaye yayi ya nufi kofa ganin haka ta miqe tabi bayansa jikinta har wani irin rawa yake dan ta kamo hannunsa ya yi saurin kaucewa hakan. Cike da kunya ta saukar da kanta ƙasa tarasa gane mai yasa bata iya controlling kanta akan soyayyar Rafeeq Gwarzo. Kusan a tare suka shiga babban parlorn. Maimoon ce da Haneefa a parlorn sai Aunty dake waya, daga Maimoon har Haneefa kallonsu suke yi da wani irin yanayi kwance acikin fuskokinsu. Ganin yadda kallo ya dawo kansu Rafeeq yasa ya yi wani irin rikicewa ji yake tamkar ya koma baya, dan da yaga Shaheed Gwarzo a wannan lokacin yana iya kwada masa mari saboda duk laifinsa ne, banda iskanci idan wajen Aunty Zee ɗin tazo da gaske meyasa ba zai kaita wajenta ba dole sai ya kaita wurinsa. Wani irin sanyi yaji ƙafafunsa sunyi masa. Karasawa suka yi cikin parlorn Zainab ta samu wuri ta zauna daga Haneefa har Maimoon babu wanda ya ce ta zauna. Shima Rafeeq zama yayi kan hannun kujerar da Zainab ɗin ta zauna yana danna wayar hannunsa yana jin yadda idanuwan Maimoon da Haneefa ke yawo akansa. Sai Zainab ɗin ce tayi karfin halin yiwa su Maimoon magana duk da sanin ta girme su dan zata basu shekaru biyu haka ta kada girmanta ta masu magana. Dukansu babu yabo babu fallasa suka gaisheta, wani irin kallo Rafeeq ya juyo yana musu daga Haneefa har Maimoon ɗin daidai lokacin kuma Aunty ta gama wayar da take cike da fara'a take yi musu magana. "Ashe ka dawo?" Ta faɗa tana kallon Rafeeq cike da kulawa, ba tare da ya yi magana ba take kallon Zee Liman dake gaishe da ita. Yana ɗago idanuwansa suka haɗa ido da Maimoon zai janye suka sauka kan fuskar Haneefa yai saurin janyewa, Aunty ya kalla yana cewa. "Ga Zainab nan a nuna mata kayan zata gani." Cike da walwala Aunty ta kalli Haneefa tana cewa. "Yauwa Haneefa sai ki yi musu jagoronci har da Maimoon ɗin tunda itama bata ga kayan ba har yanzu." Sai da ta ɗan yi murmushi sannan tace. "Kai ma Yaya Rafeeq ai baka gani ba sai ku kalla tare ko?" Ya wani haɗe rai ba tare da ya kalli kowa ba yake faɗin. "Bana kallan lefe." Dukkansu babu wanda bai kalleshi da mugun mamaki a fuska ba, Maimoon kuwa turo baki tayi tana cewa. "Amma Yaya ko bakaga na kowa ba ai kaga nawa." Wani kishi ya sake taso masa, ko zai ga kayan lefen kowa a cikin duniyar nan ba zai kalli na Maimoon ba indai ba wanda ya kawo mata bane da sunan zai aure ta. Haushi ne ya sake kamashi wato ita hankalinta ma a kwance yake ko? Wai shin bataga yana fushi da ita bane da har take san ya kalli kayan auranta wanda akan guy ɗin ta wulakanta shi? Mtsww yaja tsaki a karo na farko tare da gyara zamansa da alama ko kulata ma ba zai yi ba. Haneefa ta miƙe tsaye farin ciki ne ya kamata jin Aunty tace harda Rafeeq ɗin za a shiga ganin kayan, ko babu komai zata sake samun kusanci dashi na ɗan wani lokacin. "No Aunty bazan gani ba." Muryar Rafeeq ta bugi kunnuwansu. Ganin ya dage akan ba zai ga kayan ba yasa Aunty cewa to su suje su gani, Zee da Haneefa kawai suka miƙe yayin da Maimoon ta sake turo baki ji take kamar ta fashe da kuka, Yaya Rafeeq baya murna sam da abinda ya shafi bikinta kuma bata san dalili ba. Zee da Hanee suka wuce room ɗin Aunty ta kalli Maimoon tana faɗin. "Ki bisu mana ko har yanzu kunyar bata sake ki ba?" Ta ƙarasa faɗa tana dariya. Bata ce komai ba gabaki ɗaya hankali da tunaninta suna akan Rafeeq da ko kallo bata isheshi ba. Tashi ma ya yi cikin sauri ya nufi kofa dan dama jira yake a yakice masa Zee ya gudu saboda baya san wani dogon bayani a wannan lokacin. Jiki a sanyaye ta bishi, a jikinsa yake jin ana binsa sai dai ko waigowa bai yi ba bare yasan ko waye. "Yaya." Ta kirashi yana gab da shiga part ɗinsu . Gabansa ta ƙarasa hawaye taji suna zubar mata saman kyakkyawar fuskarta wanda bata damu da goge su ba take cewa. "Yaya Rafeeq why? Duk ka tsaneni ko ganina ma baka sanyi, yanzu Yaya ace kayan auran ƙanwar taka ma bazaka gani kasa min albarka ba? Yaya idan kuna min irin wannan a ina zan samu jin daɗi? Babu Mommma a cikin rayuwarmu ,Yaya Mubarak baya nan daga kai sai Yaya Shaheed nake gani naji sanyi da nutsuwa. Kayi hakuri nasan na ɓata maka rai tahowar da nayi . Yaya bazan iya ɓata muku rai ba kai da Wahaab hakan yasa kawai na hau motar haya na dawo Kano, kai Yaya na ne, shi kuma shine zai zama mijina cikin kwanaki kaɗan. Zuciyata tana ganin kodai dan kana ganin ba Mommma ta haifeni ce ta haifeka ba shi yasa kake kin kula wasu al'ammuran nawa." Kalamanta sun tabasa , da sauri ya kalleta yana wani ware idanuwansa akan fuskarta dake zubar da hawaye. Hannunta ya fisgo yajata suka nufi ciki bai tsaya ba sai a tsakiyar parlor. Hannunta ya saki ya shiga zagaye parlorn yana tunanin abinda zai ce mata saboda takaici. "Moon.!" Ya kirata muryarsa a raunane. Bata amsa ba sai dai ta ɗago ido tana kallonshi still hawaye basu dena zuba ba. "Wace kulawa kike bukata daga waje na? Wace irin kulawa ce bana baki a matsayinki na ƙanwata? Wannan zuwan da nayi Zaria dan waye naje? Moon!" Ya sake faɗar sunan cikin san ƙarin bayani. Maimoon ta kasa cewa komai saboda wani haushin kanta da takeji, gaskiya ya faɗa wane irin kulawa takeso ya bata? Toh amma haka kawai taji tana buƙatar duka wani motsinsa akanta, tana so ya dena fushi akan duk laifin da zata yi masa wanda babban burinta tana so ya shigo cikin harkarta da Abdul-Wahaab har a kaita gidanshi wannan shine burinta da takeso Rafeeq ɗin ya cika mata. "Saboda wancan saurayin naki shine zaki baroni a zaria ki taho? Wayeshi? And me zai iya yi dan kin biyoni mun dawo gida?" Yayi maganar yana furzar da wani hucin bakin ciki. "Iyakaci yace ya fasa auranki mexai faru idan ya fasa ya faɗa cikin daga murya da zafin rai? Ai bashine kawai namiji a duniya ba, baku dace bama sam idan ya tafi wani ƙwaƙƙwaran zai zo ya aureki." Durkushewa tayi a gurin tana sake fashewa da kuka. Sosai kukan nata yake hargitsa shi, hannu yasa ya riƙo shoulders ɗinta ya maida ita kan sofa ta zauna. "Me yasa kike irin wannan kukan Moon?" Ya faɗa da muryarsa mai sanya kasala, Maimoon ta shiga goge hawayen tana cewa. "Ban ganin kowanne namiji a matsayin mijina irin Abdul-wahab bamalli shine kalar mijin da nakeso Yaaya, please ka gaya min me yasa baka san gani na dashi? Idan wani abun yai maka toh na ari bakinsa ina mai baka hakuri Yaya, wallahi ina jin wani iri akan rashin jituwarka dashi. Taya za a ce wanda zai zama mijina basa shiri da Yayana danake matukar kauna? Ina jin zafin hakan a zuciya ta." Wani irin shock ne ya kamashi tunda ta fara maganar, cak ya yi a wajan ya kasa koda motsi da yatsan kafarsa bare yabar gabanta yadda yaji zuciyarsa na zafi da wani irin kishi. Ya akai ya makara wajan koyar da Maimoon soyayyarsa ta aure? Rashin zaman su tsawon shekaru kusa da juna ya janyo masa wannan giɓin, yanzu ya zai yi ya goge Wahaab daga cikin zuciyarta? Hannu yasa tare da jan kyakkyawan karan hancinsa yana rintsa ido. Kallanta yayi itama shi take kallo kallo da fuskar shagwaɓa wanda yasa Rafeeq saurin ɗauke kai. "Kije wajan bakuwarki." Ya faɗa cikin ɗauke kai. Baya ta juya masa tana turo baki take faɗin. "Yaya wai wannan itace zaka aura? Ni bata min ba wallahi ta fiye buɗewar ido." Kamar jira yake tayi maganar dan ta sosa masa inda yake masa kaikayi yace. "Nima Wahaab beyi min ba, idan kika canza shi nima zakiga canji." Ware ido tayi kamar zatai kuka take faɗin. "Wahaab ba irin ta bane shi yana da kunya." Da alama hirar ta fara yi masa yadda yake so dan ta hakan ne zai juye bakin cikin dake ransa. Wajan tv ya nufa yana cewa. "So hana ganin laifi kenan, shi yasa bakya ganin laifinsa. Zee kuma so ne yake sanyata zuwa duk inda tasan zataji sanyi a ranta." Maimoon ta mike tsaye sanye take cikin riga da skirt na wani pink lace tayi kyau sosai daurin ɗankwalinta ya zauna akanta kamar ɗorawa akai ta nufi ƙofa tana cewa. "Kunfi da cewa da Hanee Yaya, kuma ko babu komai zamuji daɗi idan ka zaɓe ta matsayin matarka, gida bai koshi ba ai ba za'a kai dawa ba." Cikin sauri ya isa wajan ta yana yi mata wani irin kallo, turo baki tayi ganin ya tare hanyar, ji tayi yana cewa. "Keda zaki auri wani a waje gidan ne ya ƙoshi?" Maimoon ta juya ido, "Wahaab shine namijin da xuciyata ta karbesa a matsayin mijin Aure . ni bana san auran zumunci ma." Gabansa ne yai wani irin bugawa wanda har sai da Maimoon taga canzawar yanayinshi. Kamar yace mata koda ni nace zan aure ki? Sai kuma yaji nauyi dan wani irin kwarjini take yi masa idan yazo furta mata yanayin da zuciyarsa ke ciki.......ƳAN TAGWAYE BIYAR 2023
ƘASAITATTUN LABARAI MASU DAƊI DA SANYA NISHAƊI, SABON SALO MAI ƊAUKE DA DARRUSA NA RAYUWA UWA UBA ƘASAITATTUN SOYAYYA MAI HUDA JIJIYA.
IYALINA (A'ILATY)
RAFEEQ
MUNƊO
ZAMANIN MU AYAU
FATHIYYA.DOMIN SIYAR GUDA BIYAR N1500.
DOMIN SIYAR DAYA N400.
Account Details
2083371244
Zenith Bank
Aisha m salisGa MUTANEN MU NA NIGER 🇳🇪
Tura ta Nita
Da sunanAsma'u Buhari Aliyu
08086207764SAI KI/KA IS TURA SHAIDAR BIYA TA DAYA DAGA CIKIN NUMBOBIN NAN.
+234 808 620 7764
07065283730
+234 705 124 4211
+234 704 040 2435#ASMY B ALIYU
#HAJJA Ce
#Rafeeq gwarzo
#maimoon gwarzo
#Haneefa
#Zeee liman