*NIKAAH*
*Marriage for Rent* )*By*
*HANAADY*
*Rahama Aminu Bala**WhatsApp*
*09064767796**Follow me on Whatpad*
*Rahama000*
*Instagram*
*balarahamaaminu*HE HAD THE COURAGE
TO REMARRY.
WILL HE FIND THE COURAGE TO
LOVE AGAIN?*Marubuciyar*
*BAHAAR paid book*
*And now* *NIKAAH(Rental Marriage).......*
*Free book**Page 6*
______ya dad'e a cikin toilet d'in dan Karime bata son lokacin da bacci yayi awon gaba da ita ba ,jiki a mace ya fito daga toilet d'in kallo d'aya ya yayi mata,kauda kansa yayi tareda nufar wardrobe, shiryawa yayi zuwa wasu kayan baccin ,cikin mutuwar jiki ya nufi bakin bed d'in , already ta kashe hasken dakin baya iya bacci da haske but baya son takura mata , bedside table ya bud'e tareda d'auko wani photo album .
Wasu zafafan hawaye ne suka sauka saman fuskar sa, I LOVE YOU Sa'ada ya furta tareda rungume photo album d'in, kuka yake shabe shaye sosai yau mutuwar Sa'ada ta dawo masa sabuwa ,he is missing her kaman ba gobe , d'an abunnan daya shiga tsakanin su da Karime ba k'aramin tada masa soyaya da kewar matar sa Sa'ada yayi ba , ya kusa awa d'aya da rabi yana abu d'aya, dafe kansa yayi dake masa mugun ciwo zazzabi ne ya rufe shi cikin lokacin kankane jikinsa ya dau mugun zafi.
A can bangaren Madam Karime kuwa baccin ta take ta sarba abun ka da ba'a saba ba , sanyin AC na ratsa dukkan illahirirn jikinta , cikin baccinta ta fara jiwo nishinsa , saurin durowa tayi daga saman couch direct kansa tayi cikin nuna kulawa ta zauna bakin gadon tareda magana kaman wani saurayin kauye, wanda ke nesa ma zaya iya jiyota ,meke damunka Daddy ??D'ago fuska yayi cikin hali ya kalle ta, kanta babu hula ,gashin kanta mai cika da waya duk ya barbazo janye kallon sa yayi daga kallon ta murya k'asa k'asa yace bana jin dad'i ne, please ki koma kiyi baccin ki .
Kyara zama tayi tareda daura hannun ta saman goshin sa kasancewar kwance yake yana dubar sama, jikinka da zafe sosai ta fad'a tana mai k'ara ta'ba jikin , cikin sauri ta mi'ke tareda nufar toilet , ruwa ta d'ebo cikin wani d'an k'aramin bucket had'i da k'aramin towel ,zama tayi sannan tace wannan zafin na jikinka yayi yawa barina d'an taikama maka da wanan , bai iya bata ansa ba lumshe idanuwan sa yayi kawai yana mai tunanin matarsa Sa'ada.
Nishi yake sama sama,sosai ya bata tausayi domin zafin jikin nasa ya shahara, cikin dauriya ya samu ya tashi zaune bedside table ya nuna mata tareda cewa ta d'auko masa magani, bayan ta d'akko maganin cikin sauri ta fita zuwa kitchen ,ruwan roba ta d'akko , maganin ya jefa baki tareda kora ruwa, Karime baiwar Allah sai sannu take masa .
Zaune take jingine da gado ,Ramadan na gefen ta ,nishi yake sama sama, sannu ta kuma yi masa,bai ansa ba illa k'okarin kwantawa da yake ,ganin zai kwanta ne yasa ta fara k'okarin sauka daga saman gadon,hannun sa ya daura saman jikinta , cikin yanayin ciwo ya kwanta saman cinyar ta, ba ta san ya zata misalta irin halin da take ciki,hannun ta ya kamo tared rungume shi cikin jikinsa, Nishi yake sama sama , ita kanta Karime ji take kaman ba lafiyar ne da ita ba domin yanayin jikin ta ji tayi ya canza mata.
A daskare take kaman kankara har bacci yayi gaba da Ramadan ba tareda sanin taba , bayan kaman awa d'aya Karime tace zan kwanta ?
Shuru taji, k'ara maimaita maganar tayi da zan kwanta shuru taji ,saurin duba shi tayi a tunanin ta ko baya numfashi ne ,ganin baccin sa yake hankali kwance yasa ta saki murmushi, cigaba da gadinsa tayi har bacci yayi awon gaba da ita.
Bud'e idanuwan sa yayi kwance yake comfortably saman cinyar ta , kallon ta yayi bacci take hankali kwance ,gashin kanta a barbaje saman fuskar ta kusan ma duk ya rufe fuskar, kaman wanda zai ta'ba abun tsoro haka ya saka tafin hannun sa ya fara tattara mata gashin, kasancewar Karime akwai gashi kuma gashin tana irin mai yawa ne ga kuma tsawo duk da tsawon sa baikai na matan Novel ba , bud'e idanuwan ta tayi tozali tayi da fuskar sa ,saurin janye hannun sa yayi daga cikin gashin ta tareda saurin tashi zaune ,dafe kansa yayi domin ji yayi still kansa na ciwo , sauka yayi daga saman gadon tared nufar toilet, domin watsa ruwa da kuma alwala kasancewar gari ya danyi haske sun makara sallar asuba.
YOU ARE READING
NIKAAH ( Marriage For Rent)
RomanceHE HAD THE COURAGE TO REMARRY WILL HE FIND THE COURAGE TO LOVE AGAIN? NIKAAH (Marriage for rent).