5 NIKAA(marriage for rent)

12 1 0
                                    

*NIKAAH*
       *Marriage for Rent* )

                     *By*
              *HANAADY*
       *Rahama Aminu Bala

  *WhatsApp*
*09064767796*

*Follow me on Whatpad*
*Rahama000*
*Instagram*
*balarahamaaminu*

HE HAD THE COURAGE
TO REMARRY.
WILL HE FIND THE COURAGE TO
LOVE AGAIN?


Marubuciyar
BAHAAR paid book
And now NIKAAH(Rental Marriage).......
Free book

*Not edited*

*Page 5*

_________Tafiya ya fara cikin takunsa Karime baki ya mutu domin har yanzu  yana ri'ke da hannun ta , bedroom ya shiga kwance suka tarar da Little ba bacci take ba but eyes d'inta a rufe suke , shugowar suce tasa ta bud'e idanuwan ta tana mai murzarsu , Dady bacci nake ji ,sakin hannun Karime yayi tareda matsawa kusada Little zaunawa yayi sannan yace bacci za kiyi ?Da kai ta bashi ansa saman cinyarsa ya d'aura ta sannan yace nayi miki wanka anan zaki kwana koh ??
Cikin yanayin yarinta Little tace aaa Dady bazan kwana anan ba Why ya fad'a k'asa k'asa ,Dada tace yara saba kwana da manya wai , murmushi yayi sannan yace a yaushe ta fad'a miki haka bayan mun saba kwana tare, Dada tace yanzu kai ba gwowro bane kana da mata sabida haka bazan kuma kwana da kai ba zaro idanu waje yayi yana mai saurin kallon Karime ,ita kanta Karime tayi mamakin furucin Little.

Saukowa tayi daga saman jikinsa wurin Karime ta nufa hannun ta ta kama sannan tace Dada tace yanz tareda Momyna zaku rika kwana ,kuma tace zaku samo mana saban baby .
kallon Karime ya kuma , had'a idanuwa sukayi saurin janye nata tayi tana mai ce ma Little haba d'iya ta tare zamu kwana Dada tana miki wasa ne.

Aaa Momy Dada da gaske take tace idan ina kwana tare daku ba zaki kawo mun baby ba ni kuma ina son ki kawo mana baby koh Dady ta idasa maganar da kallon Mahaifin ta ,shidai he is speechless tsohuwar can bata jin magana taya zata rin'ka irin wad'annan maganganun da karamar yarinya.

Cikin jin kunya Karime tace Sa'ada muje na miki wanka ,da kallo ya bisu har suka bacce masa da gani ajiyar zuciya yayi , tareda zama saman couch.

Bayan ta kammala wa Little wanka shirya ta tayi cikin kayan bacci kasancewar akwai kayan ta a dakinsa.

D'aukar Sa'ada yayi saman kafad'ar sa ,baice da Sa'ada komai ba ganin ya fita ,yasa tayi saurin bin bayan ,kallo d'aya ya maita ya mayar da kallonsa kan hanya ,tafiya suke suna fira shi da diyarsa da kallon burgewa take ta kalle su , Allah sarki ta ayyana cikin ranta yanzu da mahaifiyar ta nan da farinciki su tafi haka, Allah sarki Sa'adatu,sosai Karime taji tausayin Ramadan da kuma diyarsa Little,ta fahimci they are not complete, suna buk'atar wani abu a rayuwar su ,suna buk'atar farincikin da yafi haka ajiyar zuciya tayi, tasan yanda aurensu ya kasance ita d'in aronta Mahaifin ta ya bada shin ita wacce zata zo zaya sota kuwa ?? Menene dalilin da yasa Hjy Mariya ke son had'a auren d'iyar ta da Ramadan ?

Why Momy ke goya mata baya a matsayin tana mahaifiyar sa ta yaya zaya amince ayi renting mata wa d'an ta ,??

Bata tunanin farincikin sa .
Dole ta samo ansoshin wad'annan tambayoyin nata.

Wurin wa ta furta a hankali??

Tana can duniyar tunani bata san har sun kusa part d'in Dada, ganin sun d'an yi mata nisa yasa ya d'an jirata ,saurin karasowa tayi ,tare suka shiga,ba kowa falon sabida haka bedroom suka nufa shine a gaba ita kuma tana binsa baya,zaune suka tarar da Dada tana zan carbi zama suka yi tareda gaishe ta cikin sakin fuska ta ansa musu , Sa'ada muka kawo tace ba zata kuma kwana a part nawa ba cewar Ramadan.
Washe baki Dada tayi sannan tace kwarai kuwa yarinya taji magana ta yoo akan me zata ringa kwana da akai tunda yanzu kai d'in ba gwauro bane ,kana da matarka ai  kwana tareda Sa'adatu ya kare ,cikin jin kunya Karime tace Allah Dada data ri'ka kwana acan d'in.
Kallon Karime Dada tayi sannan tace a ina ake haka ai dole ta dawo nan da kwana kada taje ta gano ma kanta abunda yafi k'arfin ta ,saurin sunkuyar da kai Karime tayi shikuwa yasan k'aramin aikin Dada ne ,haka take musu shida Sa'ada bata jin kunyar yanko wata maganar .
Mi'kewa yayi tareda cewa Dada Saida safe ,kallon sa tayi sannan tace tunda anyi aure adai harraka a samo mun wasu jikokin ,jin abunda tace yasa Sa'ada tace eh Dady ina son sister da brother ,bai tsaya basu ansa ba yayi gaba abunsa.
Na dawo kanki Hjy Karime cewar Dada kiyi k'okarin jawo hankalin sa ki samu ki samo mun jika,mijinki dole sai kin had'a da dubarunmu na mata ko kina samun kansa domin kacako tunanin sa da hankalin sa suna kan marigayiyar matarsa wato Sa'adatu, sabida haka dole ki hanzarta,idan kuma kin san kina da matsala toh ki fad'a mun domin na samo miki magani, bayan haka idan baki san yanda ake jan hankalin miji na koya miki.

NIKAAH ( Marriage For Rent)Where stories live. Discover now