*PAID BOOK#400*TEAM TAGWAYE NOVEL'S
NA
*_ASMY B ALIYU_*
DA
*_HAJJA CE_*14
Addu'ar da yake yi ce kurum ta ƙarasa dashi cikin Mustapha Gwarzo mantion, ko parking motar bai yi da kyau ba drivern gidan yazo ya qarbi car key ɗin ganin yanayinsa aransa yake faɗin. "Shi dai wannan yaron abubuwansa kullum babu sauqi sai yayi ta abubuwa tamkar mai jinnu akansa." Rafeeq kam da gaske yana son ya bar Nigeria tsakanin gobe da jibi, kuma shirun daddy ya tabbatar masa da bai amince da wannan tafiyar tasa ba. Ganin yadda aka fara gyaran gidan nasu sannan mutane sun fara kai da kawo acikinsa yasa shi kuma shiga tashin hankali. Kai tsaye part ɗinsu ya nufa tun a hanya ya shiga cire botir ɗin shirt ɗin dake jikinsa yana jin yadda yake haɗa zufa ta ko'ina acikin jikinsa. Addu'a kawai yake Allah yasa Moobarak baya babban parlor dan bazai iya sauraren rigimarsa ba, yanzu yana bukatar zama shi ɗaya. Wata doguwar ajiyar zuciya ya sauke ganin Shaheed ne kawai a parlorn da suits ajikinsa da alamar daga office ya dawo, bottle water ne a hannunsa har ya buɗe marfin zai kafa kai yasha Rafeeq ya shigo cikin parlon, kallonsa yake yana nazarin yanayinsa. Ɗaga masa hannu kawai Rafeeq yayi ya nufi stairs yana kin yadda su haɗa ido da Shaheed ɗin da ya bisa da kallo yana son Rafeeq ɗin ya kallesa. Kusan karo sukaci da Moobarak Gwarzo da ya ware ido yana kallonsa. Tsakiyya suka saka shi kowanne yayi folding hannunsa akan kirjinsa suna kallon Rafeeq Gwarzo. Da wata irin rigima da yake hangowa cikin fuskar kowanensu ya ɗan haɗe rai. "Da gaske yau muna so muji damuwarka Yah Rafeeq, wai shin menene ainahin abinda ke damunka? nasan dai ba matsalar kuɗi bane saboda daddy yana da kuɗi haka kuma kai ma kana dasu muna dasu, and ba matsalar rashin jin daɗi bane dan bakayi kalar wanda ke zama cikin wahala ba, ni nafi tunanin matsalarka kamar akan mace ne dan tun dazun da ka daukoni a Airport nake nazarin hakan a tattare dakai. Maimoon Gwarzo tace ka daina damuwa da ita gabaki ɗaya kabi ka canja mata kamar ba favorite brother ɗinta ba why Rafeeq?." Shaheed Gwarzo ya ƙarasa maganar da wani yanayi tattare da muryarsa. Dafe kai yayi yana kallonsu da idanunsa da suka daɗe da canza kala. Yana jin yadda kirjinsa ke wani irin bugawa kansa ma wani irin ciwo yake yi masa, hayaniyarsu damunsa takeyi. "Kayi magana dan Allah Yaaya ko za'a samu solution." Moobarak Gwarzo ya faɗa yana kamo hannun Rafeeq Gwarzo yana damkewa cikin nasa hannun, kaunarsu mai girma ce , wacce basu farata cikin sauqi ba. Shaheed gani yayi idanun Rafeeq ɗin kamar suna juyewa lokaci ɗaya kamar so yake ya faɗi. Da sauri Shaheed ya taroshi jikiinsa yana kiransa a gigice. Kwantar dashi sukayi kan bed Moobarak na tallabe da kansa ya saka masa inhelar suna ƙoƙarin numfashinsa ya dawo daidai. "Ko dai mu kirawo daddy?" Moobarak Gwarzo ya faɗa cikin tashin hankali. Girgiza kai Shaheed Gwarzo ya shiga yi yana faɗin. "Karka kirashi ka ɗaga masa hankali. Ka duba cikin bedside akwai injection ɗin da ake yi masa." Da gudu Moobarak ya ƙarasa wajen, daukosu yayi daya bayan daya yana duba date din dake jikinsu sai da ya tabbatar da suna aiki sa'annan ya haɗa ya yiwa Rafeeq ɗin. Har lokacin suna tare dashi kusan minti goma suka fara jin saukar numfashinsa, Moobarak ya ɗora kansa akan pillow ya kalli Shaheed Gwarzo yana faɗin. "Ya samu bacci Yaya." Ɗaga kai kurum Shaheed yayi kusan tare suka baro cikin room ɗin gamida rufo masa ƙofar. "Wai mema zai kaishi yin soyayyar da zai riqa wahala har haka? nasan kuma wannan yarinyarce wacce kuka yi school tare mema sunanta? meyasa zata yi soyayya dashi idan tasan bazata iya kula dashi yadda ya kamata ba?." Moobarak Gwarzo ya faɗa cikin tsawa da ɓacin rai a muryarsa. "Kayi a hankali Moobarak kar ya tashi." A fusace ya sake cewa. "Akan me zanbi a hankali Yaya? yanzu idan ka bincika ma yaudararsa tayi shi yasa ya shiga cikin wannan yanayin, kasan mata ko kaɗan basu da amana basu da kirki idan suka ga wanda yafi ka, ni wallahi naga ma kokarinsa, bazan iya daukarwa kaina abunda zai hanani jin daɗin rayuwa ba." Ya ɗauki car key akan center table dake tsakiyar parlon ya wani sha toka yana kallon Shaheed Gwarzo dake tsaye yana kallonsa tamkar shine babba yake faɗin. "Muje gidansu Yaya, Idan har na bincika naga taci amanarsa ne, wallahi tallahi sai tayi da nasanin sanin Familyn Gwarzo, sai nasa an ɓatar da duka dangin su." Cikin sauri yace. "Kaifa wata rana baka da hankali, kusan halinku ɗaya da Rafeeq idan kuna ɓacin rai. Waya faɗa maka Zainab ce ta ɓata masa rai? waya faɗa maka Zeeee zata iya cin amanar Rafeeq?" Girgiza kai Shaheed gwarzo yayi cike da rashin yarda da tabbatarwa yake faɗin. "A yadda Zeeeee ke son Rafeeq zai yi wuya ta ɓata masa rai , sam ba matsalar Zeeee bace na faɗa maka haka, mubarshi zuwa dare sai mu lallaɓasa ya faɗa mana idan bai faɗaba muyi masa barazanar zamu haɗashi da daddy, kasan daddy shine babban weakpoint ɗinsa. Ba wai duka Moobarak Gwarzo ya yadda da maganganun Shaheed Gwarzo bane, a'a yayi shiru ne kurum dan yace su jira zuwa dare.
Da yammah sosai Yakumbo ta iso da ƴan uwanta gidan sai qara ciki yake masha Allah kowa ka gani a cikin farin ciki yake. Gabaki ɗaya ranar Maimoon bata saka Rafeeq a idonta ba, ta kirasa kuma da safe bai ɗauka ba, tun safe tana tare da maigyaran jiki a ɓangaren Aunty, har Yaya Shaheed ta kira a waya dan ya haɗasu a wayar ya faɗa mata cewa shi yana office. Haka ta hakura sai bayan magrib da Moobarak ya shigo gaishe da Yakumbo taja hannunsa gefe ta riqe hannunsa tana kallonsa da idanunta tamkar zatayi kuka take faɗin. "Yaaya Rafeeq fa?" Ya ware mata ido yaja dogon hancina, bai faɗa mata gaskiyar abinda ya samu Rafeeq ɗin ba dan yasan zata iya ɗaga hankalinta. "Kin san halinsa baya son mutane ya fita tun da yamma." Da haka ya samu ya kwantar mata da hankali. Suna dawowa sallar isha'i ganin baiga Rafeeq a massalaci ba yasa ya nufi room ɗinsa kai tsaye, sai dai ga mamakinsa baya cikin room ɗin. Wayarsa ya fitar ya kirasa, ringing ɗaya ana biyun ya ɗauka. "Ina ka shiga?" Lokacin Rafeeq Gwarzo yana kwance a hotel room ɗin da ya kama yana jinyar zuciyarsa tamkar yasan abinda Moobarak ɗin ke shirin yi kayansa ya haɗa cikin qaramar bag ɗan idan ya cigaba da kallon Maimoon Gwarzo tana shirin zama matar wani bashi ba zurciyarsa zata iya bugawa shi yasa kawai ya yanke shawarar killace kansa a ɗakin hotel ko zai samu sauqin abunda yakeji aransa. "Kana ina ne Yaya zanzo na sameka?" Girgizawa Moobarak Gwarzo kai ya shiga yi tamkar yana ganinsa a zahiri yake faɗin. "Zan dawo zuwa anjima." Cike da kulawa yace "Amman kasan baka da lafiya koh?" Moobarak ya faɗa cike da ƙaraya a muryarsa. "Nasani zan kiyaye Baraak." Yana kiransa da hakan ne mafi yawancin lokuta. Ajiyar zuciya Moobarak ɗin ya sauke yana faɗin. "Ka kula dan Allah." Ɗaga kai kurum Rafeeq yayi batare da yayi magana ba. Yana sauke wayar kiran Zainab ya shigo wayarsa, har ta katse bai ɗaga ba, kiran da tayi masa ya kai goma amma babu wanda ya ɗaga aciki. Kiran na katsewa ya kashe wayar duka yana jin kansa na sarawa. Har washe gari da za'a saka Maimoon a lalle wayarsa a kashe take, wannan karon shirin zuwa office yayi cikin shigar italyn suite kalar ash wanda suka karɓi jikinsa sosai, aikin da ya fara tarawa kansa na kwana biyu a office ya fara ragewa dan kawai ya samu Maimoon Gwarzo dake cikin zuciyarsa ta fita daga ransa amman ko wane saukan numfashi da yake yi Maimoon Gwarzo ce manne a zuciyarsa. Karshe ma ture files ɗin dake gabansa yayi saboda ya kasa yin aikin, daura kansa yayi akan desk yana ƙoƙarin saita kansa.
Su Moobarak kuwa, ganin Rafeeq bai kwana a gidan ba yasa da safe suna breakfast Shaheed ya kalli Daddyn nasu cikin girmamawa ya kira sunansa. "Daddy." Alhaji Mustapha yana rike da fork yana cin ɗanwake ya kalli Shaheed ɗin alamar yana saurarensa. "Yaya Rafeeq kamar yana cikin damuwa fa, jiya ma ba a gidan nan ya kwana ba baya yiwa kowa magana yanzu sai dai ya keɓanta kansa bamu san menene ba." Shiru Alhaji Mustapha yai yana nazari a cikin zuciyarsa. Tabbas Rafeeq yana da damuwa to amma mecece? Tun randa yace yana son tafiya chaina bayan ya fita yai masa transfer kudi zuwa account ɗinsa duk ya ɗauka ko matsalar ta danganta da rashin kudi. Amma yanzu tunda aka ce bai kwana a gidan ba hankalinsa ya tashi ya fara tunanin meke faruwa? Ko kaɗan baya so yaga abu ya samu Rafeeq yanzun nan zai ce maraya ne ba'a so ana ɓatawa marayu rai. "Kinibabban yaro kawai, toh me aka yi masa? Ni wallahi da aure akai masa kowa ma ya huta, idan wacce zai aura ne babu zan iya taimakawa a haɗashi da Haneefa." Yakumbo tayi maganar sounding so very serious da sauri Maimoon da Haneefa suka kalli juna farin ciki a fuskar Haneefa ba'a cewa komai. Murmushi Maimoon tayi ganin mafarkinsu zai cika ko babu komai idan Haneefa ta auri Rafeeq kusancinsu ba zai yi nisa ba. "Abari dai aji abinda yake damunsa yakumbo kar muje mu shiga hakkinsa." Yakumbo ta ware idanuwa tana kallon Alhaji Mustapha take faɗin. "Magana ta kare ba sai an wani biye masa ba, rana da lokaci kawai za'a sanya." Daddy dan a zauna lafiya yasa, shi cewa. "Toh shikenan ai." Daga haka gurin ya kaure da surutu kowa da abinda yake cewa a game da wannan hadin na Rafeeq da Haneefa, duk sunji daɗi ba kamar Maimoon da ta san yadda Hanee ke mutuwar son shi. Koda Daddy ya tashi yayi ta kiran wayar Rafeeq akashe, sai kusan karfe biyu da rabi na rana sannan ya sake kira. Lokacin Rafeeq ya baro office yana jin wani zafi saboda saƙon da ya buɗe yaga Zee ta turo masa. "Daddy ina yini?" Alhaji Mustapha yace. "Kazo gida ina son ganinka yanzu." Tunda yaji yanayin Muryar Daddy yasan su Moobarak sun kai masa gulma. Tuƙi kawai yake yi zuciyarsa na sake tafasa, idan ya tuna saƙon da Zainab ta turo masa sai yaji me yasa ma bai yi mata tsinannan duka ba a lokacin da ta fara kawo mishi shawarar nan? Mai ta maidashi akan soyayyar da yake yiwa Maimoon? Haushin kansa yakeji da har ya bari Zee ɗin tasan asalin sirrin zuciyarsa gashi har ta fara bashi gurguwar shawara. Da wani irin tashin hankali ya isa Gwarzo mantion, shawarar da Zee ke sake bashi tana sake rugurguza shi harma ya rasa inda zai saka ranshi yaji daɗi. Side ɗinsu ya nufa idanunsa dake ganin dishi-dishi su yake ta rintsewa yana sake buɗewa a hankali. "Yaayaah " Yaji muryar Maimoon daga bayan shi, nan take kirjinsa ya buga yana jin yadda bugun zuciyarsa ya canza. Sake runtse idon yai har zai tsaya yaji me zata ce masa sai kuma ya cigaba da tafiya dan baiga abinda zai yi mata ba a yanzu. Itama Maimoon ganin yaki tsayawa yasa ta haɗe rai su Haneefa da Zee leeman da sauran matan dake cikin rumfar suna kallanta kamar zasuyi da dariya ganin yadda takeyi masa magana cike da rigima. Tafiya yaci gaba dayi har ya isa kofa, da sauri ta shige ganin yana shirin rufe ƙofar. Rintsa ido kawai Rafeeq yai jin kusancinsu da juna, ta tsaya a gabansa tana canza fuska. Buɗe idon yai yana wani haɗe rai da kalar da bata taɓa zaton yanayin irin hakan ba. "Yaya Rafeeq ko wani laifin nayi maka ne?" Tayi maganar tana kafe shi da manyan idanuwanta. "Idan wani abu nayi maka da ya sanya kaƙi shiga cikin harkar bikina dan Allah kayi hakuri kuma ka sanar dani ko menene sai na baka hakuri kuma na kiyaye gaba. Komai na bikina baka shiga ba Yaya, duk ka tsame hannunka babu wani abu da kake yi min, ni gaskiya bana jin daɗin hakan Yaya Rafeeq. Yanzu anyi ankon shadda na ƴan uwa maza da lace na mata ƴan uwa kowa yanayi kai banji kace komai ba. Yaya Shaheed da Yaya Moobarak duk sun min abubuwan gudunmawa kai shiru ko tsintsiya baka siyo kace Moon ga gudunmuwa ta , taya zanji daɗi Yaya Rafeeq?" Ta faɗa hawayen da take ta riƙewa suka fara zirarowa akan tattausan kuncinta da fatar take sheƙi saboda gyara, bata damu da gogewa ba saboda halin da take ciki na ɓacin ran watsi da Rafeeq yayi da lamarinta ba wanda yafi komai yi mata zafi. Zuciyarsa ce ta sake hargitsewa ganin yadda take kuka ya sake rintsa ido. Shin meke damunsa ne? Yanzu me zai ce mata? Meye laifinta tunda bata san mugun son da yakeyi mata ba? Kallanta ya yi itama shi take kallo da sexy idanunta masu cike da rikici, itace ta fara ɗauke nata dan ba zata iya jure yi masa irin wannan kallon ba na cikin idanuwa. Gaba ɗaya magana sai tayi masa mugun wahala a gurin, bakinsa yaji yayi nauyi ya kasa ce mata komai. Room ɗinsa ya nufa da sauri yana sake jin zuciyarsa na san azalzalarsa, shaiɗan ya fara kwaɗaita masa bin shawarar da Zeee Liman ta bashi akan Maimoon ɗin, gashi yanzu da ya ganta sai yaga ta canza ta sake yi fresh sai walwali takeyi da wani ƙamshi na musamman. Kuka ta fashe da shi saboda a rayuwarta tana san taga ƴan uwanta maza suna bata muhimmanci a cikin lamarinta, wannan abubuwan na Rafeeq yana sanya ta tunani kala-kala, komai nashi ya canza cikin ƙanƙanin lokaci. Ta juya zata fita sukai karo da Moobarak, kallanta yai cike da mamaki kafin ya fara kallan cikin parlorn wai ko zaiga wanda ya sanya ta kukan. Ganin babu kowa yasa shi cewa. "Keda waye?" Maimoon ta cije baki. "Ba Yaya Rafeeq bane ba, wallahi ya canza duka Yaya Moobarak yadda kasan ba a cikin family ɗin Gwarzo yake ba." Ta faɗa tana share hawayen. "Ki rabu dashi ai mun gayawa Daddy insha Allah komai yazo karshe zai dena." Up stairs ɗin ta kalla tana sake turo baki, da kyar Moobarak ya lallaɓata ta hakura ta tafi wajan ƙawayenta. Yana shiga room ɗin ya rufe ƙofar tare da jingina bayansa a jiki yana sauke numfashi. Tunawa kawai yake sun kusa rabu sai kuma lokacin da tazo gidan shida ya ganta. Anya akwai abinda yafi ciwo irin na kana son mutum so irin wanda yake yiwa Moon ya kasa faɗa? Yana da tabbacin wannan ciwon yafi kowane ciwo a duniyar nan. Kenan Zeee ma tana cikin wani hali tunda tana sonshi yayin da shi kuma baya santa haka ake rayuwa ko kuwa dai sune aka tsarawa hakan? Tunawa da yai Daddy na jiransa yasa shi saurin rage kayan jikinsa. Wanka yayi ya sake kaya zuwa wani yadi ruwan zuma da akai masa ɗinki mai gajeran hannu, sosai yayi kyau abinka da dama shi ɗin mai kyau ne. Turarukansa dake jere wajan mirror ya fesa sannan ya fito zuwa side ɗin Daddy. Koda ya fito babu wanda ya kalla a cikin compound ɗin, kai tsaye babban parlor ya nufa nan kuma su Yakumbo ne da ƴan uwa dole yaje ya gaishe dasu suna ta yi masa tsiya amma ya share su ya nufi ɗakin Daddy. Knocking yayi kusan sau uku sannan aka buɗe masa, Daddy ne da kanshi wanda da alama daga toilet ya fito. "Shigo daga ciki." Daddy ya faɗa yana bashi hanya. Rafeeq ya shiga yana jin wani mugun tashin hankali dan besan me Daddyn zai ce masa ba.........ƳAN TAGWAYE BIYAR 2023
ƘASAITATTUN LABARAI MASU DAƊI DA SANYA NISHAƊI, SABON SALO MAI ƊAUKE DA DARRUSA NA RAYUWA UWA UBA ƘASAITATTUN SOYAYYA MAI HUDA JIJIYA.
IYALINA (A'ILATY)🔥
RAFEEQ🔥
MUNƊO🔥
ZAMANIN MU AYAU🔥
FATHIYYA.🔥DOMIN SIYAN GUDA BIYAR N1500.
DOMIN SIYAR ƊAYA N400.
Account Details
2083371244
Zenith Bank
Aisha m salisGa MUTANEN MU NA NIGER 🇳🇪
Tura ta Nita da sunanAsma'u Buhari Aliyu
08086207764SAI KI/KA ISAR DA SHAIDAR BIYA TA ƊAYA DAGA CIKIN NUMBOBIN NAN.
08086207764
07065283730
07051244211
07040402435#Asmy b Aliyu
#Hajja ce
#Rafeeq Gwarzo
#Moobarak Gwarzo
#Team Tagwaye