*RAFEEQ* 10

34 1 0
                                    


*PAID BOOK#400*

NA

*_ASMY B ALIYU_*
DA
*_HAJJA CE_*

10....

Lokaci ɗaya taga duk yanayin Rafeeq ɗin ya canja bata san me Daddy ya faɗa masa a waya ba, lokaci ɗaya ya yiwa motar key. Dukansu zaman shiru suka zauna a motar kowane da abunda ke cin xuciyarsa. A mafi yawancin lokuta idan taga yayi irin wannan shirun takan kyalesa ne da damuwarsa, dan duk yadda tayi dan taji damuwarsa ba faɗa mata zai yi ba. Takan yi mamakin mugun zurfin cikinsa a yawancin lokuta, baya faɗa sai dai wani lokacin tashin ciwon sa yana nuni da cewa yana cikin tsananin damuwa. Yana gama yin parking ta kallesa da dukan idanunta tana kallon tsantsar damuwa acikin fuskarsa wanda tun da ta tashi tayi wayau bata taɓa ganinsa haka ba, hasalima tun da suka dawo baya cikin walwala sosai. Maimoon ta kamo hannunsa ta riƙe cikin nata tana jin ranta duk babu daɗi ganin Rafeeq Gwarzo acikin damuwa. "Please Yaya komai zai yi dai-dai ka daina ɗagawa kanka hankali, naga akwai abinda ke damun ka da gaske, idan ba zaka faɗa min ba kayi ƙoƙari ka sanarwa Yaya Shaheed tunda shi namiji ne  idan wani abu ya sameka bazan taɓa yafewa kaina ba." Ta faɗa tana sakin hannunsa, yana kallonta da  wani yanayi kwance acikin fuskarta wanda ya kusan karya masa da zuciya. Har ta fice daga motar ta rufo masa ƙofar Rafeeq ya kasa furta mata kalma ko guda ɗaya, haka ya riqa sauke wata irin ajiyar zuciya yana jin wani irin ciwo a zuciyarsa  da take yi masa wani irin nauyi, haƙiƙa dan shi kaɗai aka halicce ta, dan shi kaɗai aka halartawa aurenta ba tare da wani ba, duk lokacin da ta ɗaga wayar Wahaab a gabansa yaji tana yi masa magana cikin salon da ko muryarta haramun ne Wahaab ɗin ya jita sai yaji zurciyarsa na wani irin narkewa. Wani sabon ciwo da tsananin kishinta da suka taru suka yi masa tsaye a rai. Wani murmushi ne ya subuce masa idan har wani namiji ne zai Auri Maimoon Gwarzo wanda bashi ba ya tabbatar da mutuwa zai yi. Motar ya yiwa key da wani irin yanayi yabar cikin makarantar, da addu'a da komai ya koma hotel ɗin da ya kama, kayansa ya ɗauka a mota daman yana yawan ajiye extra kaya a mota koda tafiya ta kamashi a irin wannan yanayin sai ya yi amfani dasu. Makulli yasa ya buɗe ƙofar ɗakin bayan ya shiga ya mayar ya rufe. Kai tsaye kayan jikinsa ya rage ya shige toilet dan yin wanka ko zai samu sauqin abinda yakeji a zuciyarsa. Maimoon kuwa koda ta shiga hostel bata tarar da Ayshaa a ɗaki ba sai kawai tayi amfani da key ɗin dake wajenta ta buɗe ɗakin nasu,sai lokacin taji tana jin wata irin gajiya mai haɗe da jin bacci. Kayan jikinta ta rage wanka kawai take bukata a wannan lokacin, wanka tayi daman tayi sallar Azzahar a hotel tare da Rafeeq, tana fitowa ta kalli agogo karfe 3 na rana, aikuwa ko baccin awa ɗaya ne sai tayi tasan zai isheta koda bata samu yin isashe ba kafin a kira sallar la'asar sai ta tashi. Haka akai tana gama shiryawa ta haye bed tayi kwanciyarta bata farka ba kuwa sai da aka kira la'asar ɗin. Sallah tayi sannan ta fara haɗa kayanta dan kar sai taje gida ta tuna ta baro wani abun a school. Bayan sallar isha'i Rafeeq ya yi mata saƙon sai da safe ba tare da ya kira wayarta ba, yana gudun karya kira yaji busy bayan yasan da wanda take yin wayar. Maimoon ta kiranshi taji a kashe, batayi tunanin komai a ranta ba ta ɗauka ko bashi da caji ne shi yasa ya kashe. Shi kuma a ɓangarensa muryarta kawai tana ƙara jefashi cikin wani kalar yanayi marar fassaruwa da wani sabon sonta dake ƙaruwa acikin zuciyarsa. Har kusan ƙarfe goma sha ɗaya na dare suna waya da Abdul-wahab wanda zuwa lokacin Aunty har ta turo mata da hoto da video na kayan lefenta ta gani. Abdul-Wahaab ya yi ƙoƙari sosai harda sarƙar gwal suka saka mata acikin kayan wanda kusan kala ɗari suka zuba na sutura only tradition attires banda ma english wears da da bags   daban. Aunty ta faɗa mata ta kira tayi masa godiya. Saƙo ta fara tura masa na yabo da godiya kafin taga kiran sa. Kalmar farko da ta fito daga bakinsa itace yabon menene ta tura da kuma godiyar menene meya faru? Wani numfashi take saukewa tana jin soyayyar Abdul-Wahaab na yawo a wurare da dama na cikin zuciyarta. Wata godiyar take ƙoƙarin yi masa, da sauri ya dakatar da ita ta hanyar cewa. "Bana so bana so dan Allah ki bari." Yanayin yadda yayi mata maganar yasa ta saki murmushin da yake jin sautinsa har ta cikin wayar, tasan kuma da gaske baya so dan ko kyauta yayi mata ta nuna jin daɗi ko tayi godiya sai ya yi mata rigima. Yanzu ma hirarsu ya canza dan sai da suka yi nisa da zancen da suke a wayar da dabara ta sanar dashi zuwan Rafeeq Gwarzo har take faɗa masa gobema tare zasu wuce kawai yayi tafiyarsa sai su hadu a Kano. Wani irin shiru ne ya ratsa a tsakanin su har ta ɗauka koya kashe wayar ne, ciro wayar tayi ta duba, ga mamakinta bai kashe wayar ba. "Dani dashi waye ya dace kibi? Baki san saboda ke na aje komai nawa na jiraki ba, shine zaki faɗa min cewa shi zaki bi? Wai yaushe ne zaki daina fifita farin cikinsa fiye da nawa?" Ya faɗa da wata irin murya tamkar bata Wahaab ɗin ta ba. "Ki jirani zanzo saboda tun farko baki sanar min ba, sannan kwana nawa ya rage a ɗaura auren mu ki daina ɓata min rai akansa?" Yana faɗin haka ya kashe wayar jiki a sanyayye tabi wayar da kallo kafin ta kara gwada kiran Abdul-Wahaab ɗin taji wayar a kashe, wani irin tsoro taji yana sauka a cikin zuciyarta ita kanta tasan Abdul-Wahaab yana hakuri. Yawancin lokuta akan yadda take nuna masa karfin da Rafeeq yake dashi a wajen ta. Haka bai taɓa faruwa a tsakaninsu ba, ta kalli Ayshaa dake kwance tana chart dan ba bacci take yi ba. Duk Ayshaa taji yadda suka yi da Wahaab a waya sai dai yadda take nunawa tamkar bata ma cikin ɗakin gabaki ɗaya dan ta riga ta aje matsalar Maimoon Gwarzo agefe in dai akan wannan Yayan nata ne mai mugun faɗin ran da isa. "Kina jina baki ce komai ba, dan Allah ki bani shawara Abdul-wahab ya kasa fahimta ta akan Yaya Rafeeq ban san ya zan yi ba yanzu." Buɗe ido Ayshaa tayi tare da ware hannayenta duka biyu take faɗin. "Ban san me zance ba Maimoon, abu ɗaya kawai na sani wallahi kina shiga hakkin Abdul-wahab akan wannan Rafeeq ɗin, ba zan fasa faɗa miki ba, yadda yake nunawa tamkar yafi iko dake akan Abdul-Wahaab. Abu ɗaya na sani karkiyi kuskuren da ba zaki iya gyarawa ba, wannan karon kiyi ƙoƙarin bin maganar Abdul-wahab ki fifita ra'ayinsa akan na Rafeeq Gwarzo tunda ba shi zaki aura ba, idan kina son zaman lafiya tunda har ya gaji yanzu ya nuna miki." Ayshaa ta ƙarasa maganar tana kallon Maimoon ɗin da ita take binta da kallo. Cikin wani yanayi mai cike da tsoro Maimoon ta shiga girgiza kai, tunani ta shiga yi ta ya zata yiwa Yaya Rafeeq wannan shirmen? Tasan idan har tayi duk randa ya gane tofa ba zai sake yadda da ita ba dan zai ce ta koyi karya. Gefen Abdul-Wahaab kuwa taga alamar ya yi fushi sosai, wannan lokacin so yake ya nuna mata karfinsa akan duk wani abu nata tunda shine zai zama miji a gareta kwanannan. Yanzu ya zata yi? Sam shawarar Ayshaa ba tayi mata ba, ta kuma san itama ta faɗa ne dan tana jin haushin halin Rafeeq ɗin. Jin batace komai ba yasa Ayshaa juyawa taci gaba da danna wayarta. Washe gari kuwa tunda wuri Maimoon ta shirya ta fice daga hostel ɗin bayan ta kwashe duk wani abu nata, Ayshaa ma sam ba ta san da fitar ta ba. Tunda ya farka daga bacci yake jin wani irin bugun zuciya, ya janyo wayarsa ya kunna tare da kiran Maimoon. Switch off yaji  yana ta kara gwada kiran still a kashe , tsaki Rafeeq ɗin ya yi tare da shiga bathroom, wanka ya yo sannan ya fito ya janyo kayan shafarsa dake cikin ƴar jakarsa mai matukar kyau. Yana shafawa yana sake kiran wayar Maimoon, wani ɓacin rai ne ya ziyarce shi yana kyautata zaton wajan yin waya da Abdul-Wahaab ne wayartata  ta mutu. Yaja tsaki tare da janyo wata dakakkiyar shaddarsa kalar sky blue yasa, ɗan ƙaramin cum brush ya ɗakko ya shiga gyara ƙawataccen bakin sajan daya ƙawata kyakkyawar halittar fuskarsa, ya yi kyau sosai ya janyo hularsa ya ɗora wacce ta ƙara fito da mutuntakarsa da wani irin kwarjini na musamman. Car key ya ɗauka da jakar ya rufe room ɗin, kai tsaye reciption ya wuce ya basu key ɗin ya wuce mota. Booth ya buɗe ya sanya jakarsa sannan ya buɗe mazaunin driver ya zauna tare da jan motar yabar hotel ɗin, ABU ya wuce yana faman addu'ar Allah yasa wayar Maimoon ta shiga amma still swtich off. Har ya isa cikin ABU ya kasa samunta a waya gashi bashi da lambar Ayshaa saboda yana ganin bashi da wani business da ita, yau kam yayi da ya  sanin rashin ajiye lambar wayar a gurinsa. Har wajan karfe goma na safe Rafeeq bai samu Maimoon ba, ransa ya gama tabbatar masa da cewa tabi Wahaab sun tafi, ransa yana suya yaja motar yabar makarantar yana jin wani irin zafi a ransa saboda ɓacin rai.
Abdul-Wahaab ma a nashi ɓangaren tunda gari ya waye yake kiran Maimoon amma a kashe wayarta, yayi mamaki sai dai ya ɗauka ko kunnawa ne batayi ba har lokacin. Koda ya iso school ɗin ya sake kiranta bata shiga ba, wayar Ayshaa ya kira bugu biyu ta ɗaga suka gaisa yake tambayarta. "Maimoon fa?" Cike da mamaki Ayshaa ta ware idanu kamar yana ganinta tace. "Wai daman baku tafi ba?" Wahaab ya dafe sitiyari zuciyarsa na masa wani irin suya jiyayi ransa yana tabbatar masa da cewa tabi Rafeeq saboda shine bata san ɓatawa rai. "Hello." Yaji Ayshaa ta yi magana, ya ɗan daure dan yau kam ba ƙaramin ɓata masa rai Maimoon tayi ba. "Ayshaa Yayanta tabi ko?" Ya faɗa muryarsa na rawa. "Gaskiya bazance ba amma dai naga duk babu komai nata a room ɗin nan." Cike da dauriya yace. "Shikenan Ayshaa sai anjima." Ko jiran abinda zata faɗa bai yi ba kawai ya kashe tare da cije lips, tabbas dole ya nunawa Maimoon kuskuran da tayi akan fifita Rafeeq dashi. Shima cikin fushi yaja motarsa yabar makaranta yana jin wani irin haushin Maimoon dan bata ɓata masa rai ba sai akan Rafeeq. Zaune tayi tare da zabga uban tagumi a cikin motar haya, gabaki ɗaya hankalinta ba a kwance yake ba, kawai ta zabi yin hakan ne wato tafiya a motar haya dan gujewa ɓatawa wani a cikin su Rafeeq da Wahaab. Tasan duk wanda yaji cewa da wane ta dawo sai ran wanda bata bi ba ya ɓaci. Tana sauka a Kano kai tsaye napep ta hau ya wuce da ita railway gidan Aunty Bara'atu wato kanwar mahaifiyarta. Da murna suka tarbeta cikin ƙanƙanin lokaci aka ajiye mata abubuwan ci da sha suna ta tsokanarta akan kayan lefen da sukaje suka gano masha Allah Abdul-wahab yayi matukar ƙoƙari. Ɗakin su Khauthar ta shiga, kai tsaye bathroom ta wuce tayi wanka, tana fitowa ta samu kaya marasa nauyi na Khauthar ɗin tasa. Parlorn ta sake dawowa nan fa aka ci gaba da hira sai dai zuciyar Maimoon tana wajan halin da Rafeeq zai shiga idan yaje school bata nan. Tasan Wahaab koyayi fushi idan ta shagwaɓe masa zai hakura ya kuma manta da laifin da tayi masa, amma Yaya Rafeeq ciwon sa kawai take ji dan tasan zai yi wahala bata janyo masa shiga mugun hali ba.
Ikon Allah ne kawai ya shigo dashi cikin  Gwarzo mantion, parking yai tare da rintsa idanuwa yana ɗora goshinsa jikin sitiyarin motar. Maimoon ta gama wulakanta shi ya kamata ya cireta aransa  musamman  yadda ta yarfa shi saboda Wahaab amma ina, sai kawai ji ya yi babu wanda ya sake tsana a cikin rayuwar shi irin Wahaab ɗin. Da kyar ya iya buɗe motar yana ziro ƙafa su Yakumbo da Haneefa tare da Shaheed sun shigo da alama wani wajan suka je. Wani irin daɗi ya kama Haneefa ta fara gyara fuskarta wacce take kunshe da fara'a. Ko kallansu bai sake yi ba ya rufe motar yana dafe da goshi ya nufi side ɗinsu. Cike da ɓacin rai Yakumbo da bata iya shanye fushinta indai akan Rafeeq ne tace. "Toh uban ƴan girman kan jaraba." Cak Rafeeq ya tsaya ba tare da ya waiga ba, wani irin haushi yake ji dan yasan yanzu zatai masa rashin mutuncin da ta saba. "Wato kai dai ba zaka sauya hali ba, tun jiya kabar gidan nan baka dawo ba sai yanzu, tsabar kai ɗin kaine ka ganmu amma bamu isheka kallo ba ko?" Yakumbo na magana tana ƙarasawa gabanshi, idanunsa da ta kalla ganin sun wani juye yasa gabanta bugawa. Baya taja hakan da Shaheed ya gani ne yasa shida Haneefa suka ƙarasa suma dan ganin abinda ya sanya Yakumbo ta razana. "Subahanallahi Rafeeq lafiya? Ina Maimoon ɗin?" Kasa cewa komai Rafeeq yai sai dafa kafaɗar Shaheed da yai yana wani iri a zuciyarsa  cije lips ɗinsa na ƙasa yayi . "Yakumbo ku wuce ciki bari na kaishi ɗakinsa yasha magani." Babu musu Yakumbo tayi gefe Shaheed ya kamo Rafeeq suna fara tafiya, cikin tashin hankali Haneefa zata bisu Yakumbo tasa hannu tare da janyota, harara ta zabga mata tana cewa. "Baki da hankali? Ina zaki bisu?"

#ASMY B ALIYU
#HAJJA CE
#Rafeeq Gwarzo
#Maimoon Gwarzo
#Wahaab Bammali
#Team Rafeeq#Tagwaye

ƳAN TAGWAYE BIYAR 2023

ƘASAITATTUN LABARAI MASU DAƊI DA SANYA NISHAƊI, SABON SALO MAI ƊAUKE DA DARRUSA NA RAYUWA UWA UBA ƘASAITATTUN SOYAYYA MAI HUDA JIJIYA.

IYALINA (A'ILATY)
RAFEEQ
MUNƊO
ZAMANIN MU AYAU
FATHIYYA.

  DOMIN SIYAR GUDA BIYAR N1500.

DOMIN SIYAR DAYA N400.

Account Details
2083371244
Zenith Bank
Aisha m salis

Ga MUTANEN MU NA NIGER 🇳🇪

Tura ta Nita
Da sunan

Asma'u Buhari Aliyu
08086207764

SAI KI/KA IS TURA SHAIDAR BIYA TA DAYA DAGA CIKIN NUMBOBIN NAN.

+234 808 620 7764
07065283730
+234 705 124 4211
+234 704 040 2435

RafeeqWhere stories live. Discover now