Chapter 26

377 35 20
                                    

URBAN-CITY CONSTRUCTION COMPANY
ABUJA-CENTRAL

Zaune suke a qaramin lounge na office din nasu yayinda take ba Marwa labarin abinda ya faru. She looked very confused, worried and disappointed all at the same time.

Marwa wadda ta zama so speechless shiru tayi tana kallon ta cike da tashin hankali.

Ilham dai a lokacin da ta fita daga gidan su Yasir babu abinda ta dinga yi banda addu'a domin kuwa gani take yi kamar Mamy zata sa securities din gidan su hana ta tafiya. Da sauri ta bar gidan kamar ana chasing dinta. Ko da ta fita tafiya tayi mai tsawo tana ta waige just to make sure she is safe. Sai da ta fita daga street din gidan ne ta samu wuri ta tsaya sannan ta fiddo wayarta ta kira bolt driver. Allah ne ya taimake ta he was very close don haka bata dade tana jira ba ya iso.

"Na rantse da Allah ban taba ganin mutum marassa tsoro ba kamar ke Ilham... How did you get the courage to speak to her like that??"

"hmmmm... wallahi nima ban sani ba Marwa. Abinda na sani shine bana iya jure wulaqanci a rayuwa na. Kin ga yadda take yi mun magana kamar trash?? da take magana fa at a point sai na fara tambayar kaina is she really his Mom because what was all that?? Ki hana yaron ki auren wadda yake so for your selfish interest"

"Toh ko bata so ya auri matar da zata qwace mata shi ne..."

"Kamar ya?? ita din auren shi take yi ne??? is she his wife??"

Marwa ce ta fashe da dariya yayinda tace "No Ilham... ina nufin gani take yi kamar the bond they share zai rage qarfi"

"Shine ta so ta hada shi aure da wadda baya so??"

"Maybe...."

"Imagine harda wani zagayawa da ni sashen shi wai duk don ta gwada mun bambanci tsakanin rayuwar da yake yi da nawa... she thinks kudin shi nake so. Da kudin shi nake so ai da yanzu na hada fortune daga aljihun shi, Ita batada labarin yadda na toshe duk wata hanya da yaron nata zai kashe mun kudi saboda that's not my priority??? Bata san cewar shi kawai nake so ba and not his money??? Na rantse da Allah matar ta ci albarkacin soyayyar da nake yi ma dan ta ne if not da ban san me zan ce mata ba"

Marwa wadda take murmushi ce tace "toh me ya rage da baki fadi ba Ilham?? Ke da kika ce tayi duk abinda ta ga dama..."

Ita ma Ilham tana murmushi tace "amma banda bin malamai da bokaye da kuma kidnapping..."

Marwa ce ta fashe da dariya tace "I can't believe you said that Ilham"

"I swear na fada ne saboda incase idan abinda take niyyan yi kenan tayi re-thinking. Her threat really scared me shiyasa nayi saurin tuna mata da Allah da kuma reputation dinta"

"Well, you actually did well gaskiya but tambaya na shine yanzu ya zakiyi??? zaki fadi mishi ne ko kuwa??"

Ajiyar zuciya Ilham ta saki sannan tace "Bana ji zan iya fadi mishi wannan abin kunyar da mahaifiyar shi tayi kuma bana so in fara kawo irin wadannan maganganun akan ta. Kar ki manta yana masifar sonta don haka bana so ya zama kamar I am trying to come between them. Ni babu ruwana da ita. I just love her son and Becoming Mrs Yasir Usman Bakura is my only priority"

"Toh idan ta fadi mishi fa??"

"Me zata fadi mishi?? tun farko da zata iya yi mishi magana ai da bata yi inviting dina ba..."

"Huh... You are too smart Ilham. Yanzu na gane abinda yasa Oga yake masifar son ki"

Kafin Ilham tayi magana ne Idris ya shigo cikin sallama yana riqe da manyan ledojin Cilantro a hannunshi.

Bayan sun gaisa ne ya ajiye ledojin tare da fadin "Hajiya Ilham ga abincin ki nan... idan da akwai abinda kike so sai ki kira ni don Allah"

Ilham wadda take murmushi ce tace "Nagode Idris..."

ILHAMWhere stories live. Discover now