Chapter 19

366 52 77
                                    

URBAN-CITY CONSTRUCTION COMPANY
ABUJA CENTRAL

A yau Monday zaune take a kujerar ta yayinda take kallon screen na Macbook dinta a zahiri amma kuma sam hankalinta yayi nisa... she looked totally lost.

A yau din ne Ilham tayi resuming aiki. Tun shekaran jiya after conversation dinta da Mummy ta sa ma zuciyarta salaama.. She actually fell in love with the wrong person and thank God she instantly realised cewar yayi mata nisa. Yanzu haka abinda zata yi shine tayi moving on and forget about him. Wannan ne ya sa jiya da Mummy zata je shago ta bi ta. A can din kuma da ta hadu da Nasreen da yadda take ta labarin auren su sai komai ya dawo mata sabo.

Wani ikon Allah ko da suka yi waya da Marwa suka yi hiran kayan lefen, bata fadi mata komai ba. Ita dai Marwa ta dage akan bata ji dadi ba don ta so ace ya qulla soyayya da Ilham din. Ita kuwa Ilham dariya kawai tayi and she made a joke out of everything and it all slid off. Mutum daya ce ta san halin da take ciki- Mahaifiyarta!

Wuraren qarfe Goma saura ne ya shigo office din. Kallo daya nayi mishi na gane akwai matsala. Yasir din da na sani mai fara'a wanda bayada damuwa ko alama ne na gan shi cikin tsananin damuwa da bacin rai. Gaba daya ma he looked like bai samu baccin arziki ba.

Basira ce ta tashi cike da girmamawa tace "Good morning sir"

"Morning Basira" ya fada ba tare da ya kalle ta ba.

Gani nayi ya kalli Ilham briefly sannan ya wuce ya shiga office dinshi. Ilham wadda hankalinta yayi nisa bata ma ji shigowar shi ba sai bayan ya shiga office dinshi ne Basira ta nufi wurinta tace "Anty Ilham yanzu oga ya shiga office dinshi baki gan shi ba"

Da sauri Ilham ta dago kai ta kalle ta tace "haba??"

Tun kafin ma Basira ta amsa ta shaida hakan domin kuwa qamshin turaren shi duk ya mamaye ko ina.

"Yes"

"Na sha'afa a wannan analysis din da nake yi da har ya shigo ban ma sani ba" ta fada yayinda ta wayance.

Murmushi Basira tayi tace "akwai abinda zan taimaka miki da shi ne??"

"No Basira thanks"

Daga nan Basira ta koma workstation dinta ta zauna.

Ajiyar zuciya Ilham ta saki yayinda ta dafe kai. Yanzu haka zata dinga ganin shi kullum a cikin office dinnan??? a yanzu ma da bai yi auren ba kenan.. Idan yayi auren fa?? Ta ya zata dinga kallon shi knowing cewar he will close from work and go back to his wife?? Can she handle this pressure???

Wayarta ce tayi ringing. Ko da ta duba sunan shi ta gani wanda har sai da ta dafe zuciyarta saboda bugawa da tayi.

Composing kanta tayi sannan tayi answering.

"Good morning sir" ta fada murya a sanyaye.

"Morning Ilham, please come" ya fada kai tsaye wanda ba tare da ya jira ta amsa ba ya kashe wayar.

Gani nayi ta bi wayar da kallo cike da mamaki. Me yake damun shi???

**************

Ilham ce ta qwanqwaso qofar office dinshi sannan ta shiga.

Gani nayi ta tsaya cak yayinda ta cika da tsananin mamaki. Wannan shine karo na farko da ta shigo office dinshi ta tarar da shi kwance a kan daya daga cikin kujerun lounge na office din shi.

Da sauri ta qarasa wurin shi hankali a tashe tace "Hey, me ya same ka?? meyasa ka kwanta?? are you...."

"Ya jikin ki? kin warke??" ya tambaye ta yayinda ya tashi zaune yana kallonta.

ILHAMWhere stories live. Discover now