*PAID BOOK*
NA
_*ASMY B ALIYU*_
DA
*_HAJJA CE_*Tunda yaji muryar Daddy a cikin ɗakin sai kawai yaji duk gabaki ɗaya ana sake hargitsa masa ƙwaƙwalwarshi, ya sake curewa cikin duvert tare da rintsa idanuwa yana sauke wahalallan numfashi. Alhaji Mustapha ya ƙarasa wajan bed ɗin tare da sanya hannunsa ya yaye duvert ɗin jikinsa yana ƙarewa ɗan marayan yaran nashi kallo. "Rafeeq meke damunka haka?" Maimakon yayi magana kawai sai ya fara ƙoƙarin tashi zaune, Shaheed ya taimaka masa ya jingina bayansa jikin gadon yana furta. "Gajiya ce kawai Daddy kuma na kasa yin bacci." Cikin tsananin tausayawa Daddyn ya sake taɓa forehead ɗinshi, jin zafi sosai yasa shi cewa. "Wannan zazzabin na jikinka yafi ƙarfin ace na gajiya ne kaɗai, ka buɗe bakinka kasanar dani ainahin abinda yake damunka, ko kanada wanda ya fini ban sani ba?" Cikin sauri Rafeeq ya shiga girgiza masa kai yana cewa. "Haba Daddy har akwai wani da zaifika a gurina? Please kayi hakuri idan na ɓatamaka rai." Ganin yadda ya wani gigice ne yasa Daddy cewa. "Shikenan naji yanzu dai karɓi tea kasha Dr Arham yana hanyarsa ta zuwa gidan nan ya dubaka." Shaheed ya shiga miƙa masa tea cup ɗin ya karɓa tare da kaiwa bakinsa. Wani amai ne ya taho masa, kafin kace wani abu ya fara sakinshi a duka jikinsa. Alhaji Mustapha ya riƙeshi a jikinsa yana matse mishi shoulder yake faɗin. "Subahanallahi wannan wane irin ciwo ne yake damunka?" Hankali a tashe Shaheed ke cewa. "Da alama ba wai zazzabin bane kaɗai." Daddy ya jinjina kai. Wayar Shaheed ce ta fara ringing ya zarota daga cikin aljihu, Dr Arham ya gani ba tare da ya tsaya ba ya fice daga ɗakin yana amsawa. Tare suka shigo cikin ɗakin, a lokacin Alhaji Mustapha ya shiga gyarawa Rafeeq jikinsa wanda gabaki ɗaya ya rasa duk wani ƙwari na jikinsa. "Yauwa Dr bari na saka masa riga sai ka duba shi." Ya faɗa yana buɗe wardrobe ɗin kayan Rafeeq ɗin. Riga da wando na bacci ya zaro masa suka sanya masa shida Shaheed, sannan suka taimaka masa ya bar kan gadon wanda bedsheet ɗin ya lalace da amai. Cikin soofa yake ƙoƙarin kwanciya suka hanashi, Daddy yace a maidashi room ɗin Shaheed kafin a gyara masa nashi. Sosai Dr Arham ya duddubashi kafin ya rubuta wata allura da magani sai kuma drip da za'a yi masa sakamakon rashin kuzarin da bashi dashi, sannan jikinsa yana buƙatar hakan saboda babu abinci a cikinsa. Kallansa kawai Alhaji Mustapha keyi yana faɗin. "Yanzu sabida Allah meyake shirin haifar maka da heart attack Rafeeq? Ko dai wani abin ake yi maka wanda ka kejin babu daɗi a cikin gidan nan? Ka sanar dani zanyi maganin abin da yardar Allah." Rafeeq yai shiru yana jin zuciyarsa na wani irin bugawa, yasa hannunsa cike da dauriya ya kamo na Daddy yana kuma rintsa ido. "Alhaji ku tsagaita da yi masa yawan tambayoyi yanzu, duk wani abu da zai yi dogon bayani yanzu a ɗan barshi har mu samu zuciyarsa ta daidaita, yanzu bari naje a ɗakko allurar da sauran abubuwan da za'ayi masa, kafin na dawo a samu ya ɗan ci wani abun koyaya yake kafin na zo." Cike da sauraro Alhaji Mustapha ya amsawa Dr, yana fita ya kalli Shaheed yana cewa. "Shaheed kira mai kula da side ɗinku ya gyara room ɗin Rafeeq yanzun nan." Babu ɓata lokaci kuwa Shaheed ya fita ya sanar dashi kafin ya koma ɗakin ya zauna sukaci gaba da jiran Dr. Kai tsaye wajan dining room ta nufa inda aka gama shirya breakfast, kallan wormers ɗin ta shiga yi kafin ta fara buɗewa dan ganin abubuwan da suke ciki. Kujera taja tare da janyo flask ɗin kunun madara ta zuba cikin glass cup, jin an shigo cikin parlorn ne yasa ta ɗan waiga kaɗan, Yaya Shaheed ne ya haye stairs still idanunta suna kan hanyar taga ya shiga ɗakin Daddyn su. Cikin sauri taga ya sake fitowa zai fice ba tare da ya kulata ba tayi saurin cewa. "Yaya Shaheed Daddy bayanan nima naje mu gaisa na tarar babu kowa." Cikin yanayin sauri yake ce mata. "Yeah muna tare dashi a wajan Rafeeq za'a sanya masa drip." Da sauri ta miƙe ganin ko tsayawa beyi ba tabi bayansa. Maimoon tasha mamaki lokacin da taga yanayin da Rafeeq ke ciki, ta dinga zaro ido cike da tashin hankali take tambayar Alhaji Mustapha. "Daddy me ya samu Yaya haka?" Alhaji Mustapha Gwarzo ya kamo hannunta ya zaunar da ita a gefenshi yana cewa. "Muma bamu sani ba kiyi masa addu'a kinji ko?" Jikinta yayi sanyi ta shiga leƙen fuskarsa da take a lumshe yana jan numfashi kaɗan-kaɗan. Hannun mahaifinta ta kamo cike da tsantsar damuwa take cewa. "Ikon Allah sai kace jiya ba muna tare da shi ba. Daddy haka mutuwa fa takeyi ko? Kuna tare da mutum lafiya lau sai kaji ance ya mutu." Alhaji Mustapha ya sake damke hannunta yana kallanta yace. "Haka ne auta . shi yasa a kullum ake son mutum ya dinga yafiya dan kar a mutu ana jin haushin wani ko wata." Sosai jikinta ya mutu da yanayin da taga ɗan uwan nata a ciki. Har aka gama masa allurar aka daura masa drip ɗin be motsa ba bare ya buɗe idanunsa. Yana jin duk wasu kalamai nata da suke fitowa daga cikin bakinta suna sauka a duka sashen jikinsa wanda har baya so yaji tayi shiru. "Shaheed kaci gaba da kula dashi bari naje sitting room zanyi baki." Cewar Alhaji Mustapha yana miƙewa tsaye ya fice daga cikin ɗakin. Maimoon ta koma wajan da Daddyn nasu ya tashi wato kusa da ƙafafuwan Rafeeq ta zauna har jikinta yana shafarsa yaji wani irin zirrr har cikin brain ɗinshi. "Kije kiyi breakfast ɗinki mana." Cewar Shaheed yana buɗe wardrobe ɗinshi. Da yanayin damuwa take cewa. "Wane irin breakfast zan iya yi Yaya Shaheed? Wallahi bazan iya ba yadda naga Yaya Rafeeq a cikin wannan yanayin." Rafeeq da idanunsa ke lumshe jin kalamanta ya sake jefa masa wata irin wutar soyayyarta a cikin ransa, ya dinga jin tamkar ya janyota zuwa cikin kirjinsa da yake jin tamkar zai rabe gida biyu. "Zaifi miki kyau dai kije kici karki janyowa kanki wata matsalar, kina gani dai shima harda ulcer da take damunsa." Girgiza kai tayi tana sake maida idanunta kan Rafeeq cike da tausayi take faɗin. "Jiya beci abinci ba ina kallansa." Rai a ɗan ɓace Shaheed yace. "Waike kin fimu damuwa da halin da yake ciki ne? Oya ki tashi ina san na kintsa a ɗakina kinzo kin zauna, sai kwana -kwana nake yi miki dan ki fita kin kasa ganewa." Maimoon ta juya tana kallan Rafeeq tana jin kamar idan har ta bar ɗakin wani abu marar daɗi zai iya samun shi, dan haka ta kawar da kai gefe tana cewa. "Yaya Shaheed ba wanka zakai ba? Taya za'a barshi shi kaɗai anan wajan, kawai kaje kayi ka barni na kula dashi." Baki wangale Shaheed yake kallanta, sai kuma ya juya ya shige bathroom bayan ya ɗauki ƙaton towel. A hankali ya shiga buɗe idanunsa ya ɗora su akan kyakkyawar fuskarta, bata san yana yi ba sakamakon wayarta da take faman dannawa suna chatting da Abdul-Wahaab. Kira ne ya shigo wayar ta ɗan saki murmushi tare da daga wayar ta kara jikin kunnenta tana cewa. "Wato chatting ɗin beyi maka ba dole sai munyi waya ko?" Rafeeq yaji kirjinsa ya sake yi masa wani irin nauyi, idanunsa suka sake ƙanƙancewa, zuciyarsa ta shiga yi masa zugi. Cikin wata irin murya Maimoon taji yana cewa. "Please get out." Jin yayi magana ne yasa tai saurin waigowa tana kallansa, sai dai idanunsa still a rufe suke. "Yaya Rafeeq magana kakeyi?" Yai mata banza sai lips da ya shiga cizawa da hakorinsa. "A'a bada kai nake ba nida Yaya Rafeeq ne bashi da lafiya." Cewar Maimoon tana sanarwa da Wahaab. Da yake bayajin abinda Wahaab ɗin ke cewa sai dai ita idan tayi magana yaji tace. "Eh shine bashida lafiya ka ganshi nan kwance ana masa ƙarin ruwa." Da salon muryar da yaji tana magana ne yasa shi kasa jurewa sauraranta, dan haka cikin azabar ciwo taji yace. "I said ki tashi ki fita." Tayi saurin kallansa da mamaki take faɗin. "Yaya Rafeeq wai dani kake ne?" Cikin tabbaci ya shiga ɗaga mata kai. Maimoon ta miƙe tsaye tare da ficewa tana turo baki.
Shiru ya ziyarci cikin ɗakin sai kuma yaji duk babu daɗi, ashe har gwara tana wajan yana jin motsinta hankalinsa yafi kwanciya. Yanzu kuwa da ta tafi sai yaji wani irin kunci, tsanar Abdul-Wahaab ta shiga cikin zuciyarsa ta zauna, duk da bai taɓa ganinsa sai da ya hango yanayinsa a cikin idanunsa ya kuma ji cewa Maimoon bata dace dashi ɗin ba. Shaheed ne ya fito yana ware ido ko zai ga Maimoon a cikin ɗakin amma baiganta ba, yaje ya murzawa ƙofar key sannan ya fara shirya jikinsa. Sai da ya kammala komai sannan ya ɗakko wayarsa ya kirata, bugu ɗaya ta ɗauka tana faman ɓata rai yace ta shiryo masa breakfast ta kawo masa ɗaki. "Zansa Lami ta kawo maka." Cike da mamaki Shaheed ke cewa. "Ke mekike yi da bazaki kawo min da kanki ba?" Maimoon ta sake cuno baki kamar tana gabansa take faɗin. "Toh ba Yaya Rafeeq ya koroni ba." Kallon inda Rafeeq ke kwance yayi ganin yadda yake tun ɗazu haka yake yanzu yasa Shaheed cewa. "Shida yake bacci tun ɗazu shine zakice ya koreki? Kinga malama idan bazaki kawo min ba ki barshi idan na shigo naci." Yana kaiwa nan ya katse tare da dire wayar yana jan ɗan ƙaramin tsaki. Rafeeq yana jinsa babu abinda yai masa daɗi irin yadda zata dawo ɗakin, yasa a ransa idan har tazo kawo breakfast ɗin bazai barta ta kuma fita ba bare taje suyi waya da Wahaab. Bakinta da sallama ta turo ƙofar da kafarta hannunta ɗauke da tray idanunta akan gadon da Rafeeq ke kwance. Tunda yaji isowarta shi kuma ya buɗe idonsa, kallanta ya shiga yi sanye take cikin wasu riga da wando Pakistan pink da ratsin white ɗin fulawoyi a jiki, tayi kyau sosai kai kace ita tayi kanta . Wajan Shaheed ta ƙarasa ta ajiye tray ɗin tana cewa. "Ni duk bansan abinda zakaci ba shi yasa kawai na zubo maka sinasir dan naga kamar shine ka daɗe bakaci ba." Shaheed na duba wasu book's yake cewa. "Kin kyauta kuwa sister dan a Cyprus ina mukaga wani sinasir." Ta juya zata fice Rafeeq ya buɗe baki a hankali ya kirata. "Moon." Tana jinsa amma tayi kamar bataji ba, sai da Shaheed ya kalleshi yana cewa. "Ah ashe ka farka? Maimoon Rafeeq na magana fa." Cak ta tsaya taki juyawa su haɗa ido saboda taji haushin korar da yai mata ɗazu. "Bakiji ba ne?" Shaheed ya faɗa da ɗan fushi ganin taki zuwa. A hankali ta juya ƙarasawa tayi wajanshi tana wani kifta idanuwa. "Zauna." Cewar Rafeeq idanunsa suna kanta. Gefen gadon ta zauna tana wasa da mayafin Pakistan ɗin jikinta. Idanunsa ya mayar ya lumshe, ta kalleshi cike da mamaki ganin bece komai. "Yaya Rafeeq gani fa." Ta faɗa cike da haushi a cikin muryarta, ya ɗan miƙa hannunsa da babu drip a jiki ya riƙo nata, ta kalli hannunwan nasu tana ware ido. "Kiyi zamanki naga kamar ɗazu kinji haushi right?" Cikin gaskiyarta tace dashi. "Sosai ma." Sakar mata hannun yayi yana sauke numfashi, kallosa take yana jinta har tsakiyar zuciyarsa yace. "Idan na mutu zaki damu?" Kafin tayi magana Shaheed yace. "Haba guy ya da wannan maganar kuma? Dan Allah ka dena maganar mutuwa sai munyi aure mun ajiye jikoki." Maganarsa tasa Maimoon tuntsirewa da dariya, yanayin yadda take dariyar cikin farin ciki shine ya haddasawa Rafeeq jin duk wani ciwo a jikinsa ya warke. "Wayaga Yaya Shaheed da jika ah." Ta faɗa tana sake fashewa da wata dariyar. Daga haka kuma sai duk ta manta da ɓacin ranta suka shiga hira duk da cewa Rafeeq baya sanya musu baki. Har ruwan ya ƙare Shaheed ya zare masa sannan ya maidashi ɗakinsa. Maimoon ce ta shiga bathroom ɗinshi ta haɗa masa ruwan wanka mai zafi, sai da ya shiga cikin bathroom ɗin sannan ita kuma ta fice zuwa sashen su...
#Asmy b Aliyu
#Hajja ce
#Maimoon Gwarzo
#Shaheed Gwarzo
#Dr Arham
#Haske writer's association...