*RAFEEQ....*
*PAID BOOK....* #400NA
*_ASMY B ALIYU_*
Da
*_HAJJA CE_*3..
Ɗaure da milk ɗin towel ya fito a ƙugunsa yana sake sharce ruwan da yake kwance a saman fuskarshi, kai tsaye closet nashi ya nufa ya zuge murfin wardrobe ɗin yana san tantance waɗanda zai sanya. Waɗanda suka kwanta a cikin zuciyarsa ya ɗakko domin ya daɗe beyi irin shigar ba. Gefe bed ya ajiye kafin ya isa wajan mayukansa masu matuƙar kyau da gyara fata, jikinsa ya shafe dasu sannan ya miƙe yasa kayan. Shigar riga da wando yayi na farar shadda wacce aka yi masa ɗinkin zamani masu gajerun hannuwa, ya janyo hularsa zannah bukar baƙa ya ɗorata akansa tare da isa wajan madubi yana gyara botir ɗin gaban rigarsa. Tsayawa kawai ya yi yana zubawa tsari da kuma kamala irin wacce ubangiji Allah ya zuba masa, yasa hannu yanajan dogon karan hancinsa da ya ƙara ƙawata kyaun fuskarsa sai wani buɗe idanuwa yake kamar mai san gano wani abu a cikinsu. Rafeeq Habeeb Gwarzo kenan matashi mai ji da taƙama, uwa uba kuma kyawun da Allah subahanahu wa ta'ala ya zuba mishi. Sai dai abinda yake matuƙar bashi mamaki shine yadda yaga Maimoon Gwaro batayi masa irin soyayyar da yakeji a cikin zuciyarsa, kallansa takeyi tamkar yadda take kallan su Shaheed Gwarzo da suka fito ciki ɗaya. Juyawa ya yi a hankali ya zaro takalmi yasa ya ɗauki car key yafito. Kai tsaye wajan tsaleliyar motarsa ya nufa wacce Alhaji Mustapha Gwarzo ya sissiya musu, tashi black marsandi ta Shaheed kuma white sai ta Maimoon red color yayin da Mubarak sai ya dawo za'a bashi tashi. Yana ƙoƙarin shiga yaji zazzaƙar muryarta mai sauke masa duk wani noti dake ɗaure a jikinsa. Kallonta yake da dukkan nutsuwarsa har ta iso gabansa idanunshi suna zagaye jikinta. Sanye take cikin doguwar riga armless tayi matuƙar karɓar surar jikinta, kanta da hula kamar net ana hangen tarin gashin dake kanta. "Yaya sai ina kuma?" Ya riƙe murfin motar yana faɗin. "Unguwa." Wajansa taje itama ta riƙe murfin motar tana leƙa ciki, yadda kusancinsu yazo har yana jin ƙamshin turaren jikinta yana shigar masa cikin kai ne yasa shi faɗin. "Kina da saƙo ne?" Maimoon ta dago tare da kallansa da manyan idanunta farare tas tace. "Naga kasha kwalliya kamar wanda zashi taɗi, da alamar Auntyn tawa ƴar Nigeria ce, ko itace wacce naganku tare?" Cikin haɗe rai Rafeeq yake kallanta yana ƙoƙarin shiga cikin motar ya zauna yake faɗin. "Idan itace menene?" Maimoon ta samu kanta da haɗe rai, cikin yatsina fuska take faɗin. "Batai min ba tun lokacin da na ganku tare, haba Yaya duk macen da zaka aura karka bari idanunta su buɗe da zuwa irin wajajan nan indai ba matarka bace ta aure. Kawai ni yarinyar batai min tun kallan farko dana ganku." Kallanta ya yi sosai yaga dagaske take maganar, sai da ya murza key a jikin motar yake cewa. "Waye ya zaɓar miki Abdul-Wahaab?" Tambayar tazo mata a wani irin yanayi, ta turo baki tana wani kifta idanuwa take cewa. "Wahaab daban ne Yaya Rafeeq, ita kuma waccen daga gani bata da kamun kai." Cikin tsuke fuska ya kalleta zai yi masifa sai kuma yaji ya kasa, yasa hannu zai rufe motar Maimoon ta riƙe tana cewa. "Dan Allah karkaje wajan yarinyar nan baku dace da juna ba sam." Fizgo ƙofar yai ya kalleta yana cewa. "Kema ai baki dace da wanda zaki aura ba, so kowa yaje yaji da matsalarsa bye sai na dawo." Yaja motarsa da ɗan karfi har Maimoon tana saurin yin gefe guda ganin kamar zai mangareta. Har sai da ya fice daga cikin gidan sannan ta juya ta koma ciki tana jin takaici indai har wajan wannan yarinyar zashi, bedroom ta wuce ta ɗauki wayarta tana daddanawa. Rafeeq na fita kai tsaye wani store ya shiga, kayan masarufi yasa aka jidar masa yasa a booth ɗin motarsa sannan ya nufi gidan marayu dake nan cikin ƙwaryar Kano. Daman tun ba yanzu ba Rafeeq yake zuwa kai taimako hakan yasa duk masu gadi da masu kula da gidan suka sanshi, ko baya cikin ƙasar yana turo da kuɗi ayiwa marayu abinda sukafi buƙata. Mutum ne shi da abin hannunshi baya rufe masa ido, yana matuƙar jin daɗi a duk lokacin da yayi irin wannan zuwan, yakan ji duk wata damuwa tashi Allah yana yayewa. Ɓangaren bebaye masu buƙata ta musamman aka fara rakashi, cike da tausayawa ya dinga shafa kawunansu yana sake godewa ubangiji da ya kaishi hannun Alhaji Mustapha Gwarzo, banda haka yasan shima da Allah zai iya kawo gidan nan yayi rayuwa makamanciyar da yaran nan keyi. Sai da aka rakashi ko'ina sannan ya fito ya bada umarnin sauke kayan dake cikin booth tare da yin alƙawarin kawowa yaran da suke under 6years suturar sakawa dan ya lura tayiwa yaran karanci a jikinsu. Yana cikin tuki yaji wayarsa na ringing, janyota yayi daga inda ya ajiye yana dubawa yaga mai kiran nashi, kamar bazai ɗauka ba sai kuma ya daure yai daga batare da yace komai ba. "Jan aji ma da yazo wajanka sai da ya sara maka, uhmm kana ina ne?" Ɗan yatsina fuska yayi kamar tana kallansa yake cewa. "Tuki nakeyi." Yanayin yadda taji yana maganar ne yasa ta gane baya cikin walwala, Zee Leeman ta kuma kashe murya cikin san janyo hankalinsa take cewa. "Ina Ado Bayero mall ko zaka ƙaraso?" Kalaman Maimoon ne ya faɗo masa inda take nuna masa cewar ba ajinshi bane yawan fita da mace zuwa wajan shaƙatawa wacce ba muharramarsa ba. Sai dai kuma shi mutum ne mai yawan san fita outing, yana so yaga yana zagawa cikin duniya dan ya dinga ganin yadda rayuwa take garawa. Karya kan motar yayi yana cewa. "Ganinan zuwa." Katsewa sukayi yana wani rintsa ido gani yake kamar bayajin shawarar ƴar uwar tashi, sai dai kuma in har beje wajan Zeee ɗin ba to babu wani waje da zashi, gida ne kuma ko yaje babu abinda zai yi a can ɗin. Tunda ta hangoshi takejin wani irin farin ciki yana cika mata zuwa, lokaci ɗaya kuma ta miƙe tare da nufowa inda yake. Kallan juna suka tsaya yi Rafeeq ya ɗage mata girarsa guda ɗaya alamar "Lafiya?" Handbag ɗin dake hannunta ta janyo tare da rungumeta a kirji. "Muje ko?" Ta faɗa tana nuna masa hanyar shiga wajan wasanni, shi yayi canji sannan suka biya suka shiga gurin.
Kai tsaye wajan zama suka nema suka zauna, Rafeeq yana karaɗe idanuwansa a wajan tamkar wani bako. Zee Leeman da takejin wata irin soyayyarsa tana taso mata takai hannunta tare da riƙo nashi, kallanta yayi sosai kafin ya janye idonsa acikin nata idon yaji tana faɗin. "Na ƙagu naji kace zaka fara zuwa gidan mu dan su san da matsayinka , amma kai sai naga kamar baka shirya aure na ba why?" Ya sauke wani irin numfashi yana zare hannunsa daga cikin nata yake cewa. "Zee har yanzu kin kasa gane inda zuciyata ta dosa, please mubar maganar auran nan yanzu." Cikin yanayin damuwa take sake kallansa, tana so ta gane sonta ne bayayi ko kuwa dai shirya yin aure yanzu ne baiyi ba? Gabaki ɗaya bata gane inda zuciyarsa ta nufa akan alaƙarsu, baya mata wulakanci haka kuma soyayya yake yi mata tamkar yadda saurayi da budurwa keyi. "Kasan ni macce ce Rafeeq, rayuwata kalilance zan so ace duk wannan zaman da mukeyi da kai ya zama mata da miji ne mu. Dan Allah baby ka shirya ka fara zuwa gidan mu su Abba su san da zamanka." Kallanta yake yi cike da tausayawa, yana jin mugun nauyinta akan yace ba itace a cikin wannan zuciyar ba. Maimoon gwarzo ta riga ta gama cika xuciyarsa da soyayyar ta"Kayi shiru baby kodai baka sona ne?" Ya kalleta da mayun idanunsa masu kama da madara farare tas dasu yake cewa. "Tun farkon haɗuwar mu dake nace ki daina yi min maganar aure saboda bana so kiyi tunanin zan aureki, Zee bana san yaudara a cikin tsari na shi yasa nake ce miki idan har kin samu wani wanda hankalinki ya kwanta dashi toh ki amince masa kiyi auranki. Zuciyata tana cikin wani irin yanayi wanda na rasa ta yadda zan ɓullo masa. Kiyi min addu'a kawai Allah ya cika min buri na." Hawaye suka fara zirarowa daga cikin idanunta, yana kallanta ta gefen ido haka kuma yana jin kukan nata har cikin jininsa saboda shi a rayuwarsa baya kaunar yaga ana kuka nan da nan yake jin tashin hankali. "Kana tunanin idanuwana zasu iya ganin wani bayan kai? Rafeeq idan wata ce a cikin zuciyarka ka gaya min hankalina zai fi kwanciya, idan kuma wani hali ne nawa da baka so ka sanar dani sai na gyara, wallahi zan gyara Rafeeq indai akan farin cikinka ne."wani irin karayewa xuciyar Rafeeq tayi lokaci ɗaya ya Xaiyi da Zainab idan ya fallasa mata sirrin dake cikin xuciyarsa xai iya karya xuciyarta.tun farko bai so wannan kusancin nasu ba,bai so tafiar su ta kawo nan ba duk laifin shaheed gwarzo ne da ya ta cusa masa ita alhalin ba itace aransa ba.haka kuma baya so ya cigaba da boye mata ,idan aka cigaba da tafia a haka xatayi wani tunani daban ne akan wanda ke ransa.
Damke hannunsa yayi yana kallonta da dukkan idanunsa,wani irin bugawa xuciyar zeey keyi a wannan lokacin tana jin bugawar da zuciyarta take har cikin tafin ƙafarta.A hankalin ya kamo hannunta abunda bai tabayi ba tsawon rayuwarsa riqa hannunta ,runtse idonta tayi xuciyarta na bugawa fisge hannunta tayi lokaci ɗaya ta fashe masa da kuka tana girgixa kai take faɗin"dan Allah karkace banice a ranka ba Rafeeq' xan iya mutuwa ka taimakeni karka fadamin dan Allah.
Ta fada tana kara sakin kukan da Rafeeq gwarzo keji har cikin xuciya da ruhi,Dukansu Abu ɗaya suke nema Amman kowane nasa ya banbanta da na dan uwansa,Zainab liman tana sonsa wanda ya lura a shirye take da ta sadaukar da farin cikinta saboda shi,shi kuma maimoon gwarzo ce acikin tashi xuciya shekaru goma sha takwas a baya ,wanda xuciya da gangar jiki basu taba gajia ba.banbancin shine yana son maimoon gwarzo Amman bata ma san yanayi ba,yasan xainab na tsananin sonsa da kaunarsa,sai dai shi kuma ba itace a tashi xuciyar ba dukan su suna cikin matsala.Hannu yasa yana squeezing sumar kansa gefe ɗaya kukan Zainab na hargitsa masa lissafi..Zainab goge hawayenki muyi magana,ya faɗa sounding so very cool cikin muryarsa, tissue ta fiddo acikin handbag nata tana goge hawayen idonta still wasu na kara fitowa...#ASMY B ALIYU
#HAJJA CE
#Rafeeq Gwarzo
#Zeey leeman
#Team tagwaye Novel