_*ASMY B ALIYU*_
Da
_*HAJJA CE👈*_Unguwar sharaɗa dake ja'in can ya nufa. Tun kafin ya gama yin parking ya kirata yace gashi a bakin gate. Sanye cikin doguwar riga ta atamfa orange da ratsin coffee brown a jiki, ta yafa ɗan karamin vail wanda ya dace da shigar jikinta. A hankali ta isa inda yake tsaye jikin mota ya zuba hannayensa duka cikin aljihun gefe da gefe na rigar. "Shaheed Allah yasa dai lafiya dan gabaki ɗaya hankali na ya tashi." Kallanta ya yi yana tsuke baki, gyara tsayuwar yai tare da shafa kyakkyawan gemunsa da yake ta faman sheƙi. Sai da ya ja numfashi ya sauke kafin yace. "Ba gaisuwa?" Zee ta ɗan janyo murmushi wanda iyakarsa zaman leɓenta tace. "Sorry Shaheed ina yini..?" Amsa mata yai yana lasar lips ɗinshi da ya fara bushewa yake faɗin. "Ko ke fa, daman tambayarki nake so nayi, dan Allah Zee ki gaya min gaskiya meke damun Rafeeq? Yace min ɗazu kuka rabu but na ganshi cikin tsananin damuwa dan har asthma ɗinshi sai da ta tashi." Wani irin zaro ido Zee tayi tana dafe kirjinta da taji ya buga da wani irin mugun karfi. Cike da tashin hankali take kallan Shaheed tana faɗin. "Shi me yace maka?" Shaheed yai mata wani kallo yana cewa. "Da ya yi min bayani bazan zo wajan ki na tambayeki ba, just tell me Zee meke damun ɗan uwana?" Ruwan hawaye ne ya fara taruwa cikin idanunta, sai dai bata bari sun sakko ba gashi bata san a gane halin da zuciyar ta ke ciki. "Kinyi shiru Zee ko ba zaki gaya min ba?" Ta wani rintsa ido tana jin zuciyarta na bugawa, bazata iya cewa Rafeeq baya santa ba. Haka kuma ba zata iya tona asirin zuciyar Rafeeq ba tunda shi be bayyana ba, ita kawai ya sanarwa cewa yana son Maimoon. "Bansan menene damuwarsa ba, nima naga baya cikin walwala da jin daɗi lokacin da muna tare. Koda muka rabu ma yana cikin damuwa shi yasa na kirashi dan naji amma yaki ɗagawa shine dalilin kiran da kaga nayi maka ina tambayarka ko yana gida? Kace bari kaje ka duba." Shaheed ya shafa sumar kansa yake faɗin . "We have to figure out Zee, Ina tausayin Rafeeq abubuwa sun masa yawa, wallahi bana son kuma yazo ya dinga ganin ko dan iyayensa basa raye ne yasa duka waɗannan problem ɗin sukai masa yawa. Yana da heart problem ga ulcer sannan uwa uba asthma ɗin nan. Dan Allah Zee kiyi iya yinki wajan ganin kin cire masa tunani da kuma yawan shiga damuwa. Ya kamata ma ku fara maganar aure dashi, ko ke baki shirya ba?" Wani irin murmushi Zee ta saki wanda bayada alaka da farin ciki.tamka anyi mata dukan kawo wuƙa dan yadda zuciyarta takeyi kaɗai azaba ce. Taya zata sanar da Shaheed cewar ba ita Rafeeq yake so ba? Ya zata sanar dashi cewar ba ita Rafeeq yake so ya aura ba? Taya zata gaya masa cewar Maimoon ƙanwarsa, jininsa ita Rafeeq ke so yake kuma san ya aure ta? Yarinyar da kwarjininta kaɗai ya hanashi bayyana mata sirrin dake ransa. "Idan kina yin shiru Zee zuciyata babu abinda bata rayawa. Ki fito ki gaya min menene abinda yake faruwa? Dan naga alamar kinsan wani abu game dashi." Kallanshi tayi da sauri kuma ta janye ganin idanunsa na neman sanya ta fallasa abinda ba huruminta ba. "Sai dai idan kana ganin babu damuwa ka tafi dani wajansa ƙila ya iya gaya min." Wani irin buɗe idanu Shaheed yai yana faɗin. "Kai a'a Zee Daddy na nan, idan yaga kinje wajan Rafeeq har ya tabbatar da cewa ke budurwarsa ce zai iya fassaraki ko ya saki a wani matsayi marar daɗi. Kawai dai zanyi ƙoƙarin ganin kunyi waya dashi a yau. Sai ki bugi cikinsa da irin salonku na masoya." Ran Zee ya fara ɓaci da murya marar daɗi tace. "Mubar wannan maganar please." Ya jinjina kai tare da cewa. "Shikenan ni zan wuce." Ta ɗan matsa baya daga wajan motar tana cewa. "Agaida Maimoon." Yana murmushi jin an faɗi ƴar uwarsa yace zataji, ya shiga motar ya bar gurin. Juyawa itama tayi jiki babu kwari ta shiga gida. Tana shiga parlor ta tarar da Ammie ɗinsu ta fito daga ɗaki, harara ta zabga mata cikin ɓacin rai take cewa. "Kin fita wajan Rafeeq ɗin ne? Wai ni Zainab yaushe zaki yi hankali ne? Duk samarinki masu son auranki kinƙi basu fuska kin biyewa wancan yaron da ba shiryawa yayi ba ko? Toh bari kiji na gaya miki, tun wuri ki rabu dashi ki kama dahir, ga Salis nan babu irin nacin da baya yi akan ki bashi dama kinƙi. Last warning Zainab, kodai kice Rafeeq ya turo manyansa, ko kuma ki fita daga cikin rayuwarsa bana san sakarci." Tana kaiwa nan tabar wajan, Zee ta lumshe ido tana jin wani mugun tashin hankali. Ɗaki ta shiga da gudu ta isa wajan madubi jikinta yana wani irin rawa, kallan fuskarta tayi hawayen da take ɓoyewa suka shiga zirarowa saman fuskarta, kanta ta shiga kaɗawa side by side a fili take faɗin. "Wane cikas gareni da ba zaka iya aure na ba Rafeeq? Me yasa dole zuciyar ka sai Maimoon wacce ba ta san ma kana yi mata soyayya ba? Ina sanka Rafeeq domin ka riga da ka zama zuciya ta (Albi), ka so ni please Rafeeq kar ka barni cikin tashin hankalin rayuwa." Kamar daga sama taji ana cewa. "San maso wani ƙoshin wahala, kina cikin gararin rayuwa Zeeee" Da sauri ta waigo tana zare idanunta da suka yi jawur saboda kuka, ganin Sofia Yayar ta yasa ta juyawa ta fara ninke veil ɗin da ta ciro a kafaɗarta. Itama Yaya Sofia cikin rashin damuwa da ƙin kulawar da Zee ta bata yasa taci gaba da cewa. "Shi so dama haka yake idan bakai dace ba kamar dai yadda baki dace ba Zainab. Kina san Rafeeq amma shi bake ce a cikin tsarin sa ba, sai kiyi haƙuri ki kuma yi addu'a Allah ya kawo miki nagari mai sanki." Zee ta juyo kallan Yaya Sofia tayi cikin zafin rai take faɗin. "Kina so kice shi ba alkairi na bane? Yaya Sofia idan ba zaki min addu'a Allah ya bani Rafeeq Gwarzo ba kawai kiyi shiru kici gaba da zubamin ido." Sofia ta nufi wardrobe tana cewa. "Allah ya kyauta." Daga haka taci gaba da abinda ya shigo da ita ɗakin, yayin da Zee ta koma kan gado tana ci gaba da hawaye. Sai wajan karfe takwas na dare sannan ya iya fitowa daga side ɗinsu. Sanye yake cikin jallabiya hannunsa riƙe da wayarsa ya nufi cikin gidan. Dai-dai inda zaka shiga entrance ɗin gidan cikin baranda yaji muryarta da alama waya take yi da Abdul-Wahaab, ji ya yi gabaki ɗaya zuciyarsa ta wani hargitse saboda babu abinda ya tsana a duniyar nan irin yaga Maimoon tana waya da Abdul-Wahaab, gaba ɗaya sai ya waniji duk ya ruɗe. Tafiya yaci gaba da yi har ya isa wajan ƙofar shiga, yana ƙoƙarin murɗa handle yaji tayi masa magana abinda bai zata ba. "Yaya Rafeeq." Cak ya tsaya kafin ya ƙarasa buɗewa ya shige ciki dan idan ya tsaya tabbas zai iya yi mata abinda batayi tsammani ba. Maimoon ta rintsa ido Yaya Rafeeq akwai wulakanci ta rasa me yasa har ita wani lokacin baya saurarawa a cikin izzarsa. Kai tsaye kitchen ya shiga ya ɗauki electric kettle, kayan dafa black tea ya zuba a ciki ya jona sannan ya janyo kwai guda biyu yasa cikin tukunya yana dafawa kafin ya koma parlor ya zauna. Yana canza Channel zuwa ta resetlling ta shigo parlorn murmushi ɗauke a saman fuskarta. Wajan da yaje ta nufa, gabaki ɗaya ƙamshin khumran jikinta ya kusa hargitse masa kai, yai saurin miƙewa ya nufi kitchen. Bayansa tabi cikin shagwaɓe fuska tana masa magana. "Haba Yaya wai me nayi maka ne? Gabaki ɗaya ka canza min Allah zan gayawa Daddy, Yaya ku nake gani naji daɗi a rayuwa ta amma kai sai wani shareni kakeyi kuma bansan menayi maka ba." Maimoon ta ƙarasa maganar cikin yanayi na son fashewa da kuka. Sai da ya kashe kettle ɗin sannan ya dawo kusa da ita ya juya mata bayansa tare da durƙusawa alamar ta hau. Zaro ido Maimoon tayi tana ja da baya cike da mamakinsa take faɗin. "Yaya me zanyi haka?" Ɗan murmushi ya saki wanda iyakarshi saman leɓensa, ba tare da ya kalleta ba yace. "Goyaki zanyi yadda zaki gane cewa bana wulakantaki." Ya miƙe tsaya tare da matsawa dab da ita har numfashinsu yana bugar musu fuskar juna, ta sake turo lips tana kuma haɗe rai. Kallanta yake yi da dukkan nutsuwarsa yana jin tamkar ya shigar da ita cikin kirjinsa sai dai basu saba irin wannan wasan ba. Yatsunsa biyu yasa tare da ɗago haɓarta sukai kallan cikin ido, ta sake turo baki cikin yanayin shagwaɓa da ta gama zame mata jiki. Yadda tayi ba ƙaramin sake tayarwa da Rafeeq hankali tayi ba, cikin sauri ya janye hannusa yana komawa ya buɗe tukunyar da yake dafa kwan yana faɗin. "Ban san me kike so a waje na ba Moon." Cikin kitchen ɗin ta sake binshi tana leƙa tukunyar da yake tsaye a wajan, yatsina fuska ta shiga yi tana taɓe baki take faɗin. "Yaya maimakon ka soya kawai sai ka wani dafa? Ni bana son dafaffan ƙwai, ko zanci sai dai gwaiduwa." Yana tsamewa yasa cikin ɗan bowl mai ɗauke da ruwan sanyi yake cewa. "Dama ni bake na dafawa ba." Maimoon ta ware idanu tana kallansa, a jikinsa yaji cewar shi take kallo dan haka ya ɗago a hankali ya zuba mata sexy idanunsa cikin nata da suke farare kal. Ganinta kawai cikin kitchen tare dashi yasa shi jin tamkar a cikin gidan auran su suke tare. Da sauri ya juya, kofi ya ɗaƙƙo yaje ya zuba tea ɗin ya suba zuma a ciki, bowl ɗin ƙwansa ya ɗauka ya nufi hanyar fita daga kitchen yana cewa ta taho masa da gishiri. Yana gaba tana bayansa ganin zai fita dan ta ɗauka a parlorn zai zauna tace. "Yaya Rafeeq." Maimakon ya amsa sai ya juya yana mika mata hannu alamar ta bashi robar gishirin. Bayanta ta mayar da hannunta tana sake kura masa ido. Tafiya yaci gaba da yi tana binsa har suka isa part ɗin su, gab da zai shiga nashi yace da ita. "Bani kije ki kwanta dare ya yi." Da wata murya tace "Magana fa zamu yi Yaya." Kamar yace ba zai yi ba sai kuma ya shiga ciki, akan soofa ta zauna tana janyo bowl ɗin kwan nashi ta fara ɓare masa. "Yaya magana zamu yi daku kai da Yaya Shaheed but kaine kawai nake samu free Ya Shaheed tunda kuka dawo ƙasar nan Allah ya zuba masa yawo.." Wayar sa ce ta shiga ruri Maimoon dake kusa da wayar tasa hannu ta janyota. 'My Zeeee Shine sunan da yake maƙale a wayar, haka kawai ta samu zuciyarta dajin babu daɗi kawai ta zubawa sunan ido. Tashi yayi yaje wajanta tare da karɓe wayarsa, ganin mai kiran yasa shi kallan Maimoon yana cewa. "Kije ki kwanta gobe sai muyi maganar idan Shaheed ɗin ya dawo." Jikinta na wani irin tsuma irin na takaicin nan taci gaba da ɓare masa, bata kalleshi ba tace. "Kayi wayarka ni ina ruwa na daku. Zan jira ka gama muyi maganar." Har wayar ta katse bai samu ya ɗaga ba, sake kira akai yaje ya karɓi bowl ɗin daga saman cinyarta yana cewa. "Kije kar Aunty taga bakya nan, idan na kammala uzuri na zanzo sai muyi maganar." Afusace ta miƙe ganin yadda yake ta wani korarta daga ɗakin. Zagaye shi tayi zata fice kawai taji ya riƙo mata hannunta, ta sake tsuke fuska tana san ƙwace hannunta ya wani janyota zuwa right side ɗinshi bayanta na jikin kirjinsa tana jin bugun numfashinsa a gefen wuyanta. Hakan yasa taji ta shiga cikin wani mugun yanayi, husky voice ɗinshi ta daki cikin kunnenta yana cewa. "Sorry." Yana kaiwa nan yaja hannunta ya zaunar da ita cikin soofa shi kuma ya daga kiran. "Hello." Zee ta lumshe ido lokacin da muryarsa ta ziyarci cikin kunnuwanta. "Ina Maimoon?" Yaji ta jeho masa wannan tambayar, inda Maimoon ɗin take ya kalla yaga tana ci gaba da ɓare masa ƙwan yace. "Lafiya lau." Zeee taji wani irin zafi a zuciyarta sai kace ba ita ta tambaya ba ya bata amsa. "Ance baka jin daɗi duk soyayyar Maimoon din ce?" Hannu yasa yana shafa kyakkyawar fuskarsa tare dajan dogon hancinsa da ya ƙarawa fuskar tashi mugun kyau yace da ita. "Yeah." Ya faɗa mata iya gaskiyarsa. Wani irin kishi ya tasowa Zee ta daure duk da yadda zuciyarta ke zafi tana faɗin........
#ASMY B ALIYU
#HAJJA CE👈
#Rafeeq Gwarzo
#Maimoon Gwarzo
#Zee Leeman
#HANNU BIYU-BIYU