NIKAAH
Marriage for Rent)By
HANAADY
(Rahama Aminu Bala)
09064767796HE HAD THE COURAGE
TO REMARRY.
WILL HE FIND THE COURAGE TO
LOVE AGAIN?Marubuciyar
BAHAAR
And now NIKAAH(Rental Marriage).......Page 2
__bakin k'ofar falon Dada ya toge ,kiran wayar Dada yayi,ta fito kad'ai ya iya furtawa katse kiran yayi Yana mai k'ara tamke fuska.
Kallon ta Dada tayi tareda cewa ki fita yana waje yana jiranki ,Allah ya baku zaman lafiya da zuria ta gari ,kanta a k'asa ta nufi hanyar fita .
Kallo d'aya yayi mata , d'auke kansa yayi tareda yin gaba abun sa, bata cikin hayyacin ta domin duk yau bata samu ta sakawa cikin ta abinci ba shiyasa bata da k'arfin maida magana ko masifa .
Bin bayan sa tayi jiki mace ,uffan baice mata illa inda take tunanin bedroom d'insa ne ya shige abunsa batayi mamakin komoi ba domin tuni tayi tsammanin fuskantar rashin mutunci fiyeda hakan .
Ganin tsayuwa bazata ficce taba yasa ta taka zuwa k'ofar bedroom d'insa.
K'ofar a bud'e take domin tana turawa ta bud'e kwance ta hango shi ya juya ma ganin ta baya sabida haka ita haryanzu baza tace ga kamannin sa, tabbas ta gane gidan da suka zo kawo kuka ne.kwana kin baya , bawai gidan ta gane ba aaa ganin part d'in Dada da haduwa da ita shine dalilin da yasa ta yanke wannan hukuncin .
D'aga kanta keda wuya ,gabanta mugun faduwa yayi ganin yanda bedroom d'insa yake manne da pictures d'insa shida wata kya'kyawar mata ,sunyi kyau sosai ,sai yanzu ta gane inda aka dosa ,sai yanzu ta gane waye aka aura mata .
Tamabayar data zo mata a zuciya itace shin yasan yanda aurensu ya kasance da sanin sa aka bama Baban Jummai ma'kudan kud'i ya siyar musu da ita ,shin wacece wannan matar wacce tazo har gidansu ta kafa mata sharudd'a akan shi,bata da mai bata anso shin tambayoyin ahalin yanzu ,amma tasha alwashin gano duk wasu amsoshin tambayoyin .
K'ara kallon pictures d'insu tayi , kallo d'aya zaka ma pictures d'in kagane tsantsar kauna tsakanin mamallakan hotunan .
Sunyi mata kyau matuk'a murmushi ne ya su'buce mata ,tana mugun son soyayya kawai bata da lokacine sabida yanayin rayuwa, bata tashi cikin sakin jiki da farinci a gidan Mahaifin taba ,tunda ta tashi ita dai a takure suke ita da mahaifiyar ta da sauran 'kannenta .
Ita tunda ta mallaki hankalin kanta nauyi ya hau kanta ,domin a kullun Mama cikin neman na kanta take wato bata zama babu sana'ar hannu wanda aikin Karime ne sayarda koma menene.
Shiyasa tuni jikinta ya saba da aikin wahala .
Ajiyar zuciya tayi tana mai kallon kayan jikin ta atamfar roba ce Mama ta d'inka mata ana gobe bikin ta, d'an satar kallon sa tayi still yana kwance ko motsawa baiyi ba , d'akin tabi da kallo aljannar duniya ta furta cikin ranta komai na d'akin farine da ratsin blue ,tsarin d'akin yayi mata kyau matuk'a , pictures d'insu ta D'an Kara satar kallon cikin ranta take mamakin toh ina matar tasa.
Wane irin dalili garesu da har zasu yi renting aure .
Cikin zuciyar ta take furta Allah shine ya jarabe tada Mahaifi mai mugun san kud'i lokutta da dama haka yake kwace dukkan kud'in da tayi wurin talla .Ganin yanda kayan suka takura mata yasa ta fara baza idanuwa domin gano toilet dan ta d'an watsa ruwa
Wardrobe d'insa ta bud'e abun sai Wanda ya gani, kaya kala kala shishshrye gwanin ban sha'awa.
Ganin babu irin kayan da take nema yasa ta rufe , d'aya bangaren ta bud'e shima haka, bangaren karshe ta duba annan ne taga jerin riguna na maza masu gajeren hannu , murmushi tayi domin abun ya burge ta , wato shi komai nasa a nitse yake kaman wata mace ita kanta bata da lokacin tsayawa ta gyara kayanta haka kusan ma ita ba d'abi'ar ta bace shirya kaya , anyhow take ajiye kayanta wani lokacin haka Mama zata tayi mata fad'a tana mai cewa watarana gidan wani zaki ba kowane namiji bane ke lamuntar mace mai irin wannan dabi'ar ta rashin kimtsa kaya da sakin su ko ina.
YOU ARE READING
NIKAAH ( Marriage For Rent)
RomanceHE HAD THE COURAGE TO REMARRY WILL HE FIND THE COURAGE TO LOVE AGAIN? NIKAAH (Marriage for rent).